





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi -: Lallai wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban kara komai akan hakan ba, zan shiga Aljanna? Ya ce : "Eh", ya ce: Na rantse da Allah ba zan kara komai ba akan hakan ba.
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya sallaci salloli biyar, wadanda suka wajabta bai kara komai akan su ba na nafilifili, kuma ya azimci watan Ramadan bai yi tadawwa’i ba, ya kudirce halatta halal ya kuma aikata shi, ya kudirce haramta haram ya kuma nisanci ta, to shi zai shiga Aljanna.
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Cewa tsarki na zahiri yana kasancewa ne da alwala da wanka, kuma sharadi ne a sallah. Kuma cewa fadin: Alhamdulillah, (wato) "Godiya ta tabbata ga Allah yana cika ma'auni", shi ne godiya gare shi - tsarki ya tabbatar maSa - da kuma siffantaShi da siffofin cika, za'a auna su ranar alkiyama sai su cika ma'aunin ayyuka. Kuma fadin: Subhanallah, "Tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah", Shi ne tsarkake Shi daga kowacce tawaya da kuma siffantaShi da cikakken cika wanda yake dacewa da girmanSa, tare da sonSa da girmamaShi suna cika abinda ke tsakanin sammai da kasa. Kuma: "Sallah haske ce’’ ga bawa a cikin zuciyarsa, da fuskarsa, da cikin kabarinsa, da a tashinsa a taron Alkiyama. Kuma: "Sadaka garkuwace" kuma dalili ce akan gaskiyar imanin mumini, da kuma banbancinsa da munafikin da yake hanuwa daga yin ta (ita sadakar) dan kasancewarsa ba ya yin sadaka a lokacin ta. Kuma: "Hakuri haske ne" - Shi ne tsare rai daga firgici da fushi - wani haskene wanda yake da zafi da kuna, kamar hasken rana; domin shi mai wahalane, kuma yana bukatuwa ga dakewar zuciya da tsareta daga abinda take so; mai shi ba zai gushe ba yana mai haskaka , mai shiriya mai zarcewa akan daidai. Shi ne hakuri akan biyayya ga Allah, da kuma barin sabonSa, da kuma hakuri akan masifu da nau'o'in abubuwan ki a duniya. Kuma: 'Alkur’ani hujjane a gareka" ta hanyar Karanta shi da kuma aiki da shi, ko kuma "Hujjane akanka", ta hanyar barinsa ba tare da wani aiki ba, ko karantawa ba. Sannan - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkanin mutane suna tafiya suna fita suna tashi daga barcinsu suna fita daga gidajensu dan ayyukansu mabanbanta, Daga cikinsu akwai mai tabbata akan biyayya ga Allah, sai ya 'yanto kansa daga wuta, daga cikinsu akwai wanda yake kaucewa daga hakan kuma yake afkawa a cikin sabo sai ya halakar da ita ta hanyar shigarta wuta.
Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair, sai ya ce: "Ya Mu'az, shin kasan hakkin Allah akan bayin Sa, kuma menene hakkin bayi ga Allah?", sai na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba", sai na ce: Ya Manzon Allah shin ba nayiwa mutane albishir da shi ba? Ya ce: "Kada ka yi musu albishir, sai su dogara".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa Shi kadai kada su hada shi da wani abu. Kuma cewa hakkin bayi ga Allah shi ne ba zai azabtar da masu kadaitaShi da bauta ba, wadanda ba sa sanya masa abokin tarayya ba. Sannan cewa Mu'az, ya ce: Ya Manzon Allah, shin baa a yi wa mutane albishir da shi ba dan su yi farinciki, kuma su yi murna da wannan falalar ba ?? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana shi dan tsoron kada su dogara akanta.
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, wadanne abu biyu ne masu wajabtawa? Sai ya ce: "Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta"
Muslim ne ya rawaito shiWani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da dabi'u biyu: Wacce take wajabta shiga Aljanna, da wacce take wajabta shiga wuta? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya amsa masa: Cewa dabi'ar da take wajabta Aljanna ita ce mutum ya mutu alhali yana bautawa Allah Shi kadai ba ya taranya wani abu da shi, Kuma cewa dabi'ar da take wajabta wuta ita ce mutum ya mutu alhali shi yana taranya wani abu da Allah, sai ya sanya kishiya ga Allah da tamka a cikin AllantakarSa ko a kasancewar shi ne Mahalicci ko sunayenSa da siffofinSa.
Daga Sufyan Dan Abdullah AlSakafi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".
Muslim da Ahmad ne suka rawaito shiSahabi Sufayanu dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ya sanar da shi wata magana mai tattaro ma'anonin Musulunci, da zai yi riko da ita, wacce ba zai tambayi waninsa game da ita ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: Na kadaita Allah, kuma na yi imani da cewa Shi ne Ubangijina kuma Allah na, Mahaliccina, Abin bautata na gaskiya ba Shi da abokin tarayya, Sannan ya jawu ga biyayya ga Allah ta hanyar bada farillan Allah, da barin abubuwan da Allah Ya haramta, ya kuma ci gaba akansu.
Daga Abdullahi dan Amr dan Al-Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama, sai Ya bude masa fayil dinsa x asa'in da tara, kowanne fayil tamkar iya ganinka ne, sannan Ya ce: Shin kana musun wani abu daga wannan? Shin marubutaNa masu kiyayewa sun zalinceka ne? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai Ya ce: Shin kana da wani hanzari? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai (Ubangiji) Ya ce: Eh, lallai kanada wani abu kyakkyawa a wurinmu, a yau babu wani zalinci akanka, sai a fitar da wani kati a cikinsa akwai: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, sai ya ce: ka zo wajan ma'aninka, sai ya ce; ya Ubangiji wannan wanne katine tare da wadannan fayilillikan? Sai Ya ce; Lallai cewa kai ba za’a zalinceka ba, sai ya ce: Sai a dora fayilillikan a bangaren ma'auni , katin kuma a daya ma'aunin, sai fayililliakn su yi sauki, kuma katin ya yi nauyi, wani abu ba zai yi nauyi tare da sunan Allah ba".
Tirmizi ne ya Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Zai zabi wani mutum daga al'ummarsa agaban halittu , za'a kira shi dan a yi masa hisabi, sai (Ubangiji) ya bijiro masa da fayilillika casa'in da tara, su ne takardun ayyukansa wadanda ya kasance yana aikatasu a duniya, kuma tsawon kowane fayil tamkar iya ganinnka ne. Sannan Allah - mai girma da daukaka - ya cewa wannan mutumin: Shin kana musun wani abu daga abinda aka rubuta a cikin wadanannan fayilillikan? Shin Mala'ikuna masu kiyayewa masu rubutu sun zalinceka?. Sai mutumin ya ce: A'a ya Ubangiji. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Shin kana da wani hanzari da za'a yi maka uzuri da shi daga abinda ka gabatar na ayyuka a duniya? daga kasancewarsa rafkanuwa ne, ko kuskurene ko jahilcine, Sai mutumin ya ce: A'a ya Ubangiji ba ni da wani hanzari. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Eh, lallai kana da wani kyakkyawan aiki a wurinMu, kuma cewa babu wani zalinci akanka a yau. Ya ce: Sai a fitar da wani kati an rubutawa a ciki: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya cewa wannan mutumin: ka zo wurin ma’aunin ka. Sai mutumin ya ce, yana mai mamaki; Ya Ubangiji! Menene nauyin wannan katin tare da wadannan fayilill din ??. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Wani zalinci ba zai afku akanka ba. Sai ya ce ; sai a dora fayilillikan a ma'aunin, katin ma a daya ma'aunin; sai ma'aunin da fayilillkan suke a ciki su yi sauki, sai ma'aunin da katin yake ciki ya rinjaya, kuma ya yi nauyi, sai Allah Ya gafarta masa.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta . Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa lokacin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, ya cewa (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -: Ka tafi zuwa ga Aljanna ka duba ta, sai ya tafi ya kallace ta sosai sannan ya dawo, Sai (Malaika) Jibril ya ce: Eh, ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa ba wanda zai ji labarin ta da kuma abinda ke cikinta na ni'ima da girmamawa da alkarai sai ya so ya shigeta, kuma ya yi aiki saboda ita. Sannan Allah Ya kewaye Aljanna da abubuwan ki da wahalhalu na aikata umarni da kuma nisantar abubuwan da aka hana; to ya wajaba ga wanda yake son shigarta da ya ketare wadananan abubuwan kin. Sannan Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Ya Jibril! ka tafi ka duba Aljanna, bayan ya kewayeta da abubuwan ki, Sai ya tafi ya dubata, sannan ya zo sai ya ce: Eh, ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa ina jin tsoro da kada wani ya kasa shigarta saboda wahalhalu da tsananin da suke akan hanyarta. Lokacin da Allah Ya halicci wuta, sai ya ce; Ya Jibri! ka tafi ka kallaceta, sai ya tafi ya kallaceta. Sannan ya zo sai (Malaika) Jibril ya ce: Eh ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa babu wani da zai ji labarin azabarta da tashin hankalin cikinta, sai ya ki shigarta ya nisanta daga sabubban shigarta. Sannan Allah - mai girma da daukaka - Ya kewaye wuta, Ya sanya hanya zuwa gareta da sha'awowi da abubuwan jin dadi, sannan Ya ce: Ya Jibril, ka tafi ka yi duba zuwa gareta, Sai (Malaika) Jibril ya tafi sai ya yi duba zuwa gareta, sannan ya dawo sai ya ce: Ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoro na ji tausayin kada wani ya kasa tsira daga gareta; saboda abinda ke gefanta na sha'awowi da abubuwan jin dadi.
Daga Abdullahi dan Amr dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah Ya rubuta abinda ya kaddarawa halittu kafin Ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin, ya ce: Al’ArshinSa yana kan ruwa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa , Allah Ya rubuta abinda zai afku na abinda ya kaddarawa halittu a fayyace, na rayuwa da mutuwa da arziki da makamancin hakan a cikin Lauhul mahfuz , tun kafin ya halicci sammai da kasa da shekara dubu hamsin, abin yana afkuwane daidai da dacewar abinda Allah - mai girma da daukaka - Ya hukunta, Dukkanin wani abu mai kasancewa to da hukuncin Allah ne da ikonSa, Abinda ya samu bawa bai zama zai kuskure shi ba, abinda ya kuskure shi bai zama zai same shi ba.
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a shirka da kafirci (shi ne) barin sallah, sallah ita ce rukuni na biyu daga rukunan musulunci, al'amarinta mai girma ne a musulunci, wanda ya barta yana mai musun wajabcinta, to, ya kafirta da ijima'in musulmai, idan ya barta gabaɗaya don wulaƙantarwa da kasala, to, shi kafiri ne, an cirato ijma'in sahabbai a kan hakan, idan ya kasance yana bari wani lokaci wani lokaci kuma yana yin sallah, to, ya kai kansa ga wannan narkon mai tsanani.