





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh, Sai ya ce: Na so ƙasa da hakan daga gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam: Kada ka ka yi min tarayya da wani abu, sai kaƙi sai dai ka yi shirka daNi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta a zaba bayan shigarta: Da ace duniya da abinda ke cikinta nakane shin zaka fanshi kanka da ita daga wannan azabar? Sai ya ce: Eh, Sai Allah Ya ce: Haƙiƙa Na nema daga gareka kuma Na umarceka da mafi sauƙi daga hakan lokacin da aka karɓi alƙawari gareka alhali kai kana cikin tsatson (annabi) Adam da kada ka yi shirka daNi da wani abu; sai kaƙi lokacin da Na fitar da kai zuwa duniya sai dai shirka.
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Wasu mutane sun tambayi Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da bokaye, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Su ba komai ba ne". Suka ce: Ya Ma’aikin Allah; Wani lokacin suna ba da labari sai kuma abin ya zama gaske. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAn tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da waɗanda suke ba da labarin abin da zai faru nan gaba na gaibu, sai ya ce: Kada ku kula su, kada ku saurari maganarsu, kada ku shiga al’amarinsu. Sai suka ce: Maganarsu tana daidai da abin da ya faru a wani lokaci, kamar a ce su ba da labarin wani abu na gaibu zai faru a wata kaza a rana kaza, sai kuma ya faru kamar yadda suka faɗa. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Aljanu suna sato abin da suke ji ne na labarun sama, sai su sauko da shi zuwa ga abokan hulɗarsu cikin bokaye, sai su ba su labarin abin da suka ji, sannan sai shi bokan ya ƙara ƙarya ɗari a kan wannan labarin da ya ji daga sama.
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Mu’azu yana bayan shi a kan jaki, Ya ce: Ya Mu’azu Ɗan Jabal!!)). Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa, Ya ce; Ya "Mu’azu" Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa sau uku [ya faɗa], ya ce: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne da gaske daga zuciayarsa sai wuta ta haramta a gareshi)). Ya ce: Ya Ma’aikin Allah shin ba na ba mutane labarin nan ba domin su yi murna? Ya ce: Za su saki jiki. Sai Mu’azu ya ba da labarin bayan rasuwar Ma’aikin Allah gudun kada ya ɓoye ilimi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiMu’azu Ɗan Jabal Allah Ya yadda da shi, ya kasance yana bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan abin hawa na dabbarsa, sai ya kira shi Ya Mu’azu, ya maimaita kiran na sa har sau uku, domin ƙarfafawa da Kuma muhimmancin abin zai faɗa masa. A duka kiran Mu’azu Allah Ya yarda da shi yana amsa masa da cewa; Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da da farincin hakan bayan farinciki, Wato na amsa maka Ya Ma’aikin Allah bayan amsawa, kuma na nemi farinciki da wannan amsawa. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba shi bayanin babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Ma’aikin Allah ne da gaske daga zuciyarsa ba ƙarya ba, idan har ya mutu a wannan hali, to, Allah Ya haramta masa wuta. Sai Mu’azu Allah Ya yarda da shi ya tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kan ya baiwa mutane labari domin su yi farin ciki su yi wa juna bushara ta alheri? Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji tsoron kada su saki jiki da hakan, su ƙaranta ayyuka. Mu’azu bai ba da wannan bayanin ba sai dab da rasuwarsa, don tsoron kada ya faɗa cikin masu ɓoye ilimi.
Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ubangijimmu maɗaukaki Yana sauka a kowanne dare, zuwa sama makusanciya, lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura yana cewa: Wa zai roƙeni in amsa masa,?? wa zai tambaye ni in ba shi, ?? wa zai nemi gafarata in gafarta masa ??
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin Allah maɗaukaki Yana sakkowa a kowanne dare zuwa sama makusanciya lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura, yana kwaɗaitar da bayinSa a kan su roƙe shi, shi kuma zai amsawa wanda ya roƙe Shi, yana zaburar da su a kan su tambaye Shi abin da suke so, Shi kuma zai ba wanda ya tambaye Shi, yana kiransu da su roƙi gafararSa daga zunubansu Shi kuma yana gafartawa bayinSa muminai.
Daga Abu Marsad Alghanawi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu.
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana zama a kan kaburbura. Kamar yadda ya hana yin Sallah ana kallon kaburbura, ta yadda kabari zai kasance ta inda alƙiblar mai Sallah take, domin hakan hanya ce ta shirka.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiUwar muminai Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - ta fadawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta kasance a kasar Habasha ta ga wata coci - ana ce mata Mariya - a cikinta akwai hotuna da kawace- kawace da zane-zane; dan mamaki daga hakan! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana dalilan sanya wadannan hotunan; Sai ya ce: Wadannan wadanda kike fada sun kasance idan mutum nagari ya mutu a cikinsu, sai su gina masallaci akan kabarinsa suna sallah a cikinsa, su kuma zazzana wadancan hotunan, ya bayyana cewa mai aikata wancan shi ne mafi sharrin halitta a wurin Allah - Madaukakin sarki -; domin aikata shi yana kaiwa zuwa shirka da Allah - Madaukakin sarki -.
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar dabi'un musulunci kamar cika ginin ne, Farkon wadanan rukunan: Shaidawa biyu; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (shaidawa) Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, su rukuni daya ne; dayansu ba ya rabuwa da dayan, bawa zai furtasu yana mai tabbatar da kadaituwar Allah da kuma cancantarSa ga bauta Shi kadai banda waninSa, kuma yana mai aiki da abinda suka hukunta, kuma yana mai imani da Manzancin Annabi Mukammadu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai binsa. Rukuni na biyu: Tsaida sallah, su ne sallolin farillai biyar a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da magariba, da Lisha, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu. Rukuni na uku: Fitar da zakkar farilla, ita ibada ce ta dukiya wajiba a kowacce dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga wadanda suka cancanceta. Rukuni na hudu: Hajji, shi ne nufin Makka dan tsaida ibadu, dan yin bauta ga Allah - Mai girma da daukaka -. Rukuni na biyar: Azumin Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga masu bata azimi da niyyar bauta ga Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana.
Daga Abu Sa'id Al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin umarni da canza abin ki - wanda shi ne dukkanin abinda Allah da ManzonSa suka hana - gwargwadon iko, Idan ya ga wani abin ki to yana wajaba akansa ya canja shi da hannu idan yana da iko, Idan ya gajiya akan hakan, to ya canja shi da harshensa, ta hanyar hana mai aikatawar, kuma ya bayyana masa cutar hakan, ya kuma shiryar da shi zuwa alheri maimakon wannan sharrin, Idan ya gajiya daga wannan matakin, to ya canja shi da zuciyarsa shi ne ya ki wannan mummunan aikin, kuma ya yi niyyar cewa shi da yana da iko akan canja shi to da ya aikata, canzawa da zuciya shi ne mafi raunin matakan imani a canja abin ki.
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin za'a kamamu da abinda muka aikata a lokacin Jahiliyya? ya ce: "Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar shiga Musulunci. Kuma cewa wanda ya musulunta kuma ya kyautata Musuluncinsa ya zama mai tsarkakewa mai gaskiya, to ba za’a yi masa hisabi da abinda ya aikata na sabo ba a lokacin Jahiliyya, Wanda ya munana a cikin Musulunci, da ya zama munafiki ko ya yi ridda ga Addininsa, za'a yi masa hisabi da abinda ya aikata a cikin kafirci, da kuma abinda ya aikata a cikin Musulunci.