Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Aliyu Bn Abi Xalib ya kasance yana fama da Ciwo a Idanuwansa, saboda toka da ta shigar masa a yaqin Khaibar, sai Manzon Allah SAW sai ya shafi fuskarsa kuma yayi tofi a cikin Idanunsa sai ya warke da yardar Allah sannan ya bashi tuta, kuma Allah ya bashi Nasarar buxe ganuwar Khaibar, kuma Ali -Allah ya yarda da shi- cewa shi Ban tava yin ciwon kai ba ko ciwon Ido tunda Manzon Allah SAW ya shafi fuskata, kuma yayi mun tofi a idona a ranar Khaibar lokacin da ya bani Tuta
Abul Ala ya Kasance Umair Bn Milhan -Allah ya yarda dashi- lokacin da Mutuwa ta zo masa, sai wani Mutum ya wuce a qarshen gida, ya ce sai naganshi a fuskar Qatada, ya ce: Kuma na kasance idan naganshi kai ka ce a fuskarsa Mai ne saboda fes xinsa da walqiyarsa da kuma haskensa kuma wancan saboda Manzon Allah SAW yashafi fuskar Qatada ne, tun daga wannan lokacin yake da wannan sheqin da walqiyar saboda Al-barkar shafawar Manzon Allah SAW da yayiwa Fuskarsa.
Yayin da ya Wanke Manzon Allah SAW ya tafi yana neman abunda ake samu ga Mamaci, na bunda yake futa daga jikinsa na futsari ko bayan gida ko mai kama da shi, bai samu komai ba, saboda ana iya samun wani abu saboda sakin da gavvai suka yi, sai Ali ya ce: Fansarka da Mahaifina ya Manzon Allah , Kana tsaftace a halin kana da Rai, haka ma bayan ka Mutu
Nana Aisha tana bada labarin cewa ita Ban taba yin kishi da wata Mata daga cikin Matan Annabi SAW sai akan Khadija, kuma ni ban risketa ba, ta ce: Kuma Manzon Allah ya Kasance idan ya yanka Akuya, sai ya ce: ku aika da ita zuwa kawayen Khadija" sai ta ce sai na bashi haushi wata rana sai na ce: Khadija, sai Manzon Allah SAW ya ce: "lallai ni Allah ya Azurtani da sonta"
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantar su, suna jiɓintar al'amuransu kamar yadda sarakuna da shugabanni suke aikatawa da talakawansu, a duk lokacin da ɓarna ta bayyana a cikinsu sai Allah Ya aiko musu da wani Annabin da zai daidaita al'amarinsu kuma ya gusar da abinda suka canja na hukunce-hukunce. Lallai cewa babu wani Annabi a bayana (ballantana) ya aikata abinda waɗancan suke aikatawa, za'a samu halifofi a bayana zasu yawaita kuma jayayya da saɓani zasu faru a tsakaninsu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Da me zaka umarce mu? Sai ya ce: Idan Aka yi wa halifa caffa bayan wani halifan; to caffar na farko ce ingantacciya wajibine a cikata, caffar na biyun kuma ɓatacciya ce kuma nemanta yana haramta, kuma ku basu haƙƙinsu, ku bisu ku yi mu'amala da su da ji da bi inba a saɓon ba ne, domin cewa Allah Zai tambayesu kuma Zai yi musu hisabi a kan abinda suke aikata shi gareku.
Wasu mutane cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun zo ɗakunan matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suna tambaya game da ibadarsa a ɓoye a cikin gidansa, lokacin da aka ba su labari kamar cewa su sunga ƙanƙantarta, sai suka ce: Wane mu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ? haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa da abinda ya jinkirta, saɓanin wanda bai san faruwar gafara gare shi ba to yana buƙatuwa zuwa kai matuƙa a cikin ibada wataƙila ya sameta. Sannan sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan yi bacci a kan shinfiɗa ba. Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi fushi, ya yi wa mutane huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi ya ce: Menene sha'anin wasu mutane ne sun ce kaza da kaza?! Na rantse da Allah lallai cewa nine mafi tsoronku ga Allah kuma mafi taƙawarku gare shi, sai dai cewa ni ina bacci dan in samu ƙarfi akan tsayuwar (dare), kuma ina buɗe baki dan in samu ƙarfin azimi, kuma ina auren mata, wanda ya bijire daga hanyata kuma ya ga cika a waninta, ya riƙi hanyar wanina to ba ya tare da ni.
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da wasu daga ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, daga abinda ta ambata: Cewa shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba'a taɓa ba shi zaɓi ba tsakanin al'amura biyu sai ya ɗauki mafi sauƙinsu muddin dai mafi sauƙin ba mai kaiwa zuwa zunubi ba ne, to cewa shi zai kasance mafi nisantar mutane ga wannan zunubin kuma zai zaɓi mafi tsanani a lokacin. Kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi bai taɓa ramuwa ba ga kansa a keɓance ba, kai ya kasance yana kau da kai kuma yana afuwa daga haƙƙinsa sai dai idan keta alfarmomin Allah aka yi sai ya zama ya yi hukunci saboda Allah, kuma ya kasance mafi tsananin mutane a fushi saboda Allah.