





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- tace "Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi bai Aure kan Khadija ba har saida ta Mutu"
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi bai Auri wata Mata ba, ya hada ta da Nana Khadija Bnt Khuwailid- Allah ya yarda da ita- har ta Mutu, kuma wannan yana nuna Matsayin Nana Khadija a Wajen Annabi SAW kuma ita ce Matarsa ta farko
An karvo -Allah ya yarda da ita- ta ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Ni nasan in kina farin ciki dani, kuma haka idan kina fushi da ni" sai ta ce: sai na ce: ta yaya kake gane hakan ? sai ya ce: "Idan kina farin ciki sai kice a'a na rantse da Muhammad kuma idan kina fushi da ni sai ki ce na Rantse da ubangijin Ibrahim" sai ta ce: na ce: Ey wallahi haka ne ya Manzon Allah, bana qauracewa sai sunanka
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiNana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: Manzon Allah SAW ya ce da ni: "Lallai ni ne mafi sanin lokacon da bakya fushi da ni, da kuma lokacin da kike fushin da ni, sai ta ce da shi: ta yaya ka sani hakan? sa i Manzon Allah SAW ya ce: "idan kina fushi da ni awani kina cewa: Na rantse da Ubangijin Muhammadu, sai ki kirawo sunana a cikin rantsuwarki, kuma idan kina fushi da ni akan wani abu na duniya da yake da alakar zamantakewar Aure, sai ki ce a cikin rantsuwarki: na rantse da Ubangijin Ibrahim, sai ki kaucewa faxar suna na zuwa sunan Ibrahim sai ta ce: E haka ne Wallahi ya Manzon Allah, ba zan bari ba sai faxar sunanka akan Harshena tsawon fushi na, sai dai Soyayyarka tana nan daram cikin Zuciyata
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rubuta (wasiku) zuwa ga Kisra, da Ƙaisara, da Najjashi, kai da dukkan mai tsaurin kai, yana kiransu zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, amma ba Najjashin da Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sallah ba.
Muslim ne ya rawaito shiAnas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin rasuwarsa ya yi rubutu zuwa ga waɗanda ke kewaye da shi daga sarakunan al'ummu, yana kiransu zuwa ga Musulunci; sai ya rubuta zuwa ga Kisra, shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Farisawa, haka zuwa ga Ƙaisara shi kuma laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Rum, haka zuwa ga Najjashi shi laƙabi ne na dukkanin wanda yake sarki ne na Habasha. Kuma ya rubuta zuwa ga kowane sarki mai tsaurin kai wanda ya yi wa mutane tumbe, ya rinjaye su, kuma Anas - Allah Ya yarda da shi - ya bayyana cewa Najjashin da aka rubuta masa ba Najjashin da ya musulunta ba ne kuma ya rasu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa sallah.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ya Allah ! Kaɗai ni mutum ne, duk mutum daga cikin musulmai da na zage shi ko na tsine masa ko na dake shi to Ka sanya hakan ya zama tsarki da rahama gare shi».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya yi addu'a sai ya ce: Ya Allah ? Kaɗai ni mutum ne, ina yin fushi kamar yadda ɗan Adam yake yin fushi, duk muminin da na cutar da shi ko na zage shi na aibanta shi, ko na tsine masa na yi masa mummunar addu'a da korewa daga rahamarKa, ko na dake shi da bulala, to ka sanya hakan ya zama tsarkaka da kusanci da tsarkakewa da kaffara da kuma rahamar da zaka yi masa rahama da ita.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce: Ya Manzon Allah ka yi wa mushrikai mummunar addu'a ya ce: "Lallai ni ba'a aikoni mai yawan tsinuwa ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama rahama".
Muslim ne ya rawaito shiAn nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa mushrikai mummunar addu'a, sai ya ce: Lallai cewa ni ba'a aikoni daga Allah in zama mai yawan tsinuwa ba ina yi wa mutane mummunar addu'a da nisantarwa da kuma korewa daga rahamar Allah sai in yanke su daga alheri, lallai ni ba'a aikoni dan haka ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama sababin alheri da kuma rahama ga mutane baki ɗaya, da kuma muminai a keɓance.
Daga Nana Aisha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ce: Farkon abinda aka fara wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na wahayi shi ne kyakkyawan mafarki a cikin barci, ya kasance ba ya ganin mafarki sai ya zo masa kwatankwacin hasken Asuba, sannan aka sa masa son kaɗaici, ya kasance yana kaɗaita a kogon Hira, sai ya yi ibada a cikinsa - shi ne ibada - a wasu ƙididdigaggun darare kafin ya koma gurin iyalansa, kuma yana yin guziri saboda hakan, sannan ya koma ga Nana Khadija, sai ya yi guzuri na kwatankwacinsu (kwanukan), har sai da gaskiya ta zo masa alhali shi yana cikin kogon Hira, sai Mala'ika ya zo masa sai ya ce: Ka yi karatu, ya ce: «Ni ba mai karatu ba ne» ya ce: «Sai ya kamani sai ya rufeni har sai da ya kai ƙololuwar wahala gareni sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, sai na ce: Ni ba mai karatu ba ne, sai ya kamani sai ya rufeni karo na biyu har sai da ya kai ƙololuwar wahala gareni sannan ya sakeni, sai ya ce: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta Ya halicci mutum daga gudan jini ka yi karatu alhali Ubangijinka shi ne mafi girma}», [al-Alaƙ: 1-3]. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawo da su (ayoyin) zuciyarsa tana karkarwa, sai ya shiga wurin Nana Khadija 'yar Kuwailid - Allah Ya yarda da ita -, sai ya ce: «Ki lulluɓeni, ki lulluɓeni» sai suka lulluɓe shi, har sai da razani ya tafi daga gare shi, sai ya faɗawa Nana Khadija kuma ya bata labari: «Haƙiƙa na ji tsoron kaina» sai Nana Khadija ta ce: A'a wallahi, Allah ba zai kunyataka ba har abada, lallai kai kana sadar da zumunci, kana ɗaukar ɗawainiya kana bawa wanda ba shi da komai, kana tarbar baƙo, kuma kana taimako akan masifu na gaskiya, sai Nana Kahadija ta tafi da shi har ta zo da shi wurin Waraƙah ɗan Naufal ɗan Asad ɗan Abdul'uzza, ɗan kawun Nana Khadija. Ya kasance wani mutum ne da ya zama kirista a zamanin jahiliyya, kuma ya kasance yana rubuta harshen Ibraniyanci, yana rubuta Linjila da harshen Ibraniyanci abinda Allah Ya so ya rubuta, kuma ya kasance dattijo ne makaho, sai Nana Khadija ta ce da shi: Ya kai ɗan kawuna na ! Ka ji magana daga ɗan ɗan'uwanka, sai Waraƙah ya ce masa: Yakai ɗan ɗan'uwana me ka gani? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya labarta masa labarin da ya gani, sai Waraƙah ya ce masa: Wannan Namus ne (Mala'ika) wanda Allah Ya saukarwa (Annabi) Musa shi, kaicona inama dai a ce ni matashi ne a cikin kwanukan da za'a aikoka, inama dai a ce ina raye lokacin da mutanenka zasu koreka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Shin yanzu su zasu koreni?», ya ce: Eh, babu wani mutumin da zai zo da irin abinda ka zo da shi sai an cutar da shi, idan lokacinka ya riskeni zan taimakeka taimako mai ƙarfi. Sannan Waraƙah kuma bai jima zuwa wani lokaci ba ya rasu, kuma wahayi ya yanke.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiUwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa farkon abinda aka farawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na wahayi shi ne mafarki na gaskiya a cikin bacci, ya kasance ba ya ganin mafarki sai ya hakan ya zo a bayyane mai kama da hasken Asuba, sannan aka sa masa son kaɗaitaka, ya kasance yana kaɗaitaka a kogon Hira sai ya yi bauta a cikin wasu 'yan darare ƙididdigaggu kafin ya koma ga iyalinsa, kuma ya tafi da guzuri saboda hakan, sannan ya dawo gurin Uwar muminai Nana Khadija - Allah Ya yarda da ita - sai ya yi guziri ga kwatankwacin adadin dararen, har sai da umarni na gaskiya ya zo masa alhali shi yana kogon Hira. Sai Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya zo masa sai ya ce masa: Ka yi karatu, sai (Manzo) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ban iya karatu ba, ya ce: Sai ya kamani ya damƙeni ya matseni har sai da yakaini ƙololuwa a wahala sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, nace: Ban iya karatu ba, sai ya kamani ya damƙeni karo na biyu har sai da yakai ƙololuwa a wahalar da ni sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, sai na ce: Ban iya karatu ba, sai ya kamani a karo na uku sai ya damƙeni karo na uku sannan ya sakeni, sai ya ce: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta. Ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu alhali Ubangijinka Shi ne Mafi gima}. [al-Alaƙ: 1-3]. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya dawo da ayoyin zuciyarsa tana karkarwa dan jin tsoron mutuwa, sai ya shiga wurin matarsa Uwar muminai Nana Khadija 'yar Khuwailid - Allah ya yarda da ita -, sai ya ce: ki lulluɓeni da tufafi, sai suka lulluɓe shi da tufafi har sai da tsoron ya tafi daga gare shi, sai ya faɗawa Nana Khadija kuma ya bata labari, kuma ya ce: Haƙiƙa na ji wa kaina tsoron mutuwa, sai Nana Khadija ta ce: A'a, wallahi har abada Allah ba zai kunyataka ba, lallai kai kana sadar da zumunci, kana ɗaukar nauyin mai rauni wanda ba zai iya tsayuwa da kansa ba, kana bawa talaka wanda ba shi da komai; inda kake baiwa mutane abinda ba za su same shi ba a wurin waninka ba, kuma kana tarbar baƙi, kuma kana taimako akan masifu na gaskiya. Sai Nana Khadija ta tafi da shi har kai shi wurin Waraƙah ɗan Naufal ɗan Asad ɗan Abdul'uzza, shi ɗan kawunta ne, kuma ya kasance mutum ne da ya bar jahiliyya ya kasance kirista, ya kasance yana rubuta abinda Allah Ya so ya rubuta na Injila da harshen Ibraniyanci, kuma ya kasance dattijo ne mai yawan shekaru, ba ya gani, sai Nana Khadija ta ce da shi: Ya kai ɗan kawu, ka ji daga ɗan ɗan'uwanka, sai Waraƙah ya ce masa: Yakai ɗan ɗan'uwana, me kake gani? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi labarin abinda ya gani, sai Waraƙah ya ce masa: Wannan Jibril ne wanda Allah Ya saukar da shi ga AnnabinSa Musa - aminci ya tabbata agare shi -, kaicona a ce ni matashi ne ƙaƙƙarfa a cikinsu (kwanukan da za'a aikoka), inama dai a ce zan zama ina raye lokacin da mutanenka zasu koreka, sai (Manzo) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin su zasu koreni?! Ya ce: Eh, babu wani mutum da ya zo da abinda ka zo da shi ba sai an cutar da shi, idan lokacinka ya riskeni zan taimakeka taimako mai ƙarfi. Sannan Waraƙah bai rayu tsawon lokaci ba sai ya rasu, kuma wahayi ya yi jinkiri tsawon lokaci.
Daga Abu Salama Ibnu Abdurrahman cewa Jabir Ibnu Abdullahi al-Ansari - Allah Ya yarda da su - ya ce: Alhali shi yana bada labari game da lokacin wahayi, a cikin zancensa sai ya ce: "Wata rana ina tafiya sai na ji wata ƙara daga sama, sai na ɗaga ido na, sai ga mala'ikan da ya zo mini a (kogon) Hira a zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, ai na ji tsoronsa, sai na dawo sai na ce: Ki lulluɓeni, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da {Ya kai mai lulluɓa1 Ka tashi ka yi gargaɗi}[alMuddasir: 2] zuwa faɗinSa: {Ka ƙauracewa gumaka} [al-Muddassir: 5]. Sai wahayi ya tsananta kuma ya bibiyi juna.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari alhali shi yana bada labari game da tsayawar wahayi da kuma dakatar da saukarsa a farkon manzancinsa: Wata rana ina tafiya a lungun Makka sai na ji wata ƙara daga sama sai na ɗaga idona, sai ga mala'ikan da ya zo mini a kogon Hira yana zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, sai na tsorata na razana daga gare shi, sai na dawowa iyalina sai na ce: Ku lulluɓeni da tufafi. Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da: {Ya kai mai lulluɓa} mai lulluɓa da tufansa, {Ka ta shi} da kira {Ka yi gargaɗi} ka gargaɗar da wanda bai yi imani da saƙonka ba. {Ubangijinka} Ubangijinka abin bauta {Ka girmama} ka gode maSa ka girmamaShi. {Tufafinka} tufafinka {Ka tsarkake} ka tsamosu daga najasa, {Gumaka} da bautar gumaka da mutun mutumi {To ka ƙaurace} ka bari, sai wahayi ya yi ƙarfi bayan haka ya yi yawa.
Daga Adullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- ya ce: "Manzon SAW ya aika Rundunar Yaqi zuwa Najd sai na futo a cikinta, sai muka samo Raquma da da Dabbobi, sai rabon mu ya zamanto Rakuma goma sha biyu, sai Manzon Allah SAW ya qara mana Raqumi xaixai"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAbdullaho Bn Umar- Allah ya yarda da su- yana bada labarin cewa Manzon SAW ya aika Rundunar Yaqi zuwa Najd sai na futo a cikinta, sai muka samo Raquma da da Dabbobi, sai rabon mu ya zamanto Rakuma goma sha biyu, sai Manzon Allah SAW ya qara mana Raqumi xaixa