





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Abdullahi Jabir ibnu Abdullahi al-Ansari - Allah Ya yarda da su -: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli waɗanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban ƙara komai akan hakan ba, zan shiga Aljanna? Ya ce : «Eh».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya sallaci salloli biyar, wadanda suka wajabta bai kara komai akan su ba na nafilifili, kuma ya azimci watan Ramadan bai yi tadawwa’i ba, ya kudirce halatta halal ya kuma aikata shi, ya kudirce haramta haram ya kuma nisanci ta, to shi zai shiga Aljanna.
Daga Mu'az ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah! Bani labarin aikin da zai shigar da ni aljanna kuma ya nisantar da ni daga wuta, ya ce: «Haƙiƙa ka yi tambaya game da wani abu mai girma, kuma cewa shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa ka bautawa Allah kada ka hada shi da kowa, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azumci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin (Allah). Sannan ya ce: Shin ba zan shiryar da kai zuwa ga ƙofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaka tana shafe zunubi kamar yadda ruwa yake kashe wuta, da kuma sallar mutum a tsakiyar dare, sannan ya karanta: {Sasanninsu suna nisantar makwanci} har ya kai (suna aikatawa). sannan ya ce: Shin bana baka labari da asalin al'amari ba da ginshiƙinsa da kuma ƙololuwar tozansa, sai na ce: Na'am ya Manzon Allah, ya ce: Asalin al'amari shi ne Musulunci, ginshiƙinsa ita ce sallah, kuma ƙololuwar tozansa shi ne jihadi. Sannan ya ce: Shin bana baka labari ba da abinda zai haɗa haka gaba ɗaya ba? na ce: Na'am ya Manzon Allah! Sai ya riƙe harshensa kuma ya ce: Ka riƙe wannan, na ce: Ya Annabin Allah! Muma za’a kama mu da abin da muke magana da shi? sai ya ce: Babarka ta yi wabinka ! ai ba wani abu ne yake afkar da mutane ta fuskokinsu ko ta hancinsu ba sai abin da harsunansu suke girba».
Tirmizi ne ya ruwaito shiMu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna kan tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar da ni aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, Ya ce: Haƙiƙa ka tambayeni daga wani aiki mai girman aikatawa ga rayuka, kuma mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa; ka yi farillan Musulunci: Na farko: Ka bauta wa Allah Shi kaɗai kada ka taranya wani abu da Shi. Na biyu: Ka tsaida salloli biyar na farilla a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da Magariba, da Isshai, da sharuɗɗansu da rukunansu da wajibansu. Na uku: Ka fitar da zakkar farilla, ita ce ibada ta dukiya wajiba a kowace dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga waɗanda suka cancanceta. Na huɗu: Ka azimci Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga abubuwan da suke karya azimi da niyyar bauta, daga ɓollowar alfijir zuwa faɗuwar rana. Na biyar: Ka ziyarci Ɗakin Allah, da nufin Makka dan yin ibadun aikin Hajji, dan bauta ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin ba na sanar da kai hanya mai kaiwa ga ƙofofn alheri ba? hakan da bin waɗancan farillan da nafilfilin: Na farko: Azimin nafila, shi mai hanawa ne daga afkawa cikin saɓo, hakan da karya sha'awa, da kuma rage ƙarfi. Na biyu: Sadakar nafila tana kashe laifuka bayan an aikata su kuma tana tafiyar da su tana kuma shafe su. Na uku: Sallar dare a kashi ɗaya bisa uku na ƙarshen dare, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Sasanninsu suna nisanta} wato: Suna nisanta {Daga makwantansu} wato: Wuraren kwana { Suna kiran Ubangijinsu} da yin sallah da zikiri da karatu da addu'a, {Dan tsoro da kwaɗayi kuma suna ciyarwa daga abinda muka azirta su, wata rai bata sanin abinda aka ɓoye musu na abinda ido yake farin ciki da shi} wato abinda idanunsu zasu yi farin ciki da shi a ranar Alƙiyama da kuma aljanna ta ni'ima, {Dan sakamako da abinda suka kasance suna aikatawa}. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin bana baka labari da asalin Addini ba? da ginshiƙinsa wanda yake dogaro akansa? da ƙololuwar tozansa? Mu'az - Allah Ya yarda ad shi - ya ce: Eh, ya Manzon Allah. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Asalin al'amari: Musulunci shi ne shaidawa biyu, kuma dasu ne tushen Addini zai wayi gari tare da mutum. Ginshiƙinsa: Sallah, babu Musulunci ba tare da sallah ba, kamar yadda babu gida ba tare da ginshiƙi ba, wanda ya yi sallah Addininsa zai ƙarfafa zai ɗaga; kuma ƙololuwar tozansa da ɗaukakarsa yana kasancewa ne da yin yaƙi da yin ƙoƙari a yaƙar maƙiya Addini dan ɗaukaka kalmar Allah. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin ba na baka labari da kyautata abinda ya gabata ba? sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe harshensa, ya ce: Ka hana wannan kada ka yi magana da abinda bai shafeka ba. Mu'az ya ce: Shin Ubangijinmu zai kamamu Ya yi mana hisabi da dukkan abinda muke magana da shi?! Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Mahaifiyarka ta yi wabinka! ba ana nufin mummunar addu'a akansa ba, sai dai yana daga zancen larabawa dan faɗakar da shi zuwa wani al'amarin da ya kasance yana kamata ya farka da shi ya kuma san shi, sannan ya ce: Ai babu abinda yake afka mutane ya jefasu cikin wuta ta fuskokinsu sai abinda harasansu suke girba na kafirci da ƙazafi da zagi da yi da mutum da annamimanci da ƙagen ƙarya da makamancinsu.
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga wurin Ubangijinsa - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, Ya ce: «Lallai Allah Ya rubuta kyakkyawa da mummuna, sannan ya bayyana haka, wanda ya yi niyyar (aikata) kyakkyawa bai aikatata ba; Allah zai rubuta masa kyakkyawa cikakkiya a wurinSa, idan ya yi niyyar yinta sai ya aikatata; Allah zai rubutata a wurinSa kyakkyawa goma har zuwa ninki ɗari bakwai har zuwa ninkin ba ninkin. Idan kuma ya yi niyyar mummuna bai aikatata ba; Allah zai rubuta ta kyakkyawa cikakkiya a wurinSa, idan kuma ya yi niyyarta sai ya aikatata; Allah zai rubutata mummuna ɗaya».
Bukhari da Muslim Suka ruwaito shi a cikin litattafansu da wannan lafazinManzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah Ya ƙaddara kyawawa da munana, sannan Ya bayyanawa Mala'iku biyu yaya zasu rubuta su: Wanda ya yi nufin ya aikata kykkyawa za'a rubuta masa kyakkyawa ɗaya ko da bai aikatashi ba, idan ya aikatashi, to, za a ninkashi da tamkarsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, ƙarin yana kasancewa ne da gwargwadan abin da ke cikin zuciya na ikhlasi da ƙetarewar amfani da makamancin hakan. Wanda ya yi nufin aikata mummuna sannan ya barshi saboda Allah, za a rubuta masa kykkyawa, idan ya barshi don shagaltuwa da barinsa, tare da rashin aikata sabubbanta ba za a rubuta masa komai ba, idan ya barshi don gajiyawa daga gareshi za a rubuta masa niyyarsa, idan ya aikatata za a rubuta masa mummuna ɗaya.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da masoyiNa to haƙiƙa na sanar da shi yaƙi, kuma bawa Na bai nemi kusanci gareni da wani abu mafi soyuwa gareNi ba daga abin da na wajabata masa, kuma bawaNa ba zai gushe ba yana neman kusanci daNi ba har sai na so shi, idan Na so shi sai in zama jinsa wanda yake ji da shi, da ganinsa wanda yake gani da shi, da hannunsa wanda yake damƙa da shi, da ƙafarsa wacce yake tafiya da ita, idan ya rokeNi lallai zan ba shi, idan ya nemi tsariNa lallai zan tsare shi ».
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari a cikin hadisi Ƙudusi cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Duk wanda ya cutar da wani waliyyi daga cikin waliyyaiNa ya fusatar da shi ya ƙishi to haƙiƙa na sanar da shi kuma na bayyanar da adawata gare shi. Waliyyi shi ne; Mumini mai tsoron Allah, kuma gwargwadan abin dake ga bawa na imani da taƙawa rabonsa na soyayyar Allah take kasancewa gare shi, kuma musulmi bai nemi kusanci ga Ubangijinsa ba da wani abu mafi soyuwa gare shi daga abin da ya wajabta masa na aikata ayyukan ɗa'a da barin abubuwan da aka haramta, kuma musulmi ba zai gushe ba yana neman kusanci ga Ubangijinsa da nafilfili tare da farillai ba; har sai ya samu soyayyar Allah, idan Allah Ya so shi sai Allah Ya zama mai daidaita masa waɗannan gaɓɓan guda huɗu. Zai daidaita shi a cikin jinsa, ba zai ji komai ba sai abinda zai yardar da Allah. Kuma Zai daidaita shi a ganinsa, ba zai kalli komai ba sai abinda Allah Yake son kallo zuwa gare shi kuma Ya yarda da shi. Kuma Zai daidaita shi a hannunsa, ba zai aikata komai da hannunsa ba sai abinda zai yardar da Allah. Kuma Zai daidaita shi a ƙafarsa, ba zai yi tafiya ba sai inda zai yardar da Allah, kuma ba zai yi wani ƙoƙari ba sai abin da a cikinsa akwai alheri. A tare da hakan idan ya roƙi Allah wani abu to lallai Allah zai ba shi abinda ya roƙa, sai ya zama wanda ake amsawa addu'a, idan ya nemi tsarin Allah ya fake gareShi dan neman tsari, to Allah Zai tsare shi Zai kare shi daga abinda yake jin tsoro.
Daga Abdullahi ibnu Amr ibnul Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Imanin ɗayanku ba zai cika ba har sai son zuciyarsa ya kasance mai bi ga abin da na zo da shi».
Mun rawaito shi a cikin littafin Al-Hujjah da isnadi ingantacceAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mutum ba ya zama mumini mai cikakken imani na wajibi har sai soyayyarsa ta zama mai bi ga abin da Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo da shi na umarni da hani da wasunsu, sai ya so abin da ya yi umarni da shi, ya kuma ƙi abin da ya yi hani daga gare shi .
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Abubuwa huɗu wanda ya kasance a cikinsu to ya kasance munafiki, idan akwai wata ɗabi'a daga cikinsu a tare da shi to ya kasance yana da ɗabi'ar munafunci har sai ya barta: Wanda idan zai yi zance sai ya yi ƙarya, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan aka yi rigima da shi sai ya yi fajirci, idan aka yi yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara».
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga ɗabi'u huɗu idan sun taru a tare da musulmi to ya zama mai tsananin kama da munafukai saboda waɗannan ɗabi'un, wannan ga wanda galibi suka zama a tare da shi akwai waɗannan ɗabi'un, amma wanda suka zama kaɗan to bai shiga cikin su ba, sune: Na farko: Idan zai yi zance sai ya yi gangancin ƙarya da rashin gaskiya a cikin zancensa. Na biyu: Idan aka yi yarjejeniya da shi ba zai cika ba, kuma ya yaudari abokinsa. Na uku: Idan ya yi alƙawari ba zai cika shi ba kuma sai ya saɓa shi. Na huɗu: Idan aka yi faɗa da shi kuma ya yi rigima tare da wani sai husumarsa ta zama mai tsanani, kuma ya bauɗe daga gaskiya, ya yi dabarar a kin karbar gaskiya da ɓata ta, kuma ya faɗi ɓata da ƙarya. Domin munafunci shi ne bayyanar da sabanin abinda aka ɓoye, wannan ma'anar samammiya ce a tare da mai waɗannan ɗabi'un, kuma munafuncinsa ya zama a cikin haƙƙin wanda ya zantar da shi, kuma ya yi masa alƙawari, ya amince masa, ya yi husuma da shi, ya yi yarjejeniya da shi cikin mutane, ba wai cewa shi munafuki ne a cikin musulunci ba sai ya bayyanar da shi alhali shi yana ɓoye kafirci, wanda ya kasance a cikinsa akwai wata ɗabi'a daga waɗannan ɗabi'un; to a cikinsa akwai siffa ta munafunci har sai ya barta.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa da Allah cewa wani daya daga wannan al'ummar ba zai ji shi ba, Bayahude ne ko Kirista ko waninsu (ba zai ji) kiran Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya isa zuwa gare shi ba, sannan ya mutu bai yi imani da shi ba sai ya zama daga 'yan wuta yana madawwami a cikinta har abada.
Daga Nana A'isha da Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - sun ce: Lakacin da (wafati) ya saukar wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara yana rufe fuskarsa da wani mayafinsa, idan ya ji ya yi masa tsanani sai ya yaye shi daga fuskarsa, sai ya ce yana hakan: "Tsinuwar Allah ta tabbata a kan Yahudawa da Nasara, sun riƙi kaburburan Annabawansu masallatai" yana gargaɗi game da abin da suka aikata.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiNana A'isha da Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - suna ba mu labarin cewa lokacin da wafati ya halartowa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya fara sanya wani yanki na riga a kan fuskarsa, idan numfashi ya wuyata a gareshi saboda magagin mutuwa, sai ya gusar da shi daga fuskarsa, sai ya faɗa a wannan halin mai tsanani: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, ya koresu daga rahamarSa; domin su sun gina masallatai a kan kaburburan Annabawansu, da ba don haɗarin al'amarin ba da bai ambace shi a irin wannan lokacin ba, saboda haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya hana al'ummarsa da kamanceceniya da wannan aikin; domin yana daga aikin Yahudawa da Nasara, kuma hanya ce da za ta kai zuwa ga shirka da Allah - mai girma da ɗaukaka.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki, Allah Ya la'anci mutanen da suka maida kaburburan Annabawansu masallatai".
Ahmad ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roki Ubangijinsa da kada Ya maida kabarinsa tamkar gunkin da mutane suke bauta masa ta hanyar girmama shi, da fuskantarsa a cikin sujjada, sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanar da cewa Allah Ya nisantar Ya kore wanda ya maida kaburburan Annabawa masallatai daga rahamarsa' domin maida su masallatai sila ce zuwa bauta musu da kuma kudircewa a cikinsu.