





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi ya ce: "Lallai cewa Gwaggwaben lada yana tare da Girman Bala'i kuma cewa Allah Mai girma da Daukaka idan yaso Mutane to sai ya Jarrabesu, to duk wanda yarda da Jarrabawar to sai ya sami yardar Allah, kuma duk wanda yayi fushi to shi ma sai Allah yayi fushi da shi"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shiAnnabi-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yana bamu labari acikin wannan Hadisi cewa Mumini wani lokaci wani abu na masibu yakan same shi akansa ko Dukiyarsa ko waninsa, kuma cewa Allah zai bashi lada akan kowace Musiba ce ta Sameshi, Sannan ya bayyana cewa Musibu koyaushe suka zamo Manya kuma hadarin su ya girmama to ladansu yakan girmama a wajen Allah Sannan Annabi yayi bayanin cewa cewa afkuwar Musibu yana daga cikin Alamomin Son Allah ga Mumini, Kuma Hukunin Allah da Kaddararsa babu Makawa sai sun afku, sai dai kuma wanda yayi Hakuri kuma ya yarda da Kaddarar , to Allah zai saka masa kan hakan da Yardarsa kuma babu ladan da yafi wannan, kuma duk wanda ya yayi fushi kuma yaki yarda da Kaddarar Allah to Allah zai fushi da shi , kuma babu ukubar da tafi wannan.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Lallai cewa Shi ne mafi wadatar abokanan tarayya game da shirka, to Shi ne Mawadaci daga dukkanin komai, kuma cewa mutum idan ya aikata wani aiki na biyayya kuma ya sanya shi ga Allah da kuma wanin Allah; to Zai bar shi ba zai karba daga gare shi ba, kuma Ya miyarwa da mai shi; To tsarkake aiki yana wajaba ga Allah - Madaukakin sarki -; domin cewa shi Allah tsarki ya tabbatar maSa ba ya karba sai abinda ya zama tsarkakakke ga zatinsa Mai girma.
Daga Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin mutuwarsa da (darare) biyar alhali shi yana cewa: "Lallai ni ina barranta zuwa ga Allah da ya zama ina da badadi daga cikinku, to lallai cewa Allah - Madaukakin sarki - hakika Ya rike ni badadi, kamar yadda Ya riki (Annabi) Ibrahim badadi, da na kasance mai rikon badadi daga al'ummata da na riki Abubakar badadi, ku saurara lallai wadanda suka gabace ku sun kasance suna maida kaburburan Annabawansu da salihansu masallatai, ku saurara kada ku maida kaburbura masallatai, lallai ni ina hanaku hakan".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincinAllah su tabbata a gare shi - ya sanar game da darajarsa a wurin Allah - Madaukain sarki -, kuma cewa ita takai mafi kololuwar darajojin soyayya, kamar yadda (Annabi ) Ibrahim - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya sameta, saboda haka ne ya kore ya zama cewa yana da wani badadi wanin Allah; domin cewa zuciyarsa ta cika da soyayyar Allah - Madaukakin sarki - da girmama Shi da saninsa, to ba ta yalwatuwa ga wani koma bayan Allah. Da a ce yana da wani badadi daga halitta da ya zama sayyidin Abubakar - Allah Ya yarda da shi -. Sannan ya yi gargadi daga ketare iyakar da ta halatta a cikin soyayya kamar yadda Yahudawa da Nasara suka aikata a kaburburan Annabawansu da salihansu har suka maida su alloli na shirka ana bauta musu koma bayan Allah, kuma suka sanya siminti da kayan alatu a kaburburan dake masallatai da guraren ibada, kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana al'ummarsa da su aikata irin aikinsu.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Yana kishi kuma Yana ki, kamar yadda cewa mumini yana kishi yana kuma ki, kuma cewa sababin kishin Allah shi ne mumini ya zo wa abinda Allah Ya haramta akansa na alfasha kamar ; zina da liwadi da sata da shan giya da wasunsu na alfasha.
Daga Abdullahi Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji wani mutum yana cewa: A'a na rantse da Ka'abah, sai Dan Umar ya ce: Ba'a rantsuwa da wanin Allah, domin cewa ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah da sunayensa da siffofinsa to hakika ya kafircewa Allah ko ya yi shirka; domin rantsuwa tana hukunta girmama wanda aka rantse da shi, girma kadai ya tabbata ga Allah ne Shi kadai; ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayensa da siffofinsa - tsarki ya tabbatar masa, Wannan rantsuwar tana daga karamar shirka; saidai da a ce mai rantsuwa ya girmama abinda ya rantse da shi kamar girmama Allah - Madaukakin sarki - ko sama da haka; to a wannan lokacin zai zama daga babbar shirka.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba da labari game da munafukai da kasalarsu a kan zuwa sallah, musamman ma sallar Issha'i da Asuba, kuma cewa su da ace suna sanin girman lada da sakamako a halartarsu tare da jama'ar musulmai da sun zo musu ko da da rarrafe ne kamar rarrafen yaro da hannaye da kuma gwiwoyi. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi niyyar ya yi umarni a tsai da Sallah, sai ya sanya wani mutumin ya yi wa mutane limanci a maimakonsa, sannan ya tafi tare da shi akwai wanda zai ɗauki ɗauri na itatuwa zuwa mazajen da ba sa zuwa sallar jama'a, sai ya ƙona gidajensu da wuta; sabo da tsananin abin da suka aikata na laifi a hakan, - sai dai bai aikata ba - sabo da abinda ke cikin gidaje na mata da yara da babu-ruwansu da kuma wasunsu cikin masu uzuri waɗanda ba su da wani laifi.
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Lallai cewa yana daga mafi sharrin mutane wadanda alkiyama zata riske su alhali suna raye, da wanda yake rikon kaburbura masallatai".
Ahmad ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da mafi sharrin mutane, cewa sune wadanda alkiyama zata tsaya akansu alhali su suna raye, da wadanda suke daukar kaburbura masallatai, suna sallah a wurinsu suna kuma kallonsu..
Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya, Allah - Mai girma da daukaka - Zai ce da su a ranar Alkiyama idan za’a yi wa mutane sakayyar ayyukansu: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna nuna musu ayyukanku a duniya, sai ku duba shin zaku samu wani sakamako a wurin su?".
Ahmad ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafi yawan abinda yake jin tsoronsa ga al'ummarsa: Karamar shirka ita ce: Riya; Ita ce ya yi aiki saboda mutane. Sannan ya bada labari game da ukubar masu riya a ranar Alkiyama za’a ce da su: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna aiki saboda su, ku duba shin suna mallakar saka muku da baku lada akan wannan aikin?!
An samo daga Adi Dan Hatim -Allah ya yarda dashi- "cewa ya ji Annabi -tsira da amincin Allah yana karanta wannan ayar: Sun riki malamansu "yahudawa" da malamansu "nasarawa" abin yiwa bauta ba Allah ba haka nan Isa Dan Maryam. kuma ba'a umarce su ba sai da cewa su bautawa abin bauta shi kadai wanda ba abin bautawa da cancanta sai shi tsarki ya tabbatar masa game da abin da suke yi masa tarayya? sai na ce da shi: lallai mu ba bauta musu muke yi ba. sai ya ce: shin ba haramta abin da Allah ya halatta suke ba sai ku ma ku haramta shi? kuma su halarta abin da Allah ya haramta ku ma ku halarta shi ba? sai nace: ey.Sai yace wannan ita ce bauta musu din."
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiyayin da wannan Sahabin mai girma yaji karatun Manzon Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-na wannan ayar wacce ta kunshi labarin yahudu da nasara:cewa sun mayar da malamansu da masu ibadar cikinsu abin bauta,suna shar'anta musu abinda yasabawa shari'ar Allah kuma suyi musu biyayya a kan haka,to sai ma'anar ayar ta rikitar,domin shi sahabin ya zaci cewa bauta ta takaita akan yin sujjada da makamantanta,sai Manzo -tsira da amincin Allah-ya bayyana masa cewa yana daga bautawa malamai yi musu biyayya a wajan haramta halal da kuma halarta haram,sabanin hukunci Allah madaukaki da Manzonsa tsira da aminci su tabbata a gare shi