





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkan abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son haddace shi, sai Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Shin ka dinga rubuta dukkan abin da ka ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, alhali Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin fushi da yarda? sai na dakata daga rubutun, sai na fadawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hakan sai ya yi nuni da 'yan yatsunsa zuwa bakinsa, sai ya ce: "Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiAbdullah ɗan Amr - Allah Ya yarada da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkanin abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - don na haddace shi a rubuce, sai wasu mutane daga Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin yarda da fushi, zai iya yin kuskure, sai na daina rubutun. Sai na ba wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - labarin abin da suka faɗa, sai ya yi nuni da danyatsansa zuwa bakinsa, sai ya ce; Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da yake fita daga cikinsa sai gaskiya a kowanne hali, haka a halin yarda da fushi. Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa game da AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ba ya magana bisa son rai* shi (Alƙur'ani) ba wani abu ba ne ba ban da wahayi da ake saukar masa) [Al-najm 3-4].
Daga Athilah Ibn Al-Asqa '- yardar Allah ta tabbata a gare shi - da isnadi: "Daya daga cikin mafi girman dalilai shi ne mutum ya yi addu'a ga wanin mahaifinsa, ko ya gani da idanunsa abin da ba ku gani ba, ko kuma ya ce wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da bai fada ba".
Buhari ne ya rawaito shiDaga Abu Abdurrahman Abdullahi ibnu Umar ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar dabi'un musulunci kamar cika ginin ne, Farkon wadanan rukunan: Shaidawa biyu; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (shaidawa) Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, su rukuni daya ne; dayansu ba ya rabuwa da dayan, bawa zai furtasu yana mai tabbatar da kadaituwar Allah da kuma cancantarSa ga bauta Shi kadai banda waninSa, kuma yana mai aiki da abinda suka hukunta, kuma yana mai imani da Manzancin Annabi Mukammadu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai binsa. Rukuni na biyu: Tsaida sallah, su ne sallolin farillai biyar a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da magariba, da Lisha, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu. Rukuni na uku: Fitar da zakkar farilla, ita ibada ce ta dukiya wajiba a kowacce dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga wadanda suka cancanceta. Rukuni na hudu: Hajji, shi ne nufin Makka dan tsaida ibadu, dan yin bauta ga Allah - Mai girma da daukaka -. Rukuni na biyar: Azumin Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga masu bata azimi da niyyar bauta ga Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana.
Daga Abu Abdurrahman Abdullahi ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya karantar da mu alhali shi mai gaskiya ne kuma abin gasgatawa: «Lallai cewa ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa kwana arba’in yana maniyyi, sannan ya zama gudan jini misalin haka, sannan ya zama gudan tsoka misalin haka, sannan a aiko masa da mala’ika sai ya busa masa rai, kuma a umarce shi da kalmomi guda huɗu: Da rubuta arziƙinsa, da ajalinsa, da aikinsa, kuma shi ɗan wuta ne ko ɗan aljanna ne, na rantse da wanda babu wani abin bautawa da cancanta in ba shi ba, lallai ɗayanku zai yi aiki irin na 'yan aljanna har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta sai zira’i, sai littafi ya rigaya a kansa, sai ya yi aiki aiki irin na 'yan wuta sai ya shige ta, kuma cewa ɗayanku zai yi aiki aiki irin na 'yan wuta har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta sai dai zira’i sai littafi ya rigaya a kansa, sai ya yi aiki aiki irin na 'yan aljannah sai ya shige ta».
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiDan Mas'ud ya ce:: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiyane a zancensa, kuma abin gasgatawa yayin da Allah - Madaukakin sarki - Ya gasgata shi. Ya ce: Lallai cewa dayanku ana taro halittarsa, cewa mutum idan ya zo wa iyalansa to tarwatsettsen maniyyinsa ana taroshi a cikin mace kwana arba'in yana maniyyi. Sannan ya zama gudan jini ita ce gudan jini mai kauri sandararre, wannan a arba'in ta biyu ne, Sannan ya zama gudan tsoka ita ce yanki na nama gwargwadan abinda ake taunawa, wannan a arba'in ta uku ce, Sannan sai Allah Ya aiko masa da Mala'ika, sai ya busa rai a cikinsa bayan karewar arba'in ta uku, Sai a umarci Mala'ikan da ya rubuta kalmomi hudu su ne: Arzikinsa, shi ne gwargwadan abin da zai samu daga ni'imomi a rayuwarsa, Da ajalinsa, shi ne gwargwadan wanzuwarsa a duniya, Da aikinsa, menene shi? dan wutan ne ko dan Aljanna ne. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa cewa; mutum zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna kuma aikinsa zai zama na gari, wato a abinda yake bayyana ga mutane, kuma ba zai gushe a haka ba har ya kasance tsakaninsa da ita bai zama ba sai zira'i daya, wato: Babu abinda zai wanzu tsakaninsa da tsakanin saduwa da ita aljannar sai kamar wanda zai zama tsakaninsa da tsakanin wani wuri na kasa zira'i daya ne, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa to a wannan lokacin zai yi aiki da aikin 'yan wuta sai a cika masa da shi sai ya shiga wutar; Domin cewa sharadin karbar aikinsa shi ne ya tabbata akansa ta yadda ba zai canjaba, wani dayan kuma daga mutane zai yi ayyukan 'yan wuta har sai ya kusanci shigarta, kuma gwargwadan zira'i ne na kasa zai kasance tsakakninsa da wutar, sai littafi ya rinjaya akansa da abinda aka kaddara akansa, sai ya yi aikin 'yan Aljanna kuma ya shiga Aljannar.
Daga uwar muminai Babar Abdullahi Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, ta ce: Manzon Allah - tsira amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki, to shi abun mayarwa ne». A cikin wata riwaya ta Muslim: «Wanda ya aikata wani aikin da babu umarninmu a cikinsa to shi abin mayarwa ne».
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nuni akansa ba na Alkur’ani ko hadisi, to shi abin juyarwane akan mai shi ba abin karba ba ne a wurin Allah.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: «Duk abin da na haneku daga gare shi to ku nisance shi, kuma abinda na umarce ku da shi to ku zo da shi dai dai iyawarku, domin abin da ya halaka magabatanku (shi ne) yawan tambayoyinsu da kuma saɓawarsu ga Annabawansu».
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana mana cewa shi idan ya hana mu wani abu to ya wajaba a kanmu mu nisance shi, ba tare da togaciya ba, idan kuma ya umarce mu da wani abu to wajibi ne a kanmu mu aikata abin da zamu iya daga gare shi. Sannan ya gargaɗemu dan kar mu zama kamar wasu daga cikin al'ummun da suka gabata lokacin da suka yawaita tambayoyi ga Annabawan su tare da saɓa wa annbawan, sai Allah Ya yi musu uƙuba da nau'ikan halaka da rusawa, to yana kamata kada mu zama irinsu dan kada mu halaka kamar yadda suka halaka.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karɓa sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}. Kuma Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama (yana cewa): Ya Ubangiji! ya Ubangiji! abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to ta yaya za'a amsa masa ga hakan?».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah tsarkakakke ne, tsarkakakke abin tsarkakewa daga nakasa kowacce iri da aibuka, kuma Mai siffantuwa ne da cika, ba Ya karɓar ayyuka da maganganu da ƙudirce-ƙudirce sai abinda ya kasance mai tsarki, shi ne tsantsa saboda Allah, wanda ya dace da shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, baya kamata a nemi kusanci zuwa ga Allah sai da hakan, daga mafi girman abinda tsarkin ayyuka yake faruwa ga mumini tsarkin abin cinsa, kuma ya zama na halal ne, da hakan ne aikinsa zai tsarkaka, saboda haka ne Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci manzanni da shi, na cin halal da aiki na gari, sai Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa} kuma Ya ce: {Ya ku wadanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirtaku}. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga cin haram wanda yake ɓata aiki kuma yake hana karɓarsa duk irin kokarin da ya yi na sabubban karɓar na zahiri; daga cikinsu: Na farko: Tsawaita tafiya ta fuskokin ayyukan ɗa'a kamar hajji da jihadi da sada zumunci da wanin hakan. Na biyu: Cukurkuɗar gashi dan rashin taje shi, wanda launinsa ya canja da launin tufansa daga turɓaya, shi mabuƙaci ne. Na uku: Yana ɗaga hannayensa sama da addu'a. Na huɗu: Yana tawassuli zuwa ga Allah da sunayenSa kuma yana nacewa a cikin hakan (yana cewa): Ya Ubangiji ya Ubangiji! A tare da waɗannan sabubban na amsar addu'a ba'a saurare shi ba; hakan saboda abin cinsa da abin shansa da abin ɗaurawarsa haramun ne, kuma an shayar da shi da haram, to ya nisanta a amsa wa wanda wannan ita ce siffarsa, to ta yaya za'a amsa masa?!
Daga Abul Abbas, Abdullahi ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wata rana, sai ya ce: «Ya kai yaro! zan sanar da kai wasu kalmomi: Ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka same shi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da ace al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru kuma a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka; an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe». A cikin wata riwayar da ba ta Tirmizi ba: «Ka kiyaye Allah zaka same shi a gabanka, ka nemi sanin Allah a lokacin wadata zai taimakeka a cikin tsanani, ka sani cewa abin da ya kuskure maka bai zama zai sameka ba, abin da kuma ya sameka bai zama zai kuskure maka ba, ka sani cewa nasara tana tare da haƙuri, kuma yaye baƙin ciki yana tare da farin ciki, kuma sauƙi yana tare da tsanani».
Tirmizi da Ahmad ne sun rawaito shiIbnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Zan sanar da kai wasu al'amura da wasu abubuwan da Allah zai amfanar da kai da su: Ka kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninSa da nisantar hane-hanenSa, ta inda Zai sameka a ayyukan biyayya da kusanci, ka da Ya sameka a ayyukan saɓo da zunubai, idan ka aikata haka sakamakonka zai kasance shi ne Allah Zai kiyayeka daga abubuwan ƙi na duniya da lahira, kuma Zai taimakeka a ayyukanka a duk inda ka fuskanta. Idan ka yi nufin roƙon wani abu, to, kada ka roƙi kowa sai Allah, to, domin haƙiƙa Shi Allah Shi kaɗai ne wanda Yake amsawa masu roƙo. Idan ka yi nufin neman taimako, to, kada ka nemi taimakon kowa sai Allah. Kuma ya zama kana da yaƙini cewa wani amfani ba zai sameka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya sun taru akan amfanarka sai dai abin da Allah Ya rubuta maka, kuma wani abin cutarwa ba zai faru a kanka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya za su taru a kan cutarka, sai dai abin da Allah Ya ƙaddara shi a kanka. Kuma wannan al'amarin tabbas Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya rubuta maka Ya kuma ƙaddara shi daidai da abin da hikimarSa da saninSa suka hukunta, babu canji ga abin da Allah Ya rubuta shi. Kuma cewa wanda ya kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninSa da nisantar hane-hanenSa; to Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana gaban bawa, Yana sanin abin da yake a kansa, kuma zai taimake shi Ya kuma ƙarfafe shi. Kuma lallai mutum idan ya bi Allah a cikin wadata to lallai cewa Allah zai sanya masa yayewa da mafita a lokacin tsanani, kuma kowane bawa ya yarda da abin da Allah Ya ƙaddara masa na alheri da na sharri. Kuma ya lazimci haƙuri a lokacin tsanani da kuma jarrabawa, domin haƙuri mabuɗin yaye baƙin ciki ne, kuma baƙin ciki idan ya yi tsanani sai yayewa tazo daga Allah, kuma cewa tsanani idan ya faru Allah sai Allah Ya biye masa da sauƙi.
Daga Abu Amr kuma an ce: Abu Amrata - Sufyan ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".
Muslim ne ya rawaito shiSahabi Sufayanu dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ya sanar da shi wata magana mai tattaro ma'anonin Musulunci, da zai yi riko da ita, wacce ba zai tambayi waninsa game da ita ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: Na kadaita Allah, kuma na yi imani da cewa Shi ne Ubangijina kuma Allah na, Mahaliccina, Abin bautata na gaskiya ba Shi da abokin tarayya, Sannan ya jawu ga biyayya ga Allah ta hanyar bada farillan Allah, da barin abubuwan da Allah Ya haramta, ya kuma ci gaba akansu.