





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi, sannan wasu masu sabawa zasu saba a bayansu suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umarce su ba, wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi muminin ne, kuma babu wani kwatankwacin kwayar komayya na imani bayan hakan".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a wata al'umma kafin shi sai ya kasance yana da tsarkakakku da mataimaka da mayaka masu ikhlasi a cikin al'ummarsa, wadanda suka cancanci kalifanci a bayansa; suna riko da sunnarsa, kuma suna koyi da umarninsa, sannan wasu mutane zasu zo bayan wadancan magabata na garin wadanda babu alheri a cikinsu; suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umartarsu; wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi muminin ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi mumini ne, kuma babu wani imani kwatankwacin kwayar komayya bayan hakan.
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba : An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata daya (gabanin haduwar mu), kuma an sanya mini kasa ta zama wajen yin sallah ta kuma mai tsarkakewa, don haka duk wanda sallah ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taba halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kadai , ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane baki daya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Ya ba shi wasu dabi'u uku (wadanda) bai bada su ga wani daga Annabwa a gabnina ba. Na farko: An bani nasara da tsoro da za'a jefa shi a cikin zukatan maƙiyana koda tsakanina da su akwai tafiyar wata. Na biyu: An sanya mana ƙasa ta zama masallacin da zamu dinga sallah a duk inda muke, kuma mai tsarkakewa da turɓaya a yayin rasa ruwa, ko gaza anfani da shi. Na uku: An halatta mana ganimomin yaƙi, sune waɗanda musulmai suke ɗiba a yaƙoƙinsu tare da kafirai. Na huɗu: An bani ceto mafi girma dan hutar da mutane daga firgicin tsayuwa a ranar Alkiyama. Na biyar: An aikoni zuwa halitta gaba ɗaya mutanensu da Aljanunsun, saɓanin Annabawa kafin ni sun kasance ana aikosu ne zuwa mutanensu ne kawai.
Daga Harisa ɗan Wahb alKhuza'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da Allah zai kuɓutar da shi, shin ba zan baku labarin 'yan wuta ba? duk mai ƙaton ciki mai kaushin rai mai girman kai".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin sashin siffofin 'yan aljanna da 'yan wuta. Mafi yawancin 'yan aljanna sune: "Dukkan mai rauni mai ƙanƙar da kai", wato: Mai ƙanƙan da kai mai ƙanƙanr da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki -, mai ƙasƙantar da kansa gareShi, har takai wasu daga mutane suna raunana shi kuma suna wulaƙanta shi, wannan mai ƙasƙantar da kai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da zai yi rantsuwa da Allah dan kwaɗayi a cikin karamcin Allah - Maɗaukakin sarki -, da Allah Ya kuɓutar da shi, kuma Ya tabbatar masa da abinda ya yi rantsuwa akansa kuma Ya amsa buƙatarsa da addu'arsa. Kuma mafi yawancin 'yan wuta su ne: Dukkan "Mai ƙaton ciki" shi ne mai kaushin zuciya, mai bushewar zuciya mai tsananin husuma, ko mai alfasha wanda ba ya jawuwa ga alheri, "Mai yawan girman kai" shi ne mai girman kai, mai yawan ci, mai ƙiba, mai taƙama a tafiyarsa, mai mummunar ɗabi'a, "Mai girman kai" saboda butulcewarsa ga gaskiya, da kuma wulaƙanta waninsa.
Daga Abu Huraira - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Akwai matakai dari a cikin Aljanna da Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin sahu biyu kamar tsakanin sama da kasa."
Buhari ne ya rawaito shiDaga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa gareNi yake, zan yi mu'amala da bawaNa gwargwadan zatansa da Ni, hakan dan ƙauna da burin rangwami, kuma Ina yi masa abinda yake tinanin afkuwarsa daga gareNi na alheri ne ko wanin hakan; kuma Ni ina tare da shi da rahama da dacewa da shiriya da kiyayewa da ƙarfafawa idan ya anbaceNi. Idan ya anbaceNi a cikin ransa shi kaɗai a kaɗaice da tasbihi da hailala ko waninsu; zan anbace shi a cikin raiNa. Idan ya anbaceNi a cikin jama'a; zan ambace shi a cikin jama'ar da tafisu yawa kuma ta fisu tsarki. Wanda ya nemi kusanci zuwa ga Allah gwargwadan taki Allah Zai yi masa ƙari sai Ya kusanto zuwa gare shi da zira'i. Idan ya nemi kusanci zuwa gare shi gwargwadan zira'i zai kusanto zuwa gare shi gwargwadan awon faɗin hannaye. Idan ya zo zuwa ga Allah yana tafiya to Allah zai zo masa Yana sassarfa. Bawa idan ya nemi kusanci zuwa ga Ubangijinsa da biyayya gareShi da fuskantowa gareShi, to lallai Ubangiji - Maɗaukakin sarki - Zai ƙara kusanci zuwa gareshi dan sakamako daga jinsin aikinsa. A duk lokacin da bautar mumini ta cika ga Ubangijinsa to Allah Maɗaukakin sarki zai kusanto zuwa gare shi, kyautar Allah da sakamakonSa (ita ce ) mafi yawa daga aikin bawa da kuma wahalarsa, a taƙaice cewa sakamakon Allah mai rinjaya ne akan aiki ta hanyar kaifiyya da kuma kimmiya. Mumini yana kyautata zato, kuma yana aiki, yana gaggawa yana ƙarawa har ya gamu da Allah.
Daga Dalha ɗan Ubaidullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum daga mutanen Najad ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai dattin kai, muna jin ƙarfin muryarsa, ba ma fahimtar abinda yake faɗa har ya kusanto ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai gashi yana tambaya game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Salloli biyar a yini da dare" sai ya ce: Shin akwai wasu kuma akaina? ya ce: "A'a, sai dai idan ka yi nafila. Da azumin Ramadan”. Sai ya ce: Shin akwai wani kuma?. sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Saidai idan ka yi na nafila. Sai ya ambata masa zakka, sai ya ce: Shin akaina akwai waninta ? ya ce: "A'a, saidai idan ka yi nafila", ya ce: Sai mutumin ya juya baya, yana cewa: Na rantse da Allah, ba zan kara akan wannan ba, kuma ba zan rage daga gare su ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ya rabauta idan gasgata hakan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiWani mutum daga cikin mutanen Najad ya zo wurin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - gashinsa ya yi datti, kuma muryarsa mai ƙarfi, ba'a fahimtar abinda yake faɗa, har ya kusanto ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi tambaya game da farillan musulunci? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara da sallah, kuma ya sanar da shi cewa Allah Ya faralanta masa salloli biyar a cikin kowanne yini da dare. Sai ya ce: Shin wani abu daga salloli sun wajaba a kaina banda waɗannan biyar ɗin? Sai ya ce: A'a, sai dai idan ka yi nafila daga sallolin nafila. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Daga abinda Allah Ya wajabta shi akanka azumin watan Ramadan. Sai mutumin ya ce: Shin akwai wani abu na azimi da ya wajaba a kaina banda azimin Ramadan? Sai ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila da wani azimi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ambata masa zakka. Sai mutumin ya ce: Shin wani abu na sadaka bayan farillar zakka ya wajaba a kaina? Ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila. Bayan mutumin ya ji waɗannan bayanai daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya juya baya ya yi rantsuwa da Allah - Maɗaukakin sarki - cewa shi zai dawwama a kansu ba tare da ƙari ko ragi ba, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce bayan haka: Idan ya gasgata abinda ya faɗa akan abinda ya rantse akansa to shi zai zama daga masu rabauta.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a, a cikinsa ne aka halicci (Annabi) Adam, kuma a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, kuma a cikinsa ne aka fitar da shi daga gareta, kuma AlKiyama ba za ta tsayaba sai a ranar Juma'a".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafificin yinin da rana ta ɓullo a ciknsa shi ne yinin Juma'a. Daga abinda (ginin Juma’a) ya keɓa ta da shi: Allah Ya halicci (Annabi) Adam - aminci ya tabbata agare shi - a cikinsa, a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, a cikinsa ne aka fitar da shi daga aljannar, kuma aka sakko da shi ƙasa, Alkiyama ba za ta tashiba sai a yinin Juma'a.
Daga Abu Hurairah - yardar Allah ta tabbata a gare shi - a kan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: “Bari babban mutum mai kiba ya zo ranar tashin kiyama, kuma ba zai yi zina da Allah ba kamar reshen sauro.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiBabban mutum wanda yake da katafaren tsari kuma yake da girman kai game da halittar Allah a wannan duniya yana da girman kai da girman kai ta hanyar ayyukansu da kalamansa, domin kuwa a ranar tashin kiyama ba zai sanya wa sauro wani bangare na Allah ba, kuma ba shi da wata kima ko matsayi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wani musulmi ba zai suturta ɗan uwansa musulmi ba a cikin wani al'amari daga al'amura, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya suturta shi a ranar alƙiyama; sakayya tana daga jinsin aiki, kuma suturcewar Allah gare shi zai zama da suturcewar laifukansa da saɓonsa daga yaɗasu ga ma'abota taron alƙiyama, zai iya kasancewa da barin yi masa hisabi akansu da kuma anbata masa su.