





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Muslim Al-Khaulani ya ce: Masoyi amintacce ya zantar dani, amma shi to masoyi ne gareni, amma shi a wajena to amintaccene, Awf Dan Malik Al-Ashja'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - (Mu) tara ko takwas ko bakwai, sai ya ce: "Shin ba kwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" mun kasance farkon yin caffa (mubaya’a) sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan ya ce: "Shin bakwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan Ya ce: "Shin bakwa wa Manzon Allah caffa ba?" Ya ce: Sai muka shimfida hannayenmu muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai" Hakika na ga sashin wadancan mutanan bulalar dayansu tana faduwa, amma ba ya tambayar wani ya miko masa.
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wani adadi na sahabbai sai ya nemi su yi masa caffa su yi masa alkawari akan lazimtar wasu al'amura har sau uku: Na farko: Bautar Allah Shi kadai ta hanyar riko da umarninSa, da nisantar haninSa, kuma kada su hada wani abu daShi. Na biyu: Tsaida salloli biyar na wajibai a yini da dare. Na uku: Ji da bi da aikin alheri ga wanda ya jibinci al'amarin musulmai. Na hudu: Kai dukkanin bukatunsu ga Allah da rashin tambayar mutane wani abu daga garesu, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kasa-kasa da sautinsa da su. Hakika sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi aiki da abinda suka yi caffa akansa, har maruwaicin Hadisin ya ce: Hakika na ga wasu daga wadancan sahabban bulalar dayansu tana faduwa kasa , amma ba ya tambayar wani ya miko masa ita, kai yana sauka yana daukarta da kansa.
Daga Bara'u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne". to wannan shi ne faɗinSa: {Allah Yana tabbatar wa waɗanda suka yi imani da faɗa tabbatacciya a cikin rayuwar duniya da kuma lahira} [Ibrahim: 27].
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiZa'a tambayi mumini a cikin ƙabari, sai mala'iku biyu waɗanda aka wakilta da hakan su tambaye shi su ne Munkar da Nakir, kamar yadda ambatansu ya zo a Hadisai masu yawa, sai ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: wannan shi ne tabbatacciyar magana wacce Allah Ya faɗa a cikinta: {Allah Yana tabbatar da wadanda su ka yi imani da magana matabbaciya a rayuwar duniya da kuma a lahira} [Ibrahim: 27].
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka, idan suka aikata hakan sun tsare jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai dai da hakkin Musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya umarce shi da yakar mushrikai har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma su shaida manzanci ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da aiki da abinda wannan shaidar ta hukunta na kiyayewa akan salloli biyar a yini da dare, kuma su bada zakka ta wajibi ga wadanda suka cancanta. Idan suka aikata wadannan al'amuran to Musulunci ya tsare jinanensu da dukiyoyinsu, kashe su ba ya halatta sai dai idan sun aikata laifi ko wata barnar da za su cancanci kisa akanta, ta hanyar wajabcin hukunce-hukuncen Musulunci, sannan ranar AlKiyama Allah - Madaukakin sarki - Zai jibinci hisabunsu inda Yake sanin sirrikansu.
Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».
Ibnu Majah da Baihaki da wasun su ne suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Lallai Allah Ya yi wa al'ummarsa rangwame akan halaye uku: Na farko: Kuskure, shi ne abin da ya bijiro daga garesu ba tare da ganganci ba, kuma shi ne musulmi ya nufi wani abu da aikinsa sai aikin na sa ya dace da abin da bai yi nufi ba. Na biyu: Mantuwa, shi ne musulmi ya zama mai tina wani abu, saidai a lokacin aikata shi sai ya manta shi, to babu zunubi a kan hakan. Na uku: Tilastawa, za’a iya tilastawa bawa yin wani aikin da bai yi nufinsa ba tare da rashin ikonsa akan tunkuɗe tilastawar, a wannan lokacin zunubi ko ƙunci ba zai faɗa kansa ba. Tare da lura da cewa matashiyar hadisin a abin da ke tsakanin bawa da Ubangijinsa ne, a kan aikata abinda aka haramta, amma barin abin da aka yi umarni akan mantuwa to ba zai saraya ba, amma da ace wani laifi zai faru akan aikinsa to ba zai sarayar da wani haƙƙi na abin halitta ba, kamar yadda da ace zai yi kisa akan kuskure, ko ya lalata wata mota akan kuskure to wajibi ne ya biya.
A kan hadisin A’isha, Allah Ya yarda da ita, ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce, kuma babu wani abu a gidana da wani mai hanta zai iya ci sai guntun sha’ir a cikin rake domin ni.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Safwan ɗan Muhriz ya ce: Wani mutum ya ce wa Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - yaya ka ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: A (sha'anin) sirri? ya ce: Na ji shi yana cewa: "Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - har sai ya sanya kiyayewarSa, sai Ya tabbatar masa da zunubansa, sai Ya ce: Shin kana sane ? sai ya ce: Eh ya Ubangiji ina sani, ya ce: Lallai cewa Ni haƙiƙa Na suturtasu gareka a duniya, kuma cewa lallai Ni Zan gafarta maka su a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa, amma kafirai da munafukai, sai a kirasu akan kawunan halittu waɗannan sune waɗanda suka yi wa Allah ƙarya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ganawar Allah ga bawanSa mumini ranar alƙiyama, sai ya ce: Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa sai Ya sanya suturarSa daga ma'abota wurin tsayuwa har ya zama waninsa ba zai yi tsinkaye akan sirrinsa ba, sai ya ce masa: Shin kana sanin zunubi kaza da kaza... Zai tabbatar masa da zunuban da suke tsakanin bawa da UbangijinSa. Sai ya ce: Na'am Eh, ya Ubangiji. Har idan mumini ya firgita ya ji tsoro, sai Tsarki ya tabbatar maSa Ya ce masa: Lallai cewa Ni na suturta su gareka a duniya, kuma cewa Ni na gafartasu gareka a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa. Amma kafiri da munafuki sai a yi kira a gabn mahalarta: Waɗannan sune waɗanda suka yi wa Ubangijinsu ƙarya, ku saurara tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai.
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, sai ya ce: "Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa, ka bautawa Allah kada ka yi shirka da komai da Shi, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin Allah”, sannan ya ce: "Shin ba na shiryar dakai ba ga ƙofofin alheri: Azimi garkuwa ne, sadaka tana kashe kuskure kamar yanda ruwa yake kashe wuta, da sallar mutum a tsakiyar dare" ya ce: Sannan ya karanta: "{Sasanninsu suna nisanta daga makwantansu}, har ya kai {Suke aikatawa}". Sannan ya ce: "Shin bana baka labari da asalin al'amari gaba dayansa ba da ginshikinsa, da kololuwar tozansa?" Na ce: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: "Asalin al'amari Musulunci, kuma ginshikinsa sallah, kuma kololuwar tozansa Jihadi" sannan ya ce: "Shin bana baka labari da abinda zai tattaro hakan gaba dayansa ba?" na ce: Eh, Ya Manzon Allah, sai ya rike harshensa ya ce: "Ka rike wannan", na ce Shin za’a kama mu da abinda muke magana da shi? ya ce: "Babarka ta yi wabinka ya Mu'az, ai ba wani abu ne yake afka mutane cikin wuta ta fuskokinsu ko ta hancinansu ba sai abinda harasansu suke girba".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiMu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna kan tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar da ni aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, Ya ce: Haƙiƙa ka tambayeni daga wani aiki mai girman aikatawa ga rayuka, kuma mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa; ka yi farillan Musulunci: Na farko: Ka bauta wa Allah Shi kaɗai kada ka taranya wani abu da Shi. Na biyu: Ka tsaida salloli biyar na farilla a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da Magariba, da Isshai, da sharuɗɗansu da rukunansu da wajibansu. Na uku: Ka fitar da zakkar farilla, ita ce ibada ta dukiya wajiba a kowace dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga waɗanda suka cancanceta. Na huɗu: Ka azimci Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga abubuwan da suke karya azimi da niyyar bauta, daga ɓollowar alfijir zuwa faɗuwar rana. Na biyar: Ka ziyarci Ɗakin Allah, da nufin Makka dan yin ibadun aikin Hajji, dan bauta ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin ba na sanar da kai hanya mai kaiwa ga ƙofofn alheri ba? hakan da bin waɗancan farillan da nafilfilin: Na farko: Azimin nafila, shi mai hanawa ne daga afkawa cikin saɓo, hakan da karya sha'awa, da kuma rage ƙarfi. Na biyu: Sadakar nafila tana kashe laifuka bayan an aikata su kuma tana tafiyar da su tana kuma shafe su. Na uku: Sallar dare a kashi ɗaya bisa uku na ƙarshen dare, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Sasanninsu suna nisanta} wato: Suna nisanta {Daga makwantansu} wato: Wuraren kwana { Suna kiran Ubangijinsu} da yin sallah da zikiri da karatu da addu'a, {Dan tsoro da kwaɗayi kuma suna ciyarwa daga abinda muka azirta su, wata rai bata sanin abinda aka ɓoye musu na abinda ido yake farin ciki da shi} wato abinda idanunsu zasu yi farin ciki da shi a ranar Alƙiyama da kuma aljanna ta ni'ima, {Dan sakamako da abinda suka kasance suna aikatawa}. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin bana baka labari da asalin Addini ba? da ginshiƙinsa wanda yake dogaro akansa? da ƙololuwar tozansa? Mu'az - Allah Ya yarda ad shi - ya ce: Eh, ya Manzon Allah. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Asalin al'amari: Musulunci shi ne shaidawa biyu, kuma dasu ne tushen Addini zai wayi gari tare da mutum. Ginshiƙinsa: Sallah, babu Musulunci ba tare da sallah ba, kamar yadda babu gida ba tare da ginshiƙi ba, wanda ya yi sallah Addininsa zai ƙarfafa zai ɗaga; kuma ƙololuwar tozansa da ɗaukakarsa yana kasancewa ne da yin yaƙi da yin ƙoƙari a yaƙar maƙiya Addini dan ɗaukaka kalmar Allah. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin ba na baka labari da kyautata abinda ya gabata ba? sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe harshensa, ya ce: Ka hana wannan kada ka yi magana da abinda bai shafeka ba. Mu'az ya ce: Shin Ubangijinmu zai kamamu Ya yi mana hisabi da dukkan abinda muke magana da shi?! Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Mahaifiyarka ta yi wabinka! ba ana nufin mummunar addu'a akansa ba, sai dai yana daga zancen larabawa dan faɗakar da shi zuwa wani al'amarin da ya kasance yana kamata ya farka da shi ya kuma san shi, sannan ya ce: Ai babu abinda yake afka mutane ya jefasu cikin wuta ta fuskokinsu sai abinda harasansu suke girba na kafirci da ƙazafi da zagi da yi da mutum da annamimanci da ƙagen ƙarya da makamancinsu.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}. [al-Mu'uminun: 51] . Kuma Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. [al:Baƙara: 172]. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah tsarkakakke ne, tsarkakakke abin tsarkakewa daga nakasa kowacce iri da aibuka, kuma Mai siffantuwa ne da cika, ba Ya karɓar ayyuka da maganganu da ƙudirce-ƙudirce sai abinda ya kasance mai tsarki, shi ne tsantsa saboda Allah, wanda ya dace da shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, baya kamata a nemi kusanci zuwa ga Allah sai da hakan, daga mafi girman abinda tsarkin ayyuka yake faruwa ga mumini tsarkin abin cinsa, kuma ya zama na halal ne, da hakan ne aikinsa zai tsarkaka, saboda haka ne Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci manzanni da shi, na cin halal da aiki na gari, sai Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa} kuma Ya ce: {Ya ku wadanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirtaku}. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga cin haram wanda yake ɓata aiki kuma yake hana karɓarsa duk irin kokarin da ya yi na sabubban karɓar na zahiri; daga cikinsu: Na farko: Tsawaita tafiya ta fuskokin ayyukan ɗa'a kamar hajji da jihadi da sada zumunci da wanin hakan. Na biyu: Cukurkuɗar gashi dan rashin taje shi, wanda launinsa ya canja da launin tufansa daga turɓaya, shi mabuƙaci ne. Na uku: Yana ɗaga hannayensa sama da addu'a. Na huɗu: Yana tawassuli zuwa ga Allah da sunayenSa kuma yana nacewa a cikin hakan (yana cewa): Ya Ubangiji ya Ubangiji! A tare da waɗannan sabubban na amsar addu'a ba'a saurare shi ba; hakan saboda abin cinsa da abin shansa da abin ɗaurawarsa haramun ne, kuma an shayar da shi da haram, to ya nisanta a amsa wa wanda wannan ita ce siffarsa, to ta yaya za'a amsa masa?!
Daga Miƙdadu ɗan Amr mutumin Kindi - Allah Ya yarda da shi -: Cewa shi ya cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Shin kana ganin cewa idan na haɗu da wani mutum daga kafirai sai muka yi faɗa, sai ya daki ɗaya daga hannayena da takobi sai ya yanke shi, sannan ya fake dani da wata bishiya, sai ya ce: Na miƙa wuya ga Allah, shin zan kashe shi ya Manzon Allah bayan ya faɗeta? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ka kashe shi" sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa shi ya yanke mini ɗaya daga hannayena, sannan ya faɗi hakan bayan ya yanke mini shi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ka kashe shi, domin cewa in ka kashe shi to shi yana matsayinka kafin ka kashe shi, kuma kai kana matsyinsa kafin ya fadi kalmarsa wacce ya fadeta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiMikdadu ɗan alAswad - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi idan ya gamu da wani mutum daga kafirai a yaƙi, sai suka yi fito na fito da takubba, har kafirin ya samu ɗaya daga hannayen sa da takobi sai ya yanke shi, sannan kafirin ya gudu daga gare shi ya katangantu da wata bishiya, sai ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shin ya halatta a gareni in kashe shi bayan ya yanke hannuna? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Kada ka kashe shi. Sai ya ce ya Manzon Allah, lallai cewa shi ya yanke ɗayan hannayena, shin a tare da hakan ba zan kashe shi ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ka kashe shi, domin cewa shi ya wayi gari jininsa haramun ne, domin cewa kai in ka kashe shi bayan musuluntarsa; to cewa shi a matsayinka ne wanda jininsa abin tsarewa ne da musuluntarsa, kuma kai kana matsayinsa abin halaratawar jini da ka kashe shi dan yin ƙisasi.