





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - an daga hadisin zuwa ga Annabi, Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya bada labari cewa: " shi zai zo y yi sujjada ga Ubangijinsa ya kuma yi godiya [ba da ceto zai fara ba] , sai a ce da shi: " Dago kanka ka fada za'a ji, ka roka a baka, ka nemi ceto za'a baka ceton."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiManzo mai tsira da amincin Allah zai zo ranar kiyama sai ya yi sujjada ga Allah ya kuma roke shi,sai Allah ya yi masa izini da yin ceto mafi girma, sai Ubangjinsa yace da shi: roki a baka kuma ka nemi ceto a baka, duk bukatarka an karba maka, cetonka kuma an baka
Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce a washegarin jifan babban shaidan alhali shi yana kan taguwarsa: "Ka tsintomin tsakwankwani". sai na tsinto masa tsakwankwani bakwai, su tsakwankwani ne na harbi, sai ya fara yana motsasu a tafinsa yana cewa: "Misalan wadananan sai ku yi jifa (da su)”. sannan ya ce: "Yaku mutane na haneku da wuce gona da iri a addini, kadai wuce gona da iri a addini shi ya halaka wadanda ke gabanku".
Ibnu Majah da Nasa'i da Ahmad ne suka ruwaito shiIbnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - a ranar babbar sallah wayewar garin jifan babban Shaidan a hajjin bankwana, sai ya umarce shi ya tsinto masa tsakwankwanin jifa, sai ya tsinto masa tsakwankwani bakwai, kowacce daya daga cikinsu ta kai girman wake ko bunduq, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -ya sanya su a hannu sa, sannan ya motsa su, ya ce: Ku yi jifa da kwatankwacin wannan a girma, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar daga wuce gona da iri da tsanantawa da ketare iyaka a al'amuran addini, kadai ketare iyaka da wuce gona da iri da tsanantawa a addini shi ya halaka al'ammomin da suka gabata.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka guje wa kuturu kamar yadda kake guje wa zaki".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin al'amuran Jahiliyya (maguzawa) dan gargaɗi daga gare su, da kuma bayanin al'amari yana hannun Allah, kuma wani abu ba ya kasancewa sai da umarninSa da ƙaddarawarSa, su ne: Na farko: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna zatan cewa cuta tana yaɗuwa da kanta; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga ƙudirce tashin cuta daga mara lafiya zuwa ga mai lafiya da ɗabi'arta; Allah Shi ne Mai tasarrufi a cikin kasantattu; kuma Shi ne wanda Yake saukar da cuta kuma Yake ɗauketa, hakan ba ya faruwa saida nufinSa da ƙaddarawarSa. Na biyu: Mutanen Jahiliyya sun kasance idan sun fita dan wata tafiya ko kasuwanci, sai su yi wa tsuntsu tsawa, idan ya tashi ɓangaren dama sai su yi murna, idan ya tashi ɓangaren hagu sai su canfa su dawo, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga wannan canfin da tsuntsu, ya kuma bayyana cewa hakan akida ce ɓatacciya. Na uku: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna cewa: Idan mujiya ta faɗo a kan wani gida sai musiba ta samu mutanen wannan gidan; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani game da canfa hakan. Na huɗu: Ya yi hani daga canfa watan Safar, shi ne wata na biyu daga watannin ƙamariyya. (Wasu kuma) suka ce Safar shi ne: Wata micijiya ce da take a ciki tana samun dabbobi da mutane, suna riya cewa ita ce mafi tsananin yaɗuwa daga cutar kirci; sai ya kore wannan akidar. Na biyar: Ya yi umarni da nisantar wanda aka shafa da cutar kuturta kamar yadda zaka nisanci zaki, hakan dan bai wa kai kariya da kuma nema masa kuɓuta da kuma aikata sabubban da Allah ya yi umarni da su. Kuturta: Wata cuta ce da gaɓɓan mutum suke cin juna daga gareta.
An karbo daga Al-Hassan cewa ya ce: "Babu sihiri da yake halatta sai mai sihiri."
Ibnu Abi Hatim ya rawaito shi - Al-Khattabi Ya Rawaito shiSanarwa ita ce maganin sihiri, kuma bayyananniyar ma'anar kalaman Hassan haramun ne kwata-kwata Saboda wanda yake da ilimin sihiri ne kawai yake iya warware sihiri, kuma wannan ya halatta ya narkar da sihiri da sihiri irinsa, kuma aikin Shaidan ne, kuma Ibnul-Qayyim ya yi bayani dalla-dalla kan abin da ya samu: cewa yi wa masu sihir da magunguna halatta da karatun Alkur'ani ya halatta - kuma bi da shi da sihiri kamar shi haramun ne.
Daga Abdullah bn Abbas - Allah ya yarda da shi - wanda ya ce: "Mene ne sammai bakwai da kassai bakwai a cikin tafin Mai rahama, sai dai a matsayin kwaya a hannun dayanku".
Ibn Jareer ne ya Rawaito shi - Al-Thahabi Ya Rawaito shi a Babin Uluwwi (Daukakar Allah bisa Bayinsa( - Abdullahi Bn Al-Mam Ahmad Ya Rawaito shiIbn Abbas - Allah ya yarda da shi - ya gaya mana a cikin wannan rahoton cewa, adadin sammai bakwai da duniyoyi bakwai da kashinsu zuwa tafin Mai rahama yana kama da matsayin karamin mustard zuwa tafin dayanmu. Domin Allah baya kama da sifofinsa kamar wani abu makamancin nasa.
Daga Abu Dhar al-Ghafari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - da sarkar makamai: "Kujerar tana cikin karaga sai dai kamar zoben karfe da aka jefa a tsakanin bayana na masu gidan."
Ibnu Abi Shaiba ne ya rawaito a Babin Magana kan Al'arshi - Al-Thahabi Ya Rawaito shi a Babin Uluwwi (Daukakar Allah bisa Bayinsa(Yana fada - Allah ya kara masa tsira da aminci - a cikin hadisin Abu Dharr cewa kujera, tare da karfi da girma dangane da karaga, kamar zoben karfe ne wanda aka sanya shi a cikin jejin kasa mai fadi. Wannan yana nuna girman Mahaliccin sa da kuma cikakken ikon sa.
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Babu ciratar cuta kuma babu camfi, fatan alkairi yana birgeni" ya ce: A ka ce : Menene fatan alkairi? sai ya ce: "Magana mai dadi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah agare shi - yana bada labarin cewa ciratar cutar da mutanen Jahiliyya suke ƙudircewa da cewa cuta tana cirata da kanta zuwa wani ba tare da ikon Allah ba da cewa batacce ne, (ba haka ba ne). kuma camfi batacce ne, shi ne camfi na kowanne abu, abin ji ne ko abin gani, na tsuntsaye ne ko dabbobi ko masu tawaya ko lambobi ko ranaku ko wanin hakan, kadai ya ambaci canfi ne domin cewa shi ne ya fi shahara a lokacin Jahiliyya, asalinsa shi ne sakin tsuntsu a lokacin fara wani aiki na tafiya ne ko kasuwanci ko makamancin hakan, idan ya tashi ta bangaren dama sai ya yi yunkuri ya ci gaba da abinda yake nufi, idan ya tashi bangaren hagu sai ya camfa ya ki yin abinda yake nufi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa shi fata na gari yana ƙayatar da shi, shi ne abinda yake faruwa ga mutum na farin ciki da nishadi na wata magana mai dadi da zai ji ta, ta kuma sanya shi ya dinga kyautata zato ga Ubangijinsa.
Daga Al-Barra - Allah Ya yarda da shi -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi cewa shi ya fada a sha'anin mutane Madina: "Ba mai sonsu sai mumini, kuma babu mai kinsu sai munafiki, wanda ya so su Allah zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa son mutanen Ansar daga mutanen Madina, alama ce akan cikar imani; wannan dan rigayarsu a taimakon Musulunci da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kokari akan tarbar musulmai, da bada dukiyoyinsu da rayukansu a tafarkin Allah, kuma cewa kinsu alama ce ta munafunci. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa wanda ya so mutanen Madina Allah Zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da sahabbai akan su yi aiki, kuma su ji tsoron Allah gwargwadan ikonsu, ba tare da zurfafawa ko Gazawa ba, kuma su nufi daidai da aikinsu ta hanyar ikhlasi ga Allah da bin sunna dan a karɓi aikinsu sai su zama sababi ga saukar rahama garesu. Sannan ya ba su labarin cewa wani mutum aikinsa kawai ba zai tseratar da shi ba; kai babu makawa daga rahamar Allah. Suka ce: Har kai Ya Manzon Allah aikinka ba zai tseratar da kai ba tare da girman darajarsa? Sai ya ce: Har ni, sai dai in Allah Ya suturtani da falalar rahamarSa.