





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
"Kursiyyu shi Bugirem kafafuwan, Kuma Al-Arshi ba'a iya Kaddara shi da komai
Ibn Khuzaimah ya rawaito shi a Babin magana kan Al-Tauhidi - Abdullahi Bn Al-Mam Ahmad Ya Rawaito shi a cikin littafin SuunahAn rawaito daga Abdullahi Bn Masud -Allah ya yarda da shi: Lallai cewa wani Byahude ya zo wajen Annabi sai ya ce da shi ya muhammad, Cewa Allah ya rike Sammai kan Yatsa daya, Kuma Kassai Kan Yatsa daya, kuma Duwatsu kan Yatsa daya, kuma Bushiyu Kan Yatsa daya, Kuma Halittu kan Yatsa daya, sannan ya ce: Ni ne Sarki
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiWannan Hadisin yana nuna girman Allah -Madaukaki- yada ya sanya sammai baki dayan su akan Dan yatasa daya daga cokin Yan yatsun Masu girma da Karamci, kuma ya kidanye Halittu sanannu ga Halitta da kuma girmansa da Daukaka, kumaya bada labari cewa kowane nau'i daga cikin su -yana sanya shi- akan Danyatsa daya, da kuma Allah yaga dama da ya sanya sammai da kassai da abunda ke tsakaninsu a kan Dan yatsa daya daga cikin Yan Yatsun Hannunsa -Mai girma da daukaka- kuma wannan yana daga cikin Ilimin da aka gada daga Annabaw, wanda aka karbo shi ta Hanyar Wahayi daga Allah -Madaukakin Sarki- saboda haka Manzon Allah ya gasgata Maganar bayahude kai yayi mamakin ta har yayi farin ciki da ita, shi yasa yayi Dariya kar aka ga firorinsa, don gasgata shi Kamar yadda Abdullahi Bn Mas'ud ya ce: a cikin wata Riwaya daban daga gare shi, juma Aannabi ya Karanta fadin Allah Madaukakin Sarki: "Basu girmama Allah ba Matukar girmamawa kuma Kasa tana tana damkinsa a Ranan Al-kiyama kuma Sammai suna nannade a Hannun gamansa tsarki ya tabbata ga Allah kuma ya daukaka game da Abunda suke masa shirka da shi" wacce akwai tabbatar da Hannaye ga Allah Madaukakin Sarki, saboda tabbaraewa da abin da bayahude ya ce: kuma ko kallo bai isa ba abunda wadanda suke Musanta Siffofin Allah, ya kore sifar Yatsu ga Allah, yana mai rayawa cewa tabbatar da ita ga Allah siffata shi ne da Halittarsa, kuma bap sani ba wannan Mai Musun Siffofin Allah cewa tabbatar da wannan cewa tabbatar da siffofin Allah baya nuna Kamanceceniya, kamar yadda cewa Mu muna tabbatar Masa da Rayuwa da iko da Karfi da kuma ji da gani, kuma hakan baya nuna cewa Kamanceceniya da Haliiarsa, saboda shi Allah Madaukakin Sarki "Babu wani abu Kwatankwacinsa kuma shi mai ji ne Kuma Masani"
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ""Lallai Allah Ya ce: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba, bawa Na ba zai gushe ba yana kusanta gareNi da nafilfili har sai Na soshi, idan Naso shi zan zama jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake dauka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma da zai rokeni sai na ba shi, kuma da zai nemi tsari da Ni sai Na tsare shi, kuma ban taba kai komo a kan yin wani abu kamar karbar ran mumini ba, yana kin mutuwa Ni kuma iNa ki masa wahalarsa"
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin a cikin Hadisi Kudsi cewa Allah - Mai girma da daukaka - Ya ce: Wanda ya cutar da wani masoyi daga masoyana ya fusatar da shi ya ki shi to hakika Na sanar da shi na shelanta masa kiyayya. Waliyyi shi ne: Mumini mai tsoron Allah, kuma gwargwadan abinda ke ga bawa na imani da tsoron Allah rabonsa na walicci yake kasancewa. Musulmi bai nemi kusanci ga Ubangijinsa ba da wani abu daga abinda Ya fi soyuwa gare Shi kamar wanda ya wajabta masa na aikata biyayya da barin abubuwan da aka haramta, kuma musulmi ba zai gushe ba yana kara kusanci ga Ubangijinsa da nafilfili tare da farillai ba; Har sai ya samu soyayyar Allah. Idan Allah Ya so shi, to Allah Zai zama Mai daidaita shi a wadannan gabobin guda hudu: Zai daidaita shi a jinsa, ba zai ji komai ba sai abinda Allah Ya yarda da shi. Kuma Zai daidaita shi a ganinsa, ba zai kalli komai ba sai abinda Allah Yake son kallo zuwa gare shi kuma Ya yarda da shi. Kuma Zai daidaita shi a hannunsa, ba zai aikata komai da hannunsa ba sai abinda zai yardar da Allah. Kuma Zai daidaita shi a kafarsa, ba zai yi tafiya ba sai inda zai yardar da Allah, kuma ba zai yi wani kokari ba sai abinda acikinsa akwai alheri. A tare da hakan idan ya roki Allah wani abu to lallai Allah zai ba shi abinda ya roka, sai ya zama wanda ake amsawa addu'a, idan ya nemi tsarin Allah ya fake gareShi dan neman tsari, to cewa Allah Zai tsare shi Zai kare shi daga abinda yake jin tsoro. Sannan Allah - Madaukakin sarki - Ya ce: Ban yi wani kai kawo ba game da wani abu da Ni zan aikata shi ba kamar kaikawo Na a karbar ran mumini dan tausayinsa; Domin shi yana kin mutuwa, dan abinda ke cikinta na radadi, Allah kuma Yana kin abinda zaisa mumini jin radadi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da ɗabi'u biyu a cikin mutane suna daga ayyukan kafirai, da kuma ɗabi'un Jahiliyya, su ne: Na farko: Sukar nasabobin mutane da tauyesu da yi musu girman kai. Na biyu: Ɗaga murya a lokacin masifa dan yin fushi akan ƙaddara, ko yaga tufafi saboda tsananin baƙin ciki.
An rawaito daga Imrana Bn Husain Allah ya yarda da shi Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada ga wanda ya ga a hannunsa akwai kewaye na daga tagulla, sai y ace masa menene wannan? Sai y ace maganin raunin tsufa ne.sai y ace masa jefar da ita domin ita ba za ta kara maka komai ba face rauni,domin cewa da ka mutu tana jikinka dab a za ka rabauta ba har abada
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiImrana Bn Hussain -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi yana bada Labarin wani Mataki daga cikin Matakan da Manzon SAW akan yakar Shirka da kuma tsamo mutane daga cikinta wannn Matsayi shi ne lokacin da yaga wani Mutum ya sanya wata Kawanya da akayita da Azurfa fara, sai ya tambayi mai dauke da ita dalilin sanya ta ? sai ya amsa da cewa shi ya sanya ta ne don ta kare shi daga Radadi, sai yai Umarni da gaggawar jefar da ita, sai ya bashi labarin cewa bazata anfanar da shi ba aa ma zata cutar da shi ne, kuma cewa ita zata kara Masa Cutar ne wacce ya sanya abun saboda ita, kuma mafi girma daga hakan shi ne da zai ci gaba kan hakan har mutuwarsa za'a harmta masa rabauta a cikin Duniya da Lahira kuma.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)? suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dirhami ko kaya, sai ya ce: "Lallai cewa muflis daga al'ummata zai zo ranar alƙiyama da sallah da azumi da zakka, zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, kuma ya yi wa wannan ƙazafi, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya daki wannan, sai a bawa wannan daga kyawawan ayyukansa, wannan ma daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukansa sun ƙare kafin a biya abin ke kansa sai a ɗauka daga kurakuransa sai a watsa masa, sannan a watsa shi a cikin wuta".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin kun san waye muflis? suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dukiya ko kaya, sai ya ce: Lallai muflis daga al'ummata zai zo ranar lahira da ayyuka na gari na sallah da azumi da zakka. Kuma zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, ya yi wa wannan ƙazafi a mutuncinsa, kuma ya ci dukiyar wannan ya yi musunta, kuma ya zubar da jinin wannan ya zalinci shi, ya daki wannan ya wulaƙantashi, sai a bawa wanda aka zalinta daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukan suka ƙare kafin ya biya abinda ke kansa na haƙƙoƙi da abubuwan da aka zalinta, sai a ɗauki zunuban wanda aka zalinta sai a sanya su a takardun azzalimin, sannan a watsa masa sai a jefa shi a cikin wuta inda babu wani kyakkyawan aiki da zai rage gare shi .
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta, sai a ƙona shi a kansu a cikin wutar Jahannama, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas, duk lokacin da suka ƙone sai a dawo da su, a cikin wani yinin da gawargwadansa shekara dubu hamsin ne, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai yaga hanyarsa, ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta". Aka ce : Ya Manzon Allah, to raƙuma fa? ya ce: "Ko ma'abocin raƙuma da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, yana daga haƙƙinsu tatsar nonnuwansu lokacin gangarowarsu (ruwa), sai ya kasance a ranar lahira za'a shinfiɗa su a ƙasa miƙaƙƙiya, mafi cikar abinda da suke, ba zai rasa wani ɗan maraƙi ɗaya ba, zasu dinga taka shi da kofatansu, kuma zasu dinga cizansa da bakunansu, duk lokacin da na farkonsu ya shuɗe a kansa sai a dawo da na ƙarshensu, a cikin wani yinin da ya kasance gwargwadansa shekara dubu hamsin ne, har sai an yi hukunci tsakanin mutane, sai ya ga hanyarsa ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta". Aka ce: Ya Manzon Allah, to shanu da tumakai fa? ya ce: "Ko ma'abocin shanu, ko tumakai, ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai ranar lahira ya kasance an shinfiɗa musu mikaƙƙiyar ƙasa, ba zai rasa wani abu daga cikinsu ba, babu wata mai lanƙwasasshen ƙaho, ko mara ƙaho, ko mai karyayyen ƙaho zasu dinga sukarsa da ƙahonhunansu, kuma zasu dinga taka shi da kofatansu, duk lokacin da na farkonsu ya wuce a kansa za'a dawo da na ƙarshensu, a cikin wata ranar da gwargwadanta ya kai shekara dubu hamsin, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, zai ga hanyarsa ko dai zuwa aljanna, ko kuma zuwa wuta" Aka ce : Ya Manzon Allah, to doki fa? ya ce: "Doki uku ne: (Doki) laifi ne ga wani mutumin, kuma su sutura ne ga wani mutumin, kuma su lada ne ga wani mutumin. Amma waɗanda suke su laifi ne gare shi, shi ne mutumin da ya ɗauresu dan riya da alfahari da ƙiyayya ga ma'abota Musulunci, to su laifi ne akansa, amma waɗanda su sutura ne gare shi, to shi ne mutumin da ya ɗauresu saboda Allah, sannan bai manta haƙƙin Allah a bayayyakinsu ko wuyayensu ba, to su sutura ne gare shi, amma waɗanda su lada ne gare shi, shi ne mutumin da ya ɗauresu saboda Allah dan ma'abota Musulunci, a cikin ciyayi da dausayi, duk abinda suka ci na wancan ciyayin ko dausayin, sai an rubuta masa kyakkyawan lada adadin abinda suka ci, kuma an rubuta masa kyakkyawan lada adadin torosonsu da fitsarinsu, ba zaka yanke igiyarsu ba su yi sukuwa tsawon saki daya ko biyu, sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa n lada adadin gurbinsu da torosonsu, kuma ma'abocinsu bai wuce akan wata korama ba, su sha daga gareta kuma ba ya nufin ya shayar da su, sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa adadin abinda suka sha"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana nau'ika na dukiya, da sakamakon wanda bai bada zakkarsu ba a ranar alƙiyama, daga cikinsu: Na farko: Zinare da azirfa da abinda ke cikin hukuncinsu na dukiyoyi da hajoji na kasuwanci, shi ne abinda zakka ta wajaba a cikinsa bai bayar ba, idan ranar alƙiyama ta zo za'a narka su aƙerasu akan siffar alluna, kuma a kunna wutar Jahannama a kansu, a yi masa azaba da su, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas da su, duk lokacin da suka yi sanyi sai a dawo da ƙunarsu, zai kasance a wannan halin na azaba tsawon ranar alkiyama wanda gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta. Na biyu: Wanda ya mallaki raƙuman da ba ya bada farillar zakkarsu da kuma haƙƙinsu, daga ciki (akwai) tatsar nonansu ga wanda ya zo nema cikin miskinai, za’a zo da waɗannan raƙuman masu girma masu ƙiba kuma mafi yawa kan yadda suke a cikin adadinsu, za'a shinfiɗa shi a jefa shi a miƙar da mai su ranar alƙiyama akan wata ƙasa mai yalwa miƙaƙƙiya, zasu dinga takashi da ƙafafunsu, kuma zasu dinga cizonsa da haƙoransu, duk lokacin da na ƙarshensu ya wuce akansa za'a dawo da na farkonsu a kansa, zai zarce akan wannan halin na azaba tsawon yinin alƙiyama wace gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta. Na uku: Wanda ya mallaki shanu da tumakai - wadanda suke tunkiyoyi da awakai - waɗanda mai su ba ya bada zakkarsu ta wajibi, za’a zo da su mafi yawan abinda da suke akai na adadi ba za’a tauye komai ba daga garesu, sai a shinfiɗasu a jefa shi kuma a miƙar da mai su a ranar lahira akan ƙasa mai yalwa madaidaiciya, babu wasu masu lanƙwasasshen ƙaho, ko waɗanda ba su da ƙahon, ko masu karyayyen ƙaho, kai su akan mafi cikar siffofinsu ne, sai su soke shi da ƙahonhunansu, kuma su taka shi da ƙafafuwansu, duk lokacin na ƙarshensu ya wuce a kan shi sai a dawo da na farkonsu. Zai ci gaba akan wannan halin na azaba tsawon yinin alƙiyama wacce gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta. Na huɗu: Wanda ya mallaki dawakai, su dawakai nau'i uku ne: Na farko: Su laifi ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan riya da alfahari da kuma yaƙar ma'abota Musulunci. Na biyu: Su sutura ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan yin yaƙi a tafarkin Allah, sannan ya kyautata musu da ciyar da su da ragowar ɗawainiyarsu, daga cikinsu (akwai) barbarar namijinsu. Na uku: Su lada ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan yin yaƙi a tafarkin Allah ga ma'abota Musulunci, su a cikin ciyayinsu da dausayinsu dan yin kiwo, to ba abinda zasu ci sai an rubuta masa kyakkyawa adadin abinda suka ci, kuma an rubuta masa kyakkyawa adadin torosonsu da fitsarinsu, ba'a yanke igiyarsu ba, ita ce igiyar da ake ɗauresu a cikinta, suka yi gudu kuma suka yi sukuwa a ƙasa maɗaukakiya; sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa adadin gurabensu da torosonsu, kuma ma'abocinsu bai wuce ba akan wata ƙorama sai su sha daga gareta kuma ba ya nufin ya shayar da su, sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa adadin abinda suka sha . Sannan aka tambayi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi game da jakuna shin su irin dawakai ne? Sai ya ce: Shar'antawa bai sauka ba a sha'aninsu sai dai wannan ayar wacce irinta kadan ne, ita mai gamewa ce ga dukkan nau'ikan ɗa'a da saɓo; ita ce faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Wanda ya aikata kwatankwacin ƙwayar komayya na alheri zai gan shi, wanda yaaikata kwatankwacin ƙwayar komayya na sharri zai ganshi}. [al-Zilzalah: 8], wanda ya yi aiki a cikin mallakar jakai dan yin ɗa'a zai ga ladan hakan, idan kuma ya aikata saɓo to zai ga uƙubar hakan, kuma wannan mai ƙunsar dukkan ayyuka ne.
Daga Adiyyu ɗan Hatim - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu, sai ya duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa hagunsa shima ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa gabansa ba zai ga komai ba sai wuta wajen fuskarsa, to ku ji tsoron wuta ko da kuwa da gutsiren dabino ne".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkan mumini zai tsaya a gaban Allah a ranar lahira shi kaɗai, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi magana da shi ba tare da wani wasiɗa ba, kuma babu wani tafinta a tsakaninsu wanda zai fassara zancen, sai ya yi duba ɓangaren dama da hagu saboda tsananin firgici, wataƙila zai samu hanyar da zai gudu a cikinta dan ya tsira daga wutar dake gabansa. Idan ya yi duba a ɓangaren da ke damansa ba zai ga komai ba sai abinda ya aikata na aiki na gari Idan ya yi duba a hagunsa ba zai ga komai ba sai abinda ya gabatar na mummunan aiki, idan ya duba gabansa ba zai ga komai ba sai wuta, kuma babu abinda zaisa shi kauce mata dan babu makawa daga wucewa akan siraɗi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ku sanya kariya tsakaninku da wuta da sadaka da aiki na gari, koda da wani sassauƙan abu ne kamar rabin dabino.
Daga Uƙuba ɗan Amir Aljuhani - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wasu mutane sun fuskanto gare shi , sai ya yi wa tara daga cikinsu caffa (Mubaya’a) yaki yi wa ɗaya, sai suka ce: Ya Manzon Allah, ka yi wa tara caffa ka bar wannan? ya ce: "Atare da shi akwai laya". Sai ya shigar da hannunsa sai ya yanketa, sai ya yi masa caffa, ya ce: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".
Ahmad ne ya rawaito shiWasu jama'a sun zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, adadinsu su goma ne, sai ya yi Mubaya’awa tara daga cikinsu (Wato caffa) akan Musulunci da bi, bai yi wa na goman ba, yayin da aka tambaye shi game da sababin hakan sai tsira da amincin su tabbata agare shi ya ce: Lallai atare da shi akwai laya, ita ce abinda ake ɗaurawa ko ake ratayawa na laya (guru ko kamun) ko waninsa don tunkuɗe kanbun baka ko wata cuta. Sai mutumin ya shigar da hannunsa gurin layar ya yanketa ya kuɓuta daga gareta, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa caffa, ya ce yana mai gargaɗarwa daga layu yana mai bayyana hukuncinsu: "Wanda ya rataya laya to haƙiƙa ya yi shirka".