





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, sai ya ce: "Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka, an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe".
Tirmizi ne ya ruwaito shiIbnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: Zan sanar da kai wasu al'amura da wasu abubuwan da Allah zai amfanar da kai su: Ka kiyaye Allah ta hanyar kiyaye umarninsa da nisantar hane-hanensa, ta inda Zai sameka a ayyukan biyayya da kusanci, ka da Ya sameka a ayyukan saɓo da zunubai, idan ka aikata haka sakamakonka zai kasance shi ne Allah Zai kiyayeka daga abubuwan ƙi na duniya da lahira, kuma Zai taimakeka a ayyukanka a duk inda ka fuskanta. Idan ka yi nufin roƙon wani abu, to, kada ka roƙi kowa sai Allah, to, haƙiƙa Shi kaɗai ne wanda yake amsawa masu roƙo. Idan ka yi nufin neman taimako, to, kada ka nemi taimakon kowa sai Allah. Kuma ya zama kana da yaƙini cewa wani amfani ba zai sameka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya sun taru akan amfanarka sai dai abin da Allah Ya rubuta maka, kuma wani abin cutarwa ba zai faru a kanka ba, ko da mutanen duniya gaba ɗaya za su taru a kan cutarka, sai dai abin da Allah Ya ƙaddara a kanka. Kuma wannan al'amarin tabbas Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya rubuta maka ya kuma ƙaddara shi daidai da abin da hikimarsa da saninsa suka hukunta, babu canji ga abin da Allah Ya rubuta.
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi", suka ce: ya Manzon Allah, wa zai ƙi? ya ce: "Wanda ya bi ni zai shiga aljanna, wanda ya saɓa min to haƙiƙa ya ƙi".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin al'ummarsa za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi! Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka ce: Wa zai ƙi ya Manzon Allah?! Sai (manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya amsa musu cewa: wanda ya miƙa wuya ya bi Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - zai shiga aljanna, amma wanda ya saɓa bai miƙa wuya ga shari'a ba, to, haƙiƙa ya hanu daga shiga aljanna da ayyukansa munana.
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu".
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane daga kafirai ko fasiƙai ko mutanen kirki - ta yadda zai aikata wani abu daga abin da ya keɓancesu daga aƙidu ko ibadu - to, yana daga cikinsu; domin kamanceceniya da su a zahiri yana kaiwa zuwa kamanceceniya da su a ɓoye, kuma babu kokwanto cewa kamanceceniya da mutane yana haifuwa ne daga sha'awarsu, kuma ya kan kai zuwa ga soyayyarsu da girmamasu da karkata zuwa garesu, wannan yana jan mutum zuwa ya yi kama da su har a ɓoye da ibada - Allah Ya yi mana tsari-.
Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne zunubine mafi girma a wurin Allah? ya ce: " Ka sanyawa Allah kishiya alhali Shi Ya halicceka" Na ce: Lallai wannan mai girmane, na ce: Sannan wanne? Ya ce: "Ka kashe danka; dan tsoron ya ci tare da kai". Na ce: Sannan wanne? ya ce: "Ka yi zina da matar makocinka".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAntambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga mafi girman zunubai sai ya ce: Mafi girmansu babbar shirka, ita ce ka sanya tamka ko kini ga Allah a AllantakarSa ko UbangidantakarSa ko sunayenSa da siffofinSa, wannan laifin Allah - Madaukakin sarki - ba ya gafartashi saida tuba, idan mai aikata shi ya mutu akansa to shi madawamine a cikin wuta. Sannan mutum ya kashe dansa dan tsoron ya ci tare da shi, kashe rai kuwa haramun ne, saidai zunubinsa yana girmama idan wanda aka kashe din yana da alaka ta jini da wanda ya yi kisan, kuma zunubinsa yana girmama yayin da manufar wanda ya yi kisan ta zama dan tsoron ya yi tarayya da wanda aka kashe din ne a arzzikin Allah. Sannan mutum ya yi zina da matar makocinsa shi ne ya yi kokarin rudar da matar makocinsa har ya yi zina da ita ta mika wuya gare shi . Zina haramun ce , saidai zunubinta yana girmama idan wacce aka yi zinar da ita matar makoci ce wanda shari'a ta yi wasicci da kyautatawa zuwa gareshi da yi masa kirki da kayauta zama da shi.
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi hani game da ƙauracewar musulmi ga ɗan uwansa musulmi sama da dare uku, kowane ɗaya daga cikinsu zai haɗu da ɗayan, amma ba zai yi masa sallama ba, kuma ba zai yi masa magana ba. Mafificin waɗannan masu husumar biyun shi ne wanda zai yi ƙoƙarin gusar da ƙauracewar, kuma ya fara yin sallama, abin nufi da ƙauracewa a nan shi ne na son rai, amma kauracewa saboda haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - kamar ƙauracewa masu saɓo da 'yan bidi'a da mugayen abokai, to, wannan ba a iyakanceshi da wani lokaci, kawai ya na rataya ne da maslaha a ƙauracewar, kuma yana gushewa da gushewarta.
Daga Abu Sirmah - Allah Ya yarda da shi - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiAnnabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi gargaɗi game ga shigar da cuta ga musulmi, ko riskar da wahala a gareshi a kowane al'amari daga al'amauransa; a ransa ko a dukiyarsa ko a iyalansa, kuma cewa wanda ya aikata hakan Zai yi masa sakayya, Zaiyi masa uƙuba daga jinsin aikinsa.
Daga Jariri dan Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiSahabbai sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare sai ya dubi wata - daren goma sha hudu -, sai ya ce: Lallai muminai za su ga Ubanbijinsu a hakika da ido ba tare da wani rikici ba, kuma cewa su ba za su yi cunkoso ba, kuma wahala ba zata samesu ba ko tsanani a yayin ganinsa - Madaukakin sarki -. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan kuna da ikon yanke abubuwan da zasu hana ku sallar Asuba da sallar La'asar to ku aikata, ku zo da su (Sallolin) a cike a lokacinsu a cikin jama'a, domin cewa hakan yana daga sabubban gani zuwa fuskar Allah - Mai girma da daukaka -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta ayar: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kafin faduwarta}.
Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan cewa ci gaba da zalunci da laifuka da shirka da zaluntar mutane a haƙƙoƙinsu, to, lalle Allah maɗaukaki Yana saurarawa azzalumi ya jinkirta masa, ya tsawaita masa a rayuwarsa da dukiyarsa ba zai gaggauta masa uƙuba ba, to, idan bai tuba ba sai ya damƙe shi, kuma ba zai sake shi ba, ba kuma zai ƙyale shi ba sabo da yawan zaluncinsa. Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karanta: Kuma haka damƙar Ubangijinka take idan ya damƙi alƙaryu suna azzalumai, lalle damƙarsa mai raɗaɗi ce kuma mai tsanani ce.
Daga Abu Hayyaj Al’asadi, ya ce: Aliyu Ɗan Abi Talib, ya ce da ni: Shin ba na aika ka ba a kan abin da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aike ni ba?? Kada ka bar mutum-mutumi sai ka share shi, haka kabari da aka ɗaga shi sai ka daidaita shi (da sauran kaburbura).
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana aika sahabbansa a kan kada su bar ((mutum-mutumi)) na wani abu da yake da rai aka gina shi ko ba gina shi aka yi ba, sai sun kawar da shi, sun shafe shi. Kuma kada su bar kabari wanda aka ɗaga shi sai sun daidaita shi da ƙasa, sun rushe ginin da aka yi, ko sun sanya shi a shafe kada ya daga a bayan kasa ɗagawa mai yawa, kawai ya ɗaga kamar ɗani guda.