





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce bai tashi daga gareta ba: «Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai» ta ce; Da badan haka ba da an bayyanar da ƙabarinsa, sai dai cewa an ji tsoron a riƙe shi a matsayin masallaci.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiNana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa a cikin rashin lafiyarsa wacce ta tsananta gare shi kuma ya mutu a cikinta: Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, Ya koresu daga rahamarSa; hakan domin cewa su sun riƙi ƙaburburan Annabawansu a matsayin masallatai. Ta hanyar yin gini a kansu ko yin sallah a wurinsu ko zuwa garesu (kallonsu). (Nana A'isha) Allah Ya yarda da ita ta ce: Da badan wannan hanin da gargaɗin daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tsoron sahabbai kan abinda za’a yi wa ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar yadda Yahudawa da Nasara suka yi wa ƙaburburan Annabwansu ba da anbayyanar da ƙabarinsa kuma an fito da shi.
Daga Abu Sa'idul Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya aikewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani gutsire na zinare a cikin wata fatar da aka jeme da ƙwallan bagaruwa, ba'a gama tace shi daga ƙasarta ba, ya ce: sai ya raba shi tsakanin mutum huɗu, tsakanin Uyaina ɗan Badr da Aƙra'a ɗan Habis da Zaidul Khail, na huɗun: Ko dai Alƙama ko Amir ɗan Ɗufail, sai wani mutum daga sahabbansa ya ce: Mu mun kasance mu ne mafi cancantar wannan daga waɗannan (mutane huɗun), ya ce: Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Shin bakwa amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda ke sama, labarin sama yana zo mini safiya da yamma", ya ce: Sai wani mutum ya mike mai kogon idanuwa, mai manyan kumatu, goshin shi ya yi sama, mai kaurin gemu, mai askakken kai, yana ɗaure da zani, sai ya ce: Ya Manzon Allah ka ji tsoron Allah, ya ce: "Kaicanka, shin ba ni ne nafi cancantar fin kowa tsoron Allah daga mutanen dake ƙasa ba" ya ce: Sannan mutumin ya juya baya, Khalid dan Walida ya ce: Ya Manzon Allah, shin bana daki wuyansa ba? ya ce: "A'a, wataƙila yana sallah" Khalid ya ce: da yawa mai sallar da yake faɗa da harshensa abinda ba ya cikin zuciyarsa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya ce: "Lallai ni ba'a umarceni ba in bibiyi zukatan mutane ba ko na tsaga cikkunansu ba" ya ce: sannan ya yi duba zuwa gare shi alhali shi ya juya baya, sai ya ce: "Lallai cewa wasu mutane zasu fito daga tsatson wannan suna karanta Littafin Allah danye a zuciyarsu, ba ya ketare zukatansu zasu fita daga Addini kamar yadda kibiya take fita ga kwarin da aka harba, ina zatan ya ce: Wallahi idan na riskesu zan kashesu irin kisan Samudawa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya yi aike zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Yaman da wani gutsire na zinari a cikin wata fata da aka jemeta da bagaruwa, gutsiren zinaren ba’a gama wanke shi daga ƙasarsa ba, ya ce: Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rarraba shi tsakanin mutum huɗu: Uyaina ɗan Badr al-Fuzari, da Aƙra'a ɗan Habis al-Hanzali, da Zaidul Khail al-Nabahani, da Alƙama ɗan Alasa al-Amiri, sai wani mutum daga sahabbansa ya ce: Mune mafi cancanta da wannan (kyautar) daga waɗannan, ya ce: Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Shin ba za ku amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda ke sama, labarin sama yana zo mini safiya da yamma". Sai ya ce: Sai wani mutum ya miƙe idanuwansa sun shige cikin raminsu, kuma kundukukinsa ya fito, mai babban goshi, kuma gemunsa mai kaurine ba mai tsawo ba ne, mai askakken kai, yana janye da zaninsa wanda yake rufe ƙasan jikinsa da shi, sai ya ce: Ya Manzon Allah ka ji tsoron Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Kaiconka, shin ba ni ne mafi cancantar mutanen dake doron ƙasa da jin tsoron Allah ba?!» Ya ce: Sannan mutumin ya juya baya, Khali ɗan Walid ya ce: Ya Maonzon Allah, shin ba na daki wuyansa ba? Ya ce: A'a, wataƙila yana sallah, sai Khalid ya ce: Da yawa mai sallar da yake faɗa da harshensa abinda babu shi a cikin zuciyarsa, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai cewa ni ba'a umarceni in bibiyi zukatan mutane ba ko in tsaga cikinsu ba; kaɗai an umarcenine in yi hukunci da zahirin al'amuransu, ya ce: Sannan ya kalle shi a lokacin ya juya baya, sai ya ce: Lallai wasu mutane zasu fito daga tsatson wannan da sahabbansa ko ƙabilarsa masu yawan hazaƙa a karatun Littafin Allah da murya mai daɗi, harsunansu ɗanyu ne saboda yawan karanta shi, Alƙur'ani ba zai wuce maƙogwaransu ba, sai zukatansu su kiyaye shi sai su gyara shi, kuma Allah ba Zai ɗaga shi (gareShi) ba kuma ba zai karɓe shi ba, zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga baka da aka harba da sauri kuma a ɓoye. Kuma ina zatansa ya ce: Wallahi idan na riski tawayensu akan musulmai da takobi zan yaƙesu yaƙi mai tsanani kamar mutanen Samudawa.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce : «Lallai mafi ƙankantar matsayin ɗayanku a cikin aljanna shi ne Ya ce masa: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, sai Ya ce da shi: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce da shi: Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi ƙanƙantar matsayi da daraja ga wanda ya shiga aljanna shi ne Ya ce da shi: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, har sai ya zama babu wani burin da zai rage masa sai ya ambace shi , sai Ya ce masa: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce masa: To lallai kana da abinda ka yi burin dama kwatankwacinsa tare da shi.
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wani nama sai aka ɗaga masa zira'i, ya kasance yana ƙayatar da shi sai ya gutsira daga gare shi gutsira (ɗaya), sannan ya ce: "Ni ne shugaban mutane a ranar alƙiyama, shin kun san daga menene hakan? Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba, sai mutane su ce: Shin bakwa ganin abinda haƙiƙa ya kai muku ? shin bakwa duba wanda zai yi muku ceto zuwa ga Ubangijinku ba? sai wasu daga mutane su ce wa wasu: Ku je gurin (annabi) Adam, sai su zo wa Adam - aminci ya tabbata agare shi - sai su ce masa: Kai ne uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya busa maka daga ranSa, kuma Ya umarci mala'iku sai suka yi maka sujjada, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana? sai Adam ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushi a yau bai taba irin wannan fushin ba, kuma ba zai taba yin irin wannan fushin ba, kuma lallai ni hakika Ya hanani daga bishiya sai na saba maSa, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Nuhu. Sai su zo wa (annabi) Nuhu sai su ce: kai Nuhu, lallai kai ne farkon manzanni zuwa mutanen kasa, hakika Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana, shin baka nema mana ceto ga Ubangijinka ba? sai ya ce: Lallai Ubangijina Ya yi fushi a yau bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba, kuma lallai cewa ni akwai mummunar addu'ar da na yi akan mutanena, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi gurin (annabi) Ibrahim. Sai su zo wa (annabi) Ibrahim sai su ce: kai Ibrahim, kai ne Annabin Allah kuma badaɗayinSa daga mutanen ƙasa, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce musu: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba irinsa, lallai cewa ni na yi ƙarya sau uku, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga (annabi) Musa. Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai Musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijnka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai ni naa kashe wani rai da ba'a yi umarni da in kasheta ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Isa. Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: kai Isa, kaine Manzon Allah kuma kalmarSa da ya jefata zuwa Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfidar goyo, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai Isa ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, ba zai anbaci wani zunubi ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -". Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce kai ne Manzon Allah kuma cika makin Annabawa, hakika Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai in tafi, sai in zo ƙarƙashin al’arshi sai infaɗi ina mai sujjada ga Ubangina, sannan Allah Ya buɗe mini daga godiyarSa da kyakkyawan yabo gareShi na wani abinda bai taɓa buɗewa wani a gabani na ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka shi, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in dago kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Uabngiji, sai ace: Ya Muhammad ka shigar daga al'ummarka wadanda babu wani hisabi akansu ta kofar dama daga kofofin aljanna, kuma su suna tarayya da mutane a koma bayan haka na kofofi". sannan ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lalai tsakanin ginshikai biyu daga ginshikan aljanna kamar tsakanin Makka ne da Hajar, ko tsakanin Makka ne da Busra".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance tare da sahabbansa a wata liyafa ta abinci, sai aka kawo masa zira'in akuya kuma ya kasance shi ne mafi ƙayatarwar namanta gare shi , sai ya gutsiri wani gutsire da gefen haƙoransa sannan ya zantar da su, sai ya ce: Nine shugaban 'ya'yan Adam a ranar alƙiyama; hakan dan zantarwa da ni'imar Allah - Maɗaukakin sarki -. Sannan ya ce: Shin kun san saboda me hakan? ya ce: Mutane za'a tarasu ranar alƙiyama a wata ƙasa mai faɗi madaidaiciya miƙaƙƙiya miƙewa ɗaya, waɗanda ke cikinta mai kira zai jiyar da su kuma mai kallo zai kewaye da su wani abu daga garesu ba zai ɓoyar masa ba; dan daidaituwar ƙasar a cikinta babu abinda wani zai ɓoyewa masu gani da shi, kuma gani zai zarce musu, yana nufin da ace mutum zai yi magana da mutum na ƙarshe zai ji su, ido kuma zai gansu, rana zata kusantowa halittu gwargwadan mil, kuma baƙin ciki da ɓacin rai zai riskesu abinda ba za su iya ɗauka ba kuma ba za su iya jurewa ba, sai su nemi tsira da ceto. Sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya yi wa masu imani ilhama cewa su zo wajen (annabi) Adam uban mutane, sai sū zo masa su ambaci falalarsa, wataƙila zai nema musu ceto a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, zasu ce masa: Kai ne Adam uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya sa mala'ikunSa sun yi maka sujjada, kuma Ya sanar da kai sunayen komai, kuma Ya yi busa a cikinka daga ranSa, sai ya yi hanzari sai ya ce: Lallai cewa Ubangijina Ya yi fushi a yau, fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, sannan ya ambaci kuskurensa, shi ne cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya hane shi cin bishiya sai ya ci, kuma zai ce: raina, shi ne wanda ya cancanci a nema masa ceto ku tafi zuwa wanina ku tafi zuwa Nuhu. Sai su zo wa (annabi) Nuhu; sai su ce: Kai ne farkon Manzon da Allah Ya aiko shi zuwa mutanen ƙasa, kuma cewa Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, sai dai cewa shi zai yi hanzari: Cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, lallai cewa akwai wata mummunar addu'a da ya yi ta akan mutanensa, raina shi ne wanda ya cancaci a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Ibrahim. Sai su zowa (annabi) Ibarhim sai su ce: Kai ne badaɗayin Allah a cikin ƙasa, ka nema mana ceto zuwa Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai ya ce musu: Lallai cewa Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa yin irinsa ba kafinsa, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, kuma lallai haƙiƙa na kasance na yi ƙarya ƙarya uku; sune faɗinsa: Lallai ni mai rashin lafiya ne, da faɗinsa: Babbansu ne wannan ya aikata, da faɗinsa: Ga matarsa Saratu ki ba shi labarin cewa ni ɗan uwanki ne dan ya kuɓuta daga sharrinsa. Gaskiya cewa kalmomin uku kawai sun kasance ne a zunubin zance, sai dai yayin da surarsu suka kasance surar ƙarya sai ya ji tsoro daga garesu dan ƙanƙar da kai daga ceto; domin cewa wanda ya kasance mafi sanin Allah kuma mafi kusancin matsayi ya kasance mafi girman tsoro, sai ya ce: Raina shi ne wanda ya fi cancantar a nema masa haka, ku tafi zuwa wanina ku tafi zuwa Musa. Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda mu muke cikinsa?! sai ya ce: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushin da bai taɓa fushi irinsa ba kafinsa, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai cewa ni haƙiƙa na kashe wani mutum da ba'a umarce ni na kashe shi ba, raina shi ne wanda ya fi cancanta a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Isa ɗan Maryam. Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: Kai (annabi) Isa kaine Manzon Allah, kuma kalmarSa da Ya jefata zuwa ga Nana Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfiɗar goyo alhali kana ƙarami, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai ya ce: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushin da bai taɓa fushi irinsa kafinsa ba ko sau ɗaya, kuma ba zai yi fushi irinsa a bayansa ba, bai ambaci wani zunubi ba, raina shi ne wanda ya fi cancantar a nema masa ceto, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga Muhammad. Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce: Ya Muhammad Kai ne Manzon Allah kuma cikamakin Annabawa, haƙiƙa Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa?! sai in tafi sai in je ƙarƙashin al’Arshi, sai in faɗi ina mai sujjada ga Ubangijina - Mai girma da ɗaukaka -, sannan Ya yi mini buɗin wani abu na gode maSa da kyakkyawan yabonSa, bai yi taba buɗi ga wani a gabana ba kafin ni ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in ɗaga kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangijina, al'ummata ya Uabangijina, sai akarɓi cetansa. Sai ace masa: Ya Muhammad ka shigar da wanda babu hisabi a kansu daga al'ummarka ta ƙofar dama daga ƙofofin aljanna, kuma su abokanan tarayya ne a cikin koma bayan hakan na ƙofofi. Sannan ya ce: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lallai tsakanin sasanni biyu na ƙofa daga ƙofar aljanna, kamar tsakanin Makka da San'a'a ta Yamen ne, ko kamar tsakanin Makka da Busra ta Sham ne ita ce birnin Hauran.
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji.
Nasa'i ya rawaito shi cikin Alkubra da Ibnu Majah da ma'anarsa haka kuma Ahmad suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah ga dukkan namijin da ya yi kama da mace a cikin tufafin da suka keɓanci mata; daidai ne a cikin kama ne ko launi ko kaifiyya ko hanyar sanyawa da ado ko wanin haka. Ko mace ta yi kama da kayan da suka keɓanci maza kamar haka, kuma shi laifi ne babba daga manyan laifuka.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske, ba sa fitsari ba sa bahaya, ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abin taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski, kuma abin kunna tiraren wutarsu shi ne icen tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inun (Masu tsananin farin ido da tsananin ƙwayar baƙin da ke cikin idon), suna a kan halittar mutum ɗaya, akan surar babansu (Annabi) Adam, zira'i sittin a cikin sama».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin farkon jama'a ta muminai waɗanda zasu shiga aljanna fuskokinsu suna kan surar wata daren goma sha huɗu a haske, sannan masu biye musu suna kan surar tauraro mafi tsananin haske, kuma suna da wasu siffofin cika inda ba sa fitsari ba sa bahaya, kuma ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abubuwan taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski. Kuma abin kunna tiraren wutarsu yana tada ƙanshi mafi daɗin ƙanshin tirare kuma mafi ƙanshin tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inu, halittarsu akan halittar mutum ɗaya ne akan surar babansu Annabi Adam a tsawo da kuma halitta; tsawon jikinsa zira'i sittin ne a sama.
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Akwai darajoji ɗari a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja kamar tsakanin sama da ƙasa ne, Firdausi it ce mafi ƙololuwarsu (a daraja), kuma daga nanne ƙoramun aljanna suke ɓuɓɓugowa, kuma a samanta ne Al’arshi yake. Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi».
Tirmizi ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljannar Lahira akwai darajoji da matsayi ɗari, tsakanin kowace daraja a nisa kamar tsakanin sama da ƙasa ne, kuma mafi ɗaukakar waɗanan aljannatan ita ce aljannar Firdausi, daga nan ne ƙoramun aljanna huɗu suke ɓuɓugowa, a saman Firdausi ne al’Arshi yake; idan zaku roƙi Allah to ku roƙe Shi Firdaus; saboda ita ce a saman dukkaninl aljannatan.
Daga Mugira Ɗan Shu'uba - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Wasu jama'a daga al'ummata ba za su gushe ba suna masu rinjaye, har sai al'marin Allah ya zo musu alhali su suna masu rinjaye».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu mutane ba za su taɓa gushewa ba daga al'ummata suna masu rinjaye akan mutane, masu rinjayar waɗanda suka saɓa musu, hakan har sai al'amarin Allah ya zo musu ta hanyar karɓar rayukansu a ƙarshen zamanin duniya kafin tashin alƙiyama.
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar da musulmi ya ce wa ɗan'uwansa musulmi: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya cancanci kalmar kafircin, idan ya kasance kamar yadda ya faɗa ne, inba haka ba kafirtawar da ya yi wa ɗan'uwansa za ta dawowa wanda ya fada.