





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Imran ɗan Hussain - Allah - Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mafi alherinku zamanina, sannan waɗanda suke biye musu, sannan waɗanda suke biye musu» Imran ya ce: Ban sani ba shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agatre shi - bayan nan ya ambaci ƙarni biyu ne ko uku, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai a bayanku za'a samu wasu mutane zasu dinga ha'iinci ba'a amince musu ba, sunayin shaida ba tare da an nemi shaidarsu ba, suna bakance ba sa cikawa, kuma ƙiba zata bayyana a cikinsu».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi alherin ɗabaƙa ta mutane masu taruwa a zamani ɗaya sune ɗabaƙar sahabban da a cikinsa akwai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa, sannan waɗanda suke biye musu cikin muminan da suka riski sahabbai amma ba su riski Manzon Allah ba, sannan waɗanda suke biye musu sune masu biyewa tabi'ai, sahabin ya yi kaikawo a cikin ambatan waɗanda suke biye musu ga ƙarni na huɗu. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai a bayansu za'a samu wasu mutane zasu dinga ha'inci, mutane ba za su amince da su ba, kuma zasu dinga yin shaida kafin a nemi shaida daga garesu, zasu yi bakance ba sa cikawa, zasu dinga yalwatawa a ciye-ciye da abubuwan sha har sai ƙiba ta bayyana a cikinsu.
Daga Abu Sa'alabata alKhushani Jursumu Ibnu Nashir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su».
Dar Al-Kutni ya ruwaito shi a cikin Sunan din sa da waninsaAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya wajabta wasu abubuwa kuma Ya faralanta wasu farillai, to ku lazimcesu kada ku yi sakaci a cikinsu ta hanyar barinsu ko wulaƙantar da su, kuma Ya sanya muku shamaki da abubuwan da ya tsawatar abubuwan ƙaddarawa waɗanda zasu kareku kuma su tsawatar da ku daga abin da bai yarda da shi ba, dan haka kada ku yi ƙari kan a bin da shari'a ta yi muku umarni da shi, kuma Ya haramta wasu abubuwan da Ya haramta dan haka kada ku aikata su kai karma ku kusancesu, kuma bayan wannan Ya barsu kuma Ya yi shiru game da su dan rahama ga bayinSa, sai suka wanzu akan asalin halaccinsu dan haka kada ku yi bincike game da su.
Daga Abu Muhammad al-Hasan ibnu Ali Ibnu Abi Ɗalib - jikan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma abin shinshinarsa -, ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Kabar abinda kake kokwantansa, zuwa ga abinda baka kokwantansa».
Timizi da Nasa'i ne Suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da barin abin da kake kokwanto akansa na maganganu da ayyuka cewa shin an hana kuwa ko a'a, shin haramun ne ko halal ne, zuwa ga abin da baka kokwanto a cikinsa daga abin da ka tabbatar da kyawunsa da kuma halaccinsa.
Daga Abu Ya'ala Shaddadu ibnu Aws - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai Allah Ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu, idan zaku yi kisa to ku kyautata kisan, kuma idan zaku yi yanka to ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙar tasa, don ya hutar da abin yankansa»
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki Ya wajabta mana kyuatayi a kowane abu, kyuatatawa; ita ce jin tsoron Allah a halin dawwama a bautarsa, da kuma yin alheri da kame cuta ga ababen halitta, yana daga wannan kyautatawar a kisa da yanka. Kyautatawa a kisa a lokacin yin ƙisasi: Shi ne ya zaɓi mafi sauƙin hanyoyi, kuma mafi saurinsu a fitar rai ga wanda za'a kashe. Kyautatawa a yanka: Shi ne ya tausasawa dabba ta hanyar wasa abin da za ayi yankan da shi, kuma kada a wasa a gaban abin da za a yanka ɗin, alhali tana kallon abin da za a yi yankan da shi, kuma kada a yanka alhali akwai wasu dabbobin da suke kallon wadda za a yanka.
Daga Abu Malik al-Haris al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Tsarki rabin imani ne, kuma (faɗin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (faɗin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da ƙasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, haƙuri haskene, Alƙur’ani hujjane gareka ko a kanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto shi ko kuma ya halakar da shi».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Cewa tsarki na zahiri yana kasancewa ne da alwala da wanka, kuma sharadi ne a sallah. Kuma cewa fadin: Alhamdulillah, (wato) "Godiya ta tabbata ga Allah yana cika ma'auni", shi ne godiya gare shi - tsarki ya tabbatar maSa - da kuma siffantaShi da siffofin cika, za'a auna su ranar alkiyama sai su cika ma'aunin ayyuka. Kuma fadin: Subhanallah, "Tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah", Shi ne tsarkake Shi daga kowacce tawaya da kuma siffantaShi da cikakken cika wanda yake dacewa da girmanSa, tare da sonSa da girmamaShi suna cika abinda ke tsakanin sammai da kasa. Kuma: "Sallah haske ce’’ ga bawa a cikin zuciyarsa, da fuskarsa, da cikin kabarinsa, da a tashinsa a taron Alkiyama. Kuma: "Sadaka garkuwace" kuma dalili ce akan gaskiyar imanin mumini, da kuma banbancinsa da munafikin da yake hanuwa daga yin ta (ita sadakar) dan kasancewarsa ba ya yin sadaka a lokacin ta. Kuma: "Hakuri haske ne" - Shi ne tsare rai daga firgici da fushi - wani haskene wanda yake da zafi da kuna, kamar hasken rana; domin shi mai wahalane, kuma yana bukatuwa ga dakewar zuciya da tsareta daga abinda take so; mai shi ba zai gushe ba yana mai haskaka , mai shiriya mai zarcewa akan daidai. Shi ne hakuri akan biyayya ga Allah, da kuma barin sabonSa, da kuma hakuri akan masifu da nau'o'in abubuwan ki a duniya. Kuma: 'Alkur’ani hujjane a gareka" ta hanyar Karanta shi da kuma aiki da shi, ko kuma "Hujjane akanka", ta hanyar barinsa ba tare da wani aiki ba, ko karantawa ba. Sannan - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkanin mutane suna tafiya suna fita suna tashi daga barcinsu suna fita daga gidajensu dan ayyukansu mabanbanta, Daga cikinsu akwai mai tabbata akan biyayya ga Allah, sai ya 'yanto kansa daga wuta, daga cikinsu akwai wanda yake kaucewa daga hakan kuma yake afkawa a cikin sabo sai ya halakar da ita ta hanyar shigarta wuta.
Daga Abu Sa'id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Babu cuta ba cutarwa».
Ibnu Majah da Darakutni da wasunsu Suka ruwaito shi a matsayin MusnadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, ba ya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida. Kuma ba ya halatta gare shi ya rama cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta saidai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Da a ce ana bawa mutane abu saboda iƙirarin cewa nasu ne, da da yawa daga cikin mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanansu, sai dai wanda duk ya yi da'awa to shi zai zo da shaidu, kuma rantsuwa tana kan wanda ya musanta».
Baihaki da wasu suka ruwaito shi kamar haka, kuma sashensa yana cikin Bukhari da MuslimAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa da ace ana bawa mutane saboda kawai mujarradin da'awarsu ba tare da wasu dalilai ba ba kuma tare da wasu alamomi ba to da wasu mutane sun yi da'awar dukiyoyin wasu mutane da jinanensu, sai dai gabatar da shaida da dalili ya wajaba akan mai da'awa da abinda yake nema, idan ba shi da shaidu to sai a gabatar da da'awar akan wanda aka kawo karar, idan ya yi inkarinta to ya wajaba ya yi rantsuwa sai ya kubuta.
Dada Abu Burdah, daga babansa Abu Musa al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi -: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aike shi Yaman, sai ya tambaye shi game da wasu wasu abubun sha waɗanda ake yi su a can, sai ya ce: Waɗanne ne su?, ya ce: «Bit'u da Mirzu». Sai akacewa Abu Burda: Menene Bit'u? Ya ce: Tsimin zuma, Mirzu kuma: Tsimin sha'ir (karamar shinkafa), sai ya ce: «Duk abin da yake sa maye haramun ne» Bukhari ne ya fitar da shi. Kuma Muslim ya fitar da shi da lafazin: Ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikeni ni da Mu'az zuwa Yaman, sai na ce: Ya Manzon Allah! Lallai akwai wani abin shan da ake yi sa a ƙasarmu ana ce masa: Mirzu daga sha'ir ne, (karanar Shinkafa) da kuma wani abin shan da ake ce masa: Bit'u daga zuma ne, sai ya ce: «Duk abin da yake sa maye haramun ne». A cikin wata riwaya ta Muslim: «Sai ya ce: Duka abin da yasa maye ga sallah to shi haramun ne». A cikin wata riwayar tasa kuma: «Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance haƙiƙa an ba shi matattaran kalmomi da cikarsu, sai ya ce: Ya hana duk abin da yake sa maye wanda ya bugar lokacin sallah».
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiAbu Musa al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aike shi Yaman, sai ya tambaye shi game da wasu kayan shaye-shaye waɗanda ake yin su a can, shin su haramun ne, sai ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da su. Sai Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Shi ne Bit'u: Tsimin zuma, da Mirzu: Tsimin shinkafa. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce alhali ya kasance haƙiƙa an ba shi matattaran kalmomi: «Duk abin da yake sa maye haramun ne».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya ziyarci Dakin Allah - Madaukakin sarki - da Hajji kuma bai yi kwarkwasaba, kwarkwasa ita ce jima'i da abubuwan dake da alaka da shi na sumbata da runguma, kuma ana ambatansa da mummunanan zance, kuma bai yi fasikanciba, ta hanayar aikata sabo da munanan ayyuka ba, Daga fasikanci akwai aikata abubuwan da ka haramta in an yi harama, zai dawo daga hajjinsa wanda aka gafartawa, kamar yadda ake haifar yaro kubutacce daga zunubai.