





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari cewa wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da Allah, yana mai gasgatawa da wajabcin azumin da abinda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi tanadi na gwaggwaɓan ladaddaki da sakamako, yana mai nufin zatin Allah - Maɗauakakin sarki - da shi ba don riya ko jiyarwa ba, za'a gafarta masa zunubansa da suka shuɗe.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar dare a daren Lailatul ƙadari yana mai imani da neman lada za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labari game da falalar tsayuwar Lailatul kadari wacce take kasancewa a goman ƙarshe na Ramadan, cewa wanda ya yi ƙoƙarin yin sallah a cikinta da addu'a da karatun al-ƙur'ani da zikiri, yana mai imani da ita, da kuma abin da ya zo a falalarta, yana mai kwaɗayin sakamakon Allah - Maɗaukakin sarki - da aikinsa, ba don riya ko jiyarwa ba, to, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.
Daga Nu'umanu dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : - sai Nu'uman ya sakko da 'yan yatsunsa zuwa kunnuwansa -: "Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake, a tsakaninsu akwai wasu al'amura masu rikitarwa da yawa daga mutane ba sa saninsu, wanda ya kiyaye shubuhohi ya kuɓuta a addininsa da mutuncinsa, wanda ya afka cikin shubuhohi ya afka a cikin haram, kamar mai kiwo ne da yake kiwo a gefen shinge ya kusata ya yi kiwo a cikinsa, ku saurara! lallai kowane sarki yana da shinge, ku saurara! lallai shingen Allah shi ne abubuwan da ya haramta, ku saurara lallai! Lallai a jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru jiki ya gyaru dukkaninsa, idan ta ɓaci jiki ya ɓaci dukkaninsa, ku saurara! ita ce zuciya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana wata ƙa'ida mai gamewa game da abubuwa, cewa sun kasu a shari'a zuwa kashi uku: Bayyanannen halal, da bayyanannen haram, da al'amura masu rikitarwa waɗanda hukuncinsu ba a bayyane yake ba ta bangaren halacci da haramci, da yawa daga mutane basa sanin hukuncinsu. Wanda ya bar waɗannan abubuwan masu rikitarwa gareshi, to, addininsa ya kuɓuta ta hanyar nisanta daga fadawa a cikin haram, kuma mutuncinsa ya kuɓuta daga zancen mutane da abin da za su dinga aibatashi a kansa saboda aikata wannan abin rikitarwar. Wanda bai nisanci shubuhohi ba, to, haƙiƙa ya kai kansa ko dai ga faɗawa a cikin haram, ko aibatawar mutane ga mutuncinsa. Kuma Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don ya bayyana halin wanda yake aikata shubuhohi, kuma cewa shi kamar mai kiwo ne da yake kiwon dabbobinsa kusa da ƙasar da mai ita ya sa mata shinge, dabbobin mai kiwon sun kusa su yi kiwon a cikin wannan shingen don kusancinsu gareshi, to, haka nan wanda yake aikata a bin da a cikinsa akwai shubha, to, shi da wannan ɗin yana kusantowa ga haram, kuma yana kusa da ya afka cikinsa. Bayan wannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa a cikin jiki akwai wata tsoka (ita ce zuciya) jiki yana gyaruwa da gyaruwarta, kuma yana ɓaci da ɓacinta.
Daga Shaddadu ɗan Aws - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Abubuwa guda biyu na haddacesu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu, idan za ku yi kisa, to, ku kyautata kisan, kuma idan za ku yi yanka, to, ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙarsa, ya hutar da abin yankansa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki Ya wajabta mana kyuatayi a kowane abu, kyuatatawa; ita ce jin tsoron Allah a halin dawwama a bautarsa, da kuma yin alheri da kame cuta ga ababen halitta, yana daga wannan kyautatawar a kisa da yanka. Kyautatawa a kisa a lokacin yin ƙisasi: Shi ne ya zaɓi mafi sauƙin hanyoyi, kuma mafi saurinsu a fitar rai ga wanda za'a kashe. Kyautatawa a yanka: Shi ne ya tausasawa dabba ta hanyar wasa abin da za ayi yankan da shi, kuma kada a wasa a gaban abin da za a yanka ɗin, alhali tana kallon abin da za a yi yankan da shi, kuma kada a yanka alhali akwai wasu dabbobin da suke kallon wadda za a yanka.
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa".
Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayyana, baya halatta ga wani ya cutar da kansa ko waninsa daidai wa daida. Kuma ba ya halatta gare shi ya rama cuta da cuta; domin cuta ba a tunkuɗeta da cuta sai dai ta hanyar ƙisasi ba tare da wuce gona da iri ba. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana narko da faruwar cuta ga wanda yake cutar da mutane, da kuma faruwar wahala ga wanda yake tsanantawa mutane.
Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - zuwa ga Annabi: "Duk abunda na hanreku barinsa to ku nisance shi, kuma duk abunda na umarce ku to zo da shi dai dai iyawarku, domin abunda ya halaka magabatanku yawan tambayoyinsu da kuma sabawarsu ga Annabawansu."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiManzon Allah -Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana nuna mana cewa shi idan ya hanamu wani abu ya wajaba akanmu mu nisance shi ba tare da wata togaciya ba, kuma idan ya Umarcemu da wani abu kan mu yi shi to muyi gwargwadon iko sannan ya tsawatar mana don kada mu zamanto irin wasu Al'ummai da suka gabata lokacin da suka yawaita tambayoyi ga Annabawansu kuma suka saba musu sai Allah yayi musu Ukuba da Nau'o'in Hallaka da rusawa to ya dace kada mu kasance irin su don kada mu hallaka kamar yada suka hallaka.
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Jibrilu bai gushe ba yana maimaita masa kuma yana umartarsa da kulawa da maƙoci, wanda shi ne makusancin gida, musulmi ne ko kafiri, ɗan uwa ne ko ba ɗan uwa ba ne, da kiyaye haƙƙinsa da rashin cutar da shi, da kyautatawa gareshi da haƙuri a kan cutarsa, har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi zaton cewa daga girmama haƙƙin makoci da maimaitawar Jibrilu hakan cewa wahayi zai sauka da a ba shi (wani abu )daga dukiyar maƙocinsa wacce zai barta bayan mutuwarsa.
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne".
Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana wasu abubuwa (waɗanda) aikatasu yana daga shirka; daga cikinsu akwai: Na ɗaya: Tawaida: Zancen da 'yan Jahiliyya suke neman waraka da shi wanda ya haɗo shirka. Na biyu: Layu na tsarkiya da makamancinta: Waɗanda ake ratayawa yara da dabbobi da wasunsu dan tunkuɗe kambun baka. Na uku: Tiwala: Wacce akeyi don jawo soyayyar ɗaya daga cikin ma'aurata zuwa ɗayan. Waɗannan al'amuran suna daga shirka; domin suna daga cikin riƙar abu a matsayin sababi, kuma shi ba sababi ne na shari'a ba wanda ya tabbata da dalili, ba kuma sababi ne na zahiri ba da ya tabbata da gwadawa. Amma sabubba na shari'a kamar karanta Al-ƙur'ani, ko na zahiri kamar magunguna da suka tabbata ta hanyar gwadawa, to, su sun halatta tare da ƙudire cewa su sabubba ne, kuma amfani da cuta suna hannun Allah ne.
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haramcin zagin matattu da afkawa a cikin mutuncinsu, kuma wannan yana daga munanan ɗabi'u; domin sun kai zuwa abin da suka gabatar da shi na ayyuka na gari ko na banza, kamar yadda wannan zagin ba ya isa zuwa garesu, to, lallai cewa yana cutar da rayayyu.