





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lokacin da (ayar): {Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne, idan kun bayyanar da abin da ke cikin ranku ko kuka ɓoyeshi Allah zai yi muku hisabi da shi, Yana gafartawa wanda Ya so kuma Yana azabtar da wanda Ya so, Allah Mai iko ne akan dukkan komai}. [al-Baƙara: 284] ta sauka, ya ce: Sai hakan ya tsananta ga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - , sai suka zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sannan suka durƙusa akan gwiwowinsu, sai suka ce: Ya Manzon Allah, an ɗora mana ayyukan da zamu iya, sallah da azimi da jihadi da sadaka, haƙiƙa an saukar maka wannan ayar kuma ba zamu iyata ba, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Shin kuna son ku faɗi kamar yadda mazowa littafi biyu a gabaninku suka faɗa, mun ji mun saɓa?a'a ku ce: Mun ji mun bi, muna neman gafarKa ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa», suka ce: Mun ji kuma mun bi ya Ubangijinmu gafararKa muke nema makoma tana wurinKa, lokacin da mutane suka karantata, sai harsunansu suka horu da ita, a bayanta sai Allah Ya saukar da {Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa haka ma muminai, kowannensu ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da littattafanSa da ManzanninSa bama banbanta wani daga cikin ManzanninSa, suka ce: Mun ji mun bi ya Ubangijinmu gafararKa muke nema makoma tana wurinKa}. [al-Baƙara: 285], lokacin da suka aikata hakan sai Allah Ya shafe ta, sai ya saukar da {Allah ba Ya ɗorawa wata rai sai abin da zata iya, abin da ta aikata nata ne, haka abin da ta aikata na laifi yana kanta, ya Ubangijinmu kada Ka kamamu idan muka yi kuskure ko muka manta} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh» {Ya Ubangijnmu kada Ka ɗora mana wani nauyi kamar yadda ka ɗorawa waɗanda ke gabanmu} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh», {Ya Ubangijinmu kada ka ɗora mana abin da bazamu iya ba} [al-Baƙara: 286], ya ce: «Eh», {Ka yi mana rangwami Ka gafarta mana Kajiƙanmu Ka taimakemu akan mutane kafirai} [al-Baƙara: 286].
Muslim ne ya rawaito shiLokacin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukarwa AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - faɗinSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allah ne} halitta da mulki, da tasarrufi da jujjuya al'aura, {idan kuka bayyanar} kuka bayyanar kuka nuna {abin da ke cikin rayukanku} da ƙirazanku {ko kuka ɓoye shi} sai kuka ɓoyeshi a cikin zukatanku {Allah zai yi muku hisabinsa} a ranar alƙiyama. {Yana yin gafara ga wanda Yake so} da falalarSa da kuma rahamarSa, {Kuma Yana azabtar da wanda Yake so} da adalcinSa, {Allah Mai iko ne akan dukkan komai} wani abu ba ya gajiyar da Shi. Lokacin da sahabbai suka ji ta sai hakan ya yi musu tsanani; domin a cikinta akwai kama mutum har da abin da ke cikin zuciya na tinanika. Sai suka zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai suka durƙusa akan gwiwowinsu, sai suka ce: Ya Manzon Allah, kafin haka an ɗora mana ayyuka na jiki da zamu iya zuwa da shi; misalin sallah da azimi da jihadi da sadaka, sai dai haƙiƙa an saukar maka wannan ayar kuma mu ba zamu iyata ba. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce da su: Shin zaku faɗi irin abin da Yahudawa da Nasara suka faɗa: {Mun ji mun saɓa}? Kawai ku ce: {Mun ji mun bi gafararKa muke nema ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa}, sai sahabbai suka amsawa umarnin Allah da ManzonSa, sai suka ce; Mun ji mun bi gafrarKa muke nema ya Ubangijinmu makoma tana wurinKa. Yayin da musulmai suka faɗeta da harsunansu, kuma rayukansu suka miƙa wuya gareta; sai Allah Ya saukar da tsarkakewa ga Annabi da kuma al'ummarsa da faɗinSa; {Manzo ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa muminai ma haka} harsunansu da zukatansu suka miƙa wuya gareta. {Kowannen su ya yi imani da Allah da mala'ikunSa da litattafanSa, da ManzanninSa, bamu banbancewa tsakanin wani daga cikin ManzanniSa}. Kai muna imani da su baki ɗaya {Suka ce Mun ji } faɗinKa {kuma mun bi} umarninKa, muna neman {gafararKa ya Ubangijinmu} da rangwaminKa, {makoma tana wurinKa} da makoma ranar da hisabi zai tsaya, yayin da suka aikata haka, kuma suka faɗi abin da aka umarce su da faɗinsa na bayyanar da ji da kuma bi ga umarnin Allah; sai Allah Yayi sauƙi ga wannan al'ummar Ya shafe waccar ayar da faɗinSa: {Allah ba Ya ɗorawa wata rai sai abin da zata iya} da ikonta da kuma ƙoƙarinta, {tana da} ladan {abin da ta aikata} na alheri, {kuma a kanta akwai} uƙubar {abin da ta aikata} na zunubi da laifi, kuma Allah ba Ya kama wani da laifin waninSa, haka da abin da zuciyarsa ta yi wasuwasi da shi. {Ya Ubangijinmu kada Ka kamamu} ka yi mana uƙuba {idan muka manta} bamu tuna ba, {Ko muka yi kuskure} sai muka bar daidai bada gangan ba, sai Allah Ya amsa musu hakan sai Ya ce: Haƙiƙa na aikata. {Ya Ubangijinmu kada Ka ɗora mana wani nauyi} da wahala da nauyi {Kamar yadda Ka ɗorawa waɗanda ke gabanmu} daga Banu Isra'il da wasunsu, sai Allah Ya amsa kuma Ya ce: Eh, haƙiƙa na aikata. {Ya Ubangijinmu kada Ka ɗora mana abin da bamu da ikon yin sa} na abubuwan taklifi da bala'i da al'amuran da muke gajiyawa daga ɗaukarsu, Allah Ya ce: Eh haƙiƙa na aikata, {Ka yi mana afuwar} zunubanmu Ka shafe mana su, {Ka gafarta mana} zunubanmu Ka suturta mana su, Ka yafe mana su, {Ka yi mana rahama} da rahamarKa yalwatacciya, {Kaine Majiɓincin al'amuranmu} kuma shugabanmu; {To Ka taimake mu} ta hanyar tsaida hujja da rinjaye {Akan mutane kafirai} a yaƙarsu, sai Allah Ya yi musu, sai Ya ce: Eh, haƙiƙa na aikata.
Daga Umar Ibnul Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum daga cikin Yahudawa ya ce masa: Yakai sarkin muminai, Wata aya a cikin littafinku kuna karantata, da a ce agurinmu mu Yahudawa ta sauka da mun riƙi ranar idi, ya ce: Wacce aya ce? ya ce: {A yau ne na cika muku Addininku kuma na cika muku ni'imata kuma na yardar muku da Musulunci a matsayin Addini} [al-Ma'ida: 3] Umar ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ta sauka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa alhali shi yana tsaye a Arfa a ranar Juma'a.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiWani mutum daga cikin Yahudawa ya zo gurin sarkin muminai Umar - Allah Ya yarda da shi - kuma ya ce masa: Wata aya ce da kuke karantata a cikin littafinku Alƙur'ani, da ace mu jama'ar Yahudawa ne ta sauka a garemu a cikin littafinmu Attaura da mun maida wannar ranar idin da zamu dinga taruwa da shi; dan godiya ga ni'imar saukar wannan ayar mai girma, sai Umar - Allah Ya yardada shi - yace masa: Wace aya ce? Ya ce: {Kuma yaune Na cika muku Addininku, kuma Na cika muku ni'imaTa kuma Na yarje muku musulunci a matsayin Addini} Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Haƙiƙa mun san wannan ranar, da gurin da ayar mai girma ta sauka a cikinsa, haƙiƙa ta saukane ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -a ranar idi, ita ce ranar Juma'a alhali shi yana tsaye a Arfa, kuma su ranaku biyu ne masu girma a wurin musulmai.
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune kafirai} [al-Ma'idah: 44], da {Waɗannan sune azzalimai} [al-Ma'ida: 45] da kuma {Waɗannan sune fasiƙai} [al-Ma'ida: 47]. ya ce: Ibnu Abbas ya ce: Allah Ya saukar da ita ne saboda ƙungiyoyi biyu daga cikin Yahudawa, ɗayarsu ta kasance ta rinjayi ɗayar a lokacin Jahiliyya, har suka yadda suka yi sulhu akan cewa dukkanin wadda aka kashe to wacce ta yi rinjayen (babbar kabilar) ta kashe shi daga cikin ƙasƙantacciya (wacce aka yi nasara a kanta) to diyyarsa ita ce Wusƙi hamsin, kuma dukkanin wadda aka kashe wadda ƙasƙantacciyar ta kashe shi daga mai rinjayen to diyyarsa ita ce Wusƙi ɗari, sun kasance akan haka har Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina, dukkanin ƙungiyoyi biyun suka miƙa wuya ga zuwan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wannan lokacin bai yi rinjaye galaba, kuma bai haɗasu a kansa ba, shi yana cikin sulhu, sai ƙasƙantacciyar ta kashe wani daga cikin mai rinjayan, sai mai rinjayen ta aika zuwa gurin ƙasƙantacciyar: Ku aiko mana da Wusƙi ɗari, sai ƙasƙantacciyar ta ce: Shin wannan ya kasance ne a cikin ƙabilu biyu kawai Addininsu ɗaya, nasabarsu ɗaya, garinsu ɗaya, diyyar sashinsu rabin diyyar sashi ce? Mu ɗin nan mun baku wannan ne kawai dan zalincinku a garemu, da rinjayen da kuka yi mana, amma tunda (Annabi) Muhammad ya zo to baza mu baku hakan ba, sai yaƙi ya kusa ya kunnu a tsakaninsu, sannan suka yarda su sanya Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsakaninsu, sannan wacce ta yi galabar ta ambata sai ta ce: Wallahi (Annabi) Muhammad ba zai baku daga cikinku ninkin abin da suke basu daga garesu ba, kuma haƙiƙa sun yi gaskiya, ba su bamu wannan ba sai dan zalincin da muke yi, da kuma rinjayarsu da muka yi, dan haka ku yi dassi zuwa ga (Annabi) Muhammad wanda zai binciko muku ra'ayinsa: Idan ya baku abin da kuke so to sai ku sanya shi mai hukunci, idan kuma bai baku ba sai ku kiyaye shi, ba zaku sanya shi mai hukunci ba, sai suka yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dassin wasu mutane daga cikin munafukai dan su basu labarin ra'ayin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai Allah Yaba ManzonSa labarin gabaɗayan al'amarinsu da kuma abin da suka yi nufi, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Yakai Manzo kada waɗanda suka yi gaggawa cikin kafirci daga waɗanda suka ce mun yi imani su baƙanta maka rai}[al-Ma'ida: 41] har zuwa faɗinSa: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune fasiƙai}[al-Ma'idah: 47] sannan ya ce: Wallahi ta sauka ne a cikin sha'aninsu, kuma sune Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yake nufi.
Ahmad ne ya rawaito shiA cikin Yahudawan Madina akwai Banu Ƙuraiza da Banun Nadhir, ɗaya ta kasance ta rinjayi ɗayar a lokacin Jahiliyya, sai suka yarda da sulhu akan cewa duk wanda babbar Kabila (wato wacce ta yi nasara) ta kashe cikin kowacce da aka rinjaya to diyyarsa ita ce Wusƙi hamsin kawai, kuma dukkanin wanda aka kashe daga cikin maɗaukakiyar Kabila wanda mai raunin ta kashe shi to diyyarsa ita ce Wusƙi ɗari, shi kuma Wusƙi shi ne Sa'i sittin. sai suka kasance akan haka har Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina yana mai hijira, kuma ƙungiyoyi biyun suka miƙa wuya ga zuwansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali shi - tsira da amincin Allah su tabbbata agare shi - a wannan lokacin bai yi nasara akan maƙiyansa ba, bai rijayesu akan yi masa biyayya ba; domin hakan ya kasance a farkon hijira ne, shi kuwa yana cikin sulhu. Sai ƙasƙantacciyar kabilar (wacce aka yi nasara akanta) ta kashe wani mutum daga cikin maɗaukakiyar (wacce ta yi nasara), sai maɗaukakiyar ta aikawa ƙasƙantacciyar: Cewa ku aiko mana da Wusƙi ɗari kamar yadda muka yi ittifaƙi, sai ƙasƙantacciyar ta ce: Shi wannan ya kasance ne a cikin ƙabilu biyu kawai, Addininsu ɗaya, nasabarsu ɗaya, garinsu ɗaya, diyyar sashinsu rabin diyyar sashi?! lallai mu muna baku wannan ne dan zalintarmu da kuke yi, da kuma tsoronku, amma yayin da (Annabi) Muhammad ya ya zo to ba zamu baku haka ba har abada. Sai yaƙi ya kusa barkewa a tsakaninsu, sannan suka yarda su sanya Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hukunci tsakaninsu, sannan ita babbar kabilar ta lura, sai ta ce: Wallahi Muhammad ba zai baku daga garesu ninkin abin da suke basu daga gareku ba, kuma haƙiƙa sun yi gaskiya, basu bamu wannan ba sai dan mun zalince su, da kuma rijayarsu, to ku aika zuwa ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanda zai zo musu da ra'ayinsa a ɓoye, idan ya baku abin da kuke so sai ku sanya shi mai hukunci, idan kuma bai baku abin da kuke sha'awa ba sai ku barshi bazaku sanya shi mai hukunci tsakaninku ba. Sai suka aika wasu mutane daga cikin munafukai zuwa gurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan su san ra'ayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da suka zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai Allah Ya saukar da wahayi kuma Ya bawa ManzonSa labari da al'amarinsu gabaɗayansa da abin da suka yi nufi, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da Suratul Ma'idah daga faɗinSa: {Yakai wannan Manzo, kar waɗannan da suke gaggawa cikin kafirci su baƙanta maka rai, daga cikin waɗanda sukace: "Mun yi imani"}[al-Ma'idah: 41]. Har zuwa faɗinSa: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune fasiƙai}[al-Ma'idah: 47]. Sannan Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Wallahi faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki - a sha'aninsu ne ya sauka: {Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba to waɗannan sune kafirai}[al-Ma'idah: 44]. Da {...Waɗanan sune azzalimai}[al-Ma'idah: 45] Da kuma {...Waɗanann sune fasiƙai}[al-Ma'idah: 47], kuma sune Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yake nufi.
Daga Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Mabuɗan gaibu biyar ne, {Lalle, Allah a wurinSa kawai sanin yaushe Alkiyama zata tashi yake, kuma Yanã saukar da ruwan sama, kuma Yanã sanin abin da yake a cikin mahaiffannai kuma wani rai bai san abin da yake aikatãwa a gõbe ba, kuma wani rai bai san a wace ƙasã yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne Mai ƙididdidigẽwa}».
Bukhari ne ya rawaito shiGaibu a wajen Allah babu wanda Ya san shi sai Shi, kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mabuɗan gaibu da kuma taskokinsa guda biyar ne: Na farko: Babu wanda ya san yaushe ne alƙiyama zata tsaya sai Allah, nuni ne zuwa ilimummukan lahira, domin ranar alƙiyama ne farkonta, idan sanin mafi kusa ya koru to sanin abin da ke bayansa ma ya koru. Na biyu: Babu wanda ya san yaushe ruwan sama zai zo sai Allah, nuni ne zuwa al'amuran duniyar sama, kuma an keɓanci ruwan sama ne tare da cewa yana da sabubban da suke nunin gudanar al'ada akan afkuwarsa sai dai cewa ba tare da tabbatarwa da kuma yaƙini ba. Na uku; Abin da yake kasancewa a cikin mahaifa; namiji ne ko mace, baƙi ne ko fari, mai cikakken halitta ne ko mai tauyayyar halitta ne, ɗan wuta ne ko ɗan aljanna ne da makamancinsu, kuma an keɓanci mahaifa da ambato dan mafi yawa suna saninta a al'ada, tare da hakan sai ya kore cewa wani ya zama ya san haƙiƙaninsu to waninsu ma shi yafi cancanta. Na huɗu: Babu wanda ya san abin da zai faru gobe sai Allah, nuni ne zuwa nau’ukan zamani da abin da ke cikinsu na abubuwan da zasu faru, kuma an yi amfani da lafazin: "Gobe" dan kasancewar haƙiƙarsa ta zama mafi kusancin zamaninnika, idan ya kasance tare da kusancinsa ba'a sanin abin da zai afku a cikinsa a haƙiƙa, tare da samun alama to abin da ya nisanta shi ne mamafi cancanta. Na biyar: Wata rai bata san a wacce ƙasa zata mutu, nuni ne zuwa wasu al'amuran duniyar ƙasa, tare da cewa al'adar mafi yawancin mutane ita ce ya rasu a garinsa sai dai hakan ba tabbas ba ne, kai da a ce ya rasu a cikin garinsa ba ya sanin a wani guri ne za'a binne shi a cikinsa, ko da ace akwai maƙabartar magabatansa, {Lallai Allah Masani ne Mai bada labari} Mai kewaye sani ne da zahiri da kuma baɗini, da abubuwan da ke ɓoye, da kuma sirrika, sai ayar ta haɗa nau'ikan gaibu, kuma ta gusar da ɓatattun da'awowi.
Daga Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasanace a wurin minbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wani mutum ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai kawai in shayar da mai yin aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa, sai Umar ya yi musu tsawa, kuma ya ce: Kada ku ɗaga muryarku a wajen mimbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ranar Juma'a ce, sai dai idan na sallaci Juma'a zan shiga in tambaye shi a cikin abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta.
Muslim ne ya rawaito shiNu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ambaci cewa shi yana zaune a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wani mutum yana cewa: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in shayar da mai aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa. Sai Umar Ibnul Khaɗɗabi - Allah Ya yarda da shi- ya yi musu tsawa saboda ɗaga muryarsu da suka yi a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma safiyar ranar Juma'a ce, sai dai idan na yi sallar Juma'a zan shiga in tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin, kun mayar da shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai} [al-Tauba: 19].
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ruwaito shi Marfu'i: A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shiAbdullahi ɗan mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambata a cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Duk wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci to zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi}. [al-Hajj: 25], ya ce: Da ace wani daga cikin mutane zuciyarsa zata zantar masa cewa ya yi nufin aikata wani mummunan aiki a cikin Haramin Makka wanda zai halatta abinda Allah Ya haramta masa a cikinsa na haram da harshe ne ko kisa da gangan to cewa hakan zalinci ne, kuma da a ce ƙudirin niyyar a birnin Adan ne a cikin (kasar) Yaman to lallai shi mai cancantar Allah Ya azabtar da shi ne da azaba mai raɗaɗi saboda hakan, koda kuwa bai aikata shi ba, niyyar hakan kawai ta ishe shi .
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lokacin da waɗannan ayoyin suka sauka: {Lallai Mu mun yi maka buɗi buɗi mabayyani dan Allah Ya gafarta maka} har zuwa faɗinSa: {Rabo mai girma} [al-Fath: 1-5] lokacin dawowarsa daga Hudaibiyya, alhali su baƙin ciki da ɓacin rai yana cakuɗe da su, alhali haƙiƙa annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya soke hadayarsa a Hudaibiyya, sai ya ce: "Haƙiƙa an saukar mini da wata aya ita ce mafi soyuwa gareni daga duniya da abinda ke cikinta baki ɗaya".
Muslim ne ya rawaito shiAnas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa lokacin da faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki - ya sauka ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: {Haƙiƙa mu mun yi maka buɗi buɗi mabayyani (1). Dan Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da wanda ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imarSa gareka kuma Ya shiryar da kai hanya madaidaiciya (2). Kuma Ya taimake ka taimako mai girma (3). Shi ne wanda Ya sanya nutsuwa a cikin zukatan muminai dan su ƙara imani tare da imaninsu, rundunonin sammai da ƙasa nasa ce, kuma Allah Ya kasance Masani Mai hikima (4). Dan ya shigar da muminai maza da mata aljannatai ƙoramu suna gudana ta ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu munananan ayyukansu hakan ya kasance rabo mai girma a wurin Allah} [al-Fath: 1-5]. A lokacin dawowarsa daga Hudaibiyya, su kuma sahabbai bakin ciki da bacin rai ya turnuke su, kuma an hana su yin Umarah, saboda abinda sulhun ya faru a kansa da kuma zatansu cewa sulhun ba’a yi shi akan maslahar musulmai ba, hakika kuma sun yanka hadaya a Hudaibiyya, sai (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Haƙiƙa an saukar mini da wata aya wacce ita ce mafi soyuwa gareni daga duniya bakiɗayanta sannan ya karantata.
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya haddace ayoyi goma a zahirin zuciya (hadda) daga farkon Suratul Kahf za'a tsare shi za'a kare shi daga fitinar Masihul Dajjal wanda zai fito a ƙarshen zamani kuma zai yi da'awar Uluhiyya (Allantaka), kuma fitinarsa ita ce mafi girman fitinar da za ta kasance a kan ƙasa tun lokacin da aka halicci (annabi) Adam har zuwa tashin alƙiyama; saboda abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Zai tabbatar masa daga sashin al'amura masu saɓa hankali waɗanda zai fitini wanda ya bi shi, hakan domin cewa farkon Suratul Kahf a cikinta akwai abubuwan mamaki da ayoyi abinda yake yafi girma daga abinda Dujal zai fitini mutane a cikinsa, wanda ya yi tuntuntuni to ba za'a fitina shi da Dujjal ba. A cikin wata riwayar: Ayoyi goma daga ƙarshen surar daga faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Shin waɗanda suka kafirta suna zatan zasu riƙi...}.
Daga Uƙubah Ibnu Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce mini: «An saukar min da wasu ayoyi (waɗanda) ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba ko sau ɗaya, Falaƙi da Nasi».
Muslim ne ya rawaito shiUƙbah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: A daren nan Allah Ya saukar min da wasu ayoyi ba'a taɓa ganin kwatankwacinsu ba - wato a neman tsari (Dafa'i) - sune A'uzai guda biyu: Surar {Ƙul A'uzau bi rabbil falaƙ}, da surar {Ƙul A'uzu bi rabbin Nas}.