Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way






























Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya bukaci al-ummar sa da karatun Alkur’ani. Idan, a Ranar Kiyama, Allah ya sanya - Mai Girma da --aukaka - sakamakon wannan Alkur'ani a matsayin abu mai tsayuwa da kai, ranar tashin kiyama za ta zo don yin c interto ga masu karanta ta da waɗanda suke aiki a cikinta waɗanda suka bi umarnin da kuma hana shi.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta wanda ya karanta Alƙur'ani kuma ya saba da karanta shi - daidai ne yana dubawa daga Mushafi ne ko da ka yake yi - da ma'abocin dabaibayayyun raƙuma da igiyar da ake ɗaure gwiwowin raƙuma da su, idan ya kula sai ya ci gaba da riƙesu, idan kuma ya saki ɗaurinsu sai su tafi su suɓuce, idan ma'abocin Alƙur'ani ya tsaya sai ya karanta shi zai tuna shi, idan kuma bai tsayu da shi ba to zai manta shi; lazimta ba zata gushe tana samammiya ba sai hadda itama ta zama tana nan.
Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya kasance a zaune a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wata ƙara daga sama kamar ƙarar ƙofar da aka buɗe, sai Mala’ika Jibril ya ɗaga kansa da idansa zuwa sama, sannan ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, kuma ba'a taɓa buɗeta ba sai yau ɗin nan, sai wani mala'ika daga cikin mala'iku ya sauko daga gareta zuwa ƙasa, bai taɓa sauka ba kafin nan sai yau, sai mala'ikan ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, kuma ya ce da shi: Ina maka bushara da haske biyu waɗanda aka baka ba'a taɓa bawa wani Annabi kafinka ba; sune: Suratul Fatiha, da kuma ƙarshen ayoyi biyu na Suratul Baƙara. Sannan mala'ikan ya ce: Wani ba zai karanta wani harafi daga garesu ba sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ba shi abinda ke cikinsu na alheri da addu'a da kuma abin da yake nema.
Jundub ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari mun kusa balaga, ƙarfafa masu tsananin ƙarfi, sai muka san imani a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin mu koyi Alƙur'ani, sannan muka koyi Alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa Annabawa dukkaninsu Allah Ya ƙarfafesu kuma Ya basu ayoyi da mu'ujizoji waɗanda suka saɓawa al'adu waɗanda ake kafa hujja da su akan Annabtarsu, kuma suna hukunta imanin wanda ya gansu ya gasgatasu, kuma cewa shi abin rinjaye ne a kansa a cikin kalubalantar inda ba zai iya tunkuɗesu ba akan kansa, sai dai zai iya musantasu kuma ya yi tsaurin kai. Kawai shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayarsa da mu'ujizarsa ita ce Alƙur'anin da Allah Ya yi masa wahayinsa; saboda abin da ya ƙunsa na gajiyarwa mabayyaniya tabbatacciya saboda yawan fa'idarsa da kuma gamewar amfaninsa, dan abin da ya ƙunsa akan Da’awah da hujja da kuma bada labarin abin da zai kasance, sai amfaninsa ya game wanda ya halarta da wanda baya nan da wanda aka samu da wanda za'a samu, sannan ya ce: Ina fatan in zama na fisu yawan mabiya a ranar alƙiyama.
An tambayi Anas ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na Alƙur'ani yake? sai ya ce: Ya kasance yana jan sautinsa da karatu ja; yana jan Lami kafin Ha'i na lafazin jalalah, kuma yana jan Mim wanda ke kafin Nun daga Al-Rahman, kuma yana jan Ha'i daga Al-Rahim.
An tambayi Nana Hafsa uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Yaya Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake karanra Alƙur'ani? Sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya irin nasa ba, sai aka ce mata; Faɗa mana. Nafi'u ya ce sai Ibnu Abi Mulaikah ya karanta karatun da yayi shi a hankali; dan ta hakaito kuma ta kusanto musu da yadda karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ke, sai ya karanta: {Alhamdu lillhi rabbil Aalamin} sannan ya yanyanke karatun, {Arrahmanur rahim}, sannan ya yanyanke karatun, {Maliki yaumid din}.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koyar da sahabbansa Alƙur'ani yana karantar da su shi a dukkanin halayensa muddin dai bai kasance yana da janaba ta hanyar jima'i ba.
Abu Sa'id al-Khudr - Allah Ya yarda da shi - ya fadi cewa wani mutum ya ji wani mutumin daban yana karanta Suratu (Ikhlas): {Ka ce Shi ne Allah Shi kaɗai} yana maimaitata a kowanne dare ba ya ƙari akanta, lokacin da ya wayi gari sai ya zo gurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ambata masa haka, kamar shi mai maganar yana ganin cewa ta yi kaɗan, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwa akan ma'anar ƙarfafawa: Na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai cewa ita (Surar) ta yi daidai da ɗaya bisa uku na Alƙur'ani.