





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Ya kuDaga Abu Tha`ulaah Al-Khashni - Allah ya yarda da shi - ya ce: “Na zo wurin Manzon Allah - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - na ce: Ya Manzon Allah, muna cikin kasar mutanen Ahlul Kitabi, shin za mu ci a lokacinsu? A cikin wurin farauta, zan yi kifi da bakina da karen da ba malami ba, da kuma kare na wanda ake koya wa, to me ya amfane ni? Ya ce: abin da Zkrt- ke nufi da tasoshin mutane Ketab-: idan kun sami wasu ba sa cin su, amma ba za ku iya samun Vagsloha ba, ku ci su, kuma ku tunkuɗe Bqosk, ya bayyana a kan sunan kowane, kuma ya tunkuɗe Bkbak malami, na ambaci sunan Allah a kansa kowane, Ka tuba da karen da bai koyar ba, don haka ka gane hankalinsa, sai ka ci. Mutane kada ku rika burin gamuwa da Abokan gaba ku roki Allah zaman lafiya
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Shi ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiTsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga bakance, shi ne mutum ya wajabtawa kansa wani abu wanda shari'a ba ta wajabta masa ba, kuma ya ce: Lallai bakance ba ya gabatar da komai kuma ba ya jinkirtar da shi, kawai ana fitar da shi ne daga marowacin da ba ya aikata komai sai wajibin da ke kansa kawai, kuma bakance ba ya zuwa da abinda ba'a kaddara masa shi ba.
Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mutane daga Ash'arawa ina neman ya dauki nauyinmu, sai ya ce: "Wallahi ba zan dauki nauyinku ba, bani da abinda zan dauki nauyinku" Sannan muka zauna lokacin da Allah Ya so, sai aka zo da wasu rakuma, sai ya yi mana umarni da rakuma uku, lokacin da muka tafi sai sashinmu suka ce da sashi: Allah ba Zai yi mana albarka ba, mun zowa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muna neman ya dauki nauyinmu sai ya yi rantsuwa cewa ba zai dauki nauyinmu ba sai kuma ya dauki nauyinmu, sai Abu Musa ya ce: sai muka zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai muka ambata masa hakan, sai ya ce: "Ba nine na ɗauki nauyinku ba, a’a Allah ne Ya ɗauki nauyinku, Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAbu Musa Al’Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tare da shi akwai wasu jama'a daga kabilarsa, manufarsu ita ce Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya basu rakuman da zasu hau; dan samun damar fita yaki, sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya yi rantsuwar cewa ba zai dauki nauyin su ba, ba shi da abinda zai dauki nauyinsu da shi, sai suka koma suka zauna tsawon wani lokaci, sannan wasu rakuma uku suka zo wa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, sai ya aika musu, sai sashinsu ya cewa sashi: Allah ba zai yi mana albarka a wadannan rakuma ukun ba; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi rantsuwar cewa ba zai dauki nauyinmu ba, sai suka zo masa suka tambaye shi , sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Wanda ya dauki nauyinku Shi ne Allah - Madaukkain sarki -; domin cewa Shi ne Mai datarwa kuma Mai azirtawa, kadai ni sababi ne wanda hakan ya gudana ta hannuna, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na rantse da Allah, idan Allah Ya so ba na rantsuwa akan wani abu da aikata shi ko na bar shi, kuma in ga wanin wannan abinda na rantse akansa shi ne mafi alheri, sai na aikata abinda yafin kuma in bar wanda na rantse akansa din, kuma in yi kaffarar rantsuwa ta.
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAn tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga saɓanin manufofin masu yin yaƙi; wanda ya yi yaƙi dan jarumtaka ko ƙabilanci ko dan aga matsayinsa a cikin mutane ko wanin hakan, wannene saboda Allah? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya yi yaƙi saboda Allah shi ne: Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya.
Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kun ji kiran sallah, to ku fadi irin abinda ladani yake fada".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwadaitarwa akan amsa wa ladani a lokacin jinsa, hakan da mu fadi irin abinda yake fada, jumla da jumla, A yayin da ya yi kabbara sai mu yi kabbara a bayansa, a yayin da ya zo da shaida biyu, sai mu zo da su a bayansa. An togance lafazin: (Ku yi gaggawa zuwa sallah, ku yi gaggawa zuwa tsira) cewa za'a fada a bayansu: Babu dabara babu karfi sai ga Allah.
Daga Mugira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a daya daga tafiye-tafiyensa sai ya yi alwala, lokacin da ya isa wanke kafafuwa sai Mugira dan Shu'uba - Allah Ya yarda dashi - ya mika hannayensa dan ya cire abinda ke saman kafar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na kuffi dan wanke kafafuwansa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka barsu kada ka cire su, ni na shigar da kafafuwamna a cikin kuffin alhali ni ina da tsarki (Alwala). Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shafa akan kuffinsa, maimakon wanke kafafuwa kenan.
Daga A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Fatima 'yar Abu Hubaishi ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce : Ni ina yin jinin cuta bana tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: "A'a, Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiFadima 'yar Hubaishin ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ni jini ba ya yanke mini, yana zarcewa har a lokacin da ba na al’ada ba, shin hukuncin hakan zai zama hukuncin al’ada sai inbar sallah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Lallai shi jinin cuta ne, shi jinin rashin lafiya ne yana faruwa daga yankewar jijiya a mahaifa, ba jinin haila ba ne, Idan lokacin haila ya zo wanda kika kasance kina haila a cikinsa akan al'adarki ta wata kafin ki yi rashin lafiya da jinin cuta, to ki bar sallah da azimi da wasunsu , na abinda haila take hanawa a lokacin al’ada . Idan gwargwadan lokacin ya kare sai ki zama kin yi tsrki, to sai ki wanke gurin jinin, sannan ki wanke jikinki cikakken wankewa dan dauke hadasi, sannan ki yi sallah.
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar masu yin sallah kan su daidaita sahunsu, kuma kada sashinsu ya gabata akan sashi kada kuma ya jinkirta, kuma daidaita sahu yana daga cikar sallah , kuma karkace sahu ɓaci ne da tawaya a sallah.
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri, idan dayanku ya farka daga baccinsa to ya wanke hannunsa kafin ya shigar da su a ruwan alwalarsa, domin cewa dayanku ba ya sanin a'ina hannunsa ya kasance". Lafazin Muslim: "Idan dayanku ya farka daga baccinsa kada ya nutsa hannunsa a cikin kwarya har sai ya wankesu sau uku, domin cewa shi ba ya sanin a'ina hannunsa ya sakance ".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin huklunce-hukuncen tsarki, daga cikinsu: Na farko: Cewa wanda zai yi alwala to ya wajaba akansa ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da numfashi, sannan ya fitar da shi ta numfashi kuma. Na biyu: Cewa wanda ya yi nufin tsarkake kazanta mai fita daga gareshi da gusar da ita ba tare da ruwa ba kamar duwatsu da makancinsu to tsarkakewarsa ta zama akan adadin mara mafi karancinsa uku, mafi yawa wanda zai kawar da abinda ya fita zai kuma tsarkake wurin. Na uku: Cewa wanda ya farka daga baccin dare kada ya shigar da tafinsa a cikin kwarya dan ya yi alwala har sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, domin cewa shi bai san a'ina hannunsa ya kasance ba, ba zai iya amintar da najasa akan su ba, zai iya yiwuwa Shaidan ya yi wasa da su kuma ya dora abubuwa masu cutarwa garesu ga mutum ko mai bata ruwan.