





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi:- Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya mana jawabin fara magana: Lalle godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsari daga sharrin kawunammu, wanda Allah Ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda ya ɓatar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, ina kuma shaidawa [Annabi] Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne. {Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicceku daga rai guda ɗaya, Ya halitta masa matarsa daga shi, daga su ya yaɗa maza da yawa da mata, Ku ji tsoron Allah Wanda ku ke magiya da Shi, (ku kiyaye) da zumunta, lalle Allah Ya kasance Mai kula da ku ne}. {Ya ku waɗanda ku ka yi imani ku ji tsoron Allah haƙiƙanin jin tsoronSa, kada ku mutu face kuna Musulmai}. {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku faɗi magana ta daidai, zai gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku, duk wanda Ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, to, haƙiƙa ya rabauta, rabauta mai girman gaske.
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDan Mas’ud Allah Ya yarda da shi, yana ba da labarin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya musu huɗubar buƙata, wato wadda ake faɗa lokacin buɗe magana a huɗubobi, da kuma kafin faɗin buƙatar mai jawabi, kamar huɗubar aure da huɗubar Juma’a da sauransu. Wannan huɗubar ta ƙunshi ma’anoni masu girman gaske na bayanin cacncantar Allah ga dukkanin nau’o'in yabo, da neman taimakonSa Shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, da neman yafiyar zunubai da kankarewsu , da neman kariyarSa daga dukkan sharri, da sharrin kai da sauransu. Sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ba da bayanin, ita shiriya tana hannun Allah ne, wanda kuma Ya shiryar da shi, to, babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar, to, babu mai shiryar da shi. Sannan ya ambaci shaidawa da Tauhidi, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da shaidawa da Manzanci da cewa Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) bawanSa ne kuma manzanSa ne. Sai Kuma ya rufe wannan huɗubar da ayoyi guda uku waɗanda suka ƙunshi umarni da jin tsoron Allah maɗaukaki ta hanyar aikata umarninSa da kuma nisantar abin da Ya hana don neman yardar Allah, kuma sakamakon wanda ya aikata haka kyautatuwan ayyuka da maganganu da kankarewar zunubi da gafarta laifuka, da kuma kyakyawar rayuwa a duniya, da rabauta da aljanna ranar Alƙiyama.
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu aure sai da waliyyi".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mace auranta ba ya inganta sai da waliyyin da zai tsaya a ɗaurin auren.
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga (tsawon) tafiyar shekara arba'in".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana narko mai tsanani a kan wanda ya kashe kafirin amana - shi ne kafiri wanda ya shiga garin musulunci bisa alƙawari da amincin - cewa ba zai shaƙi ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta yana kasancewa ne a kan nisan tafiyar shekara arba'in.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsinewa mai karɓar rashawa da mai ba da ita a hukunci.
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mummnar addu'a da korewa da nisantarwa daga rahamar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a kan mai ba da rashawa da mai karɓarta. Daga hakan akwai abin da ake ba wa alƙalai don su yi zalunci a hukuncin da suke jiɓintarsa; don mai bayarwa ya kai ga manufarsa ba tare da wani haƙƙi ba.
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Mun dawo tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Makka zuwa Madina har sai da muka kasance a wani ruwa a hanya, sai wasu mutane suka yi gaggawar (sallar) La'asar, sai suka yi alwala alhali suna gaggawa, sai muka kai gare su alhali karshen kafafuwanusu suna haske (lam’a) ruwa bai tabasu ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tafiya daga Makka zuwa Madina a tare da shi akwai sahabbansa, sai suka samu ruwa a hanyarsu, sai wasu daga sahabbai suka yi gaggawar alwala dan sallar La'asar har karshen kafafuwansu suka dinga bayyana ga mai kallo saboda bushewarsu daga ruwa, sai Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Azaba da halaka a cikin Wuta sun tabbata ga masu takaitawa a wanke karshen kafa a lokacin alwala, kuma ya umarcesu da sukai matuka a cikin cika alwala.
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaida wa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce; Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ya ce; Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa sallah, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa tsira, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah daga zuciyarsa zai shiga aljanna".
Muslim ne ya rawaito shiKiran sallah shi ne sanar da mutane shigowar lokacin sallah, kuma kalmomin kiran sallah kalmomi ne masu tattaro aƙidar imani. A wannan Hadisin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana abin da aka shara'anta a yayin jin kiran sallah, shi ne mai ji ya faɗi irin abin da ladanin yake faɗa, idan ladani ya ce: "Allah ne mafi girma", mai ji ya ce: "Allah ne mafi girma", haka nan; sai dai a lokacin fadin ladani: "Ku yi gaggawa zuwa sallah", "Ku yi gaggawa zuwa tsira" sai mai ji ya ce: "Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah". Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa wanda ya maimaita tare da ladani yana mai tsarkake (niyya) daga zuciyarsa zai shiga aljanna. Ma'anonin kalmar kiran sallah: "Allah ne mafi girma": Wato cewa Shi (Allah) - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi girma mafi ɗaukaka mafi girma daga dukkan komai. "Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. "Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne": Wato ina tabbatarwa kuma ina shaidawa da harshena da zuciyata cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, Allah - Mai girma da ɗaukaka -Ya aiko shi , kuma yana wajaba a yi masa biyayya . "Ku yi gaggawa zuwa sallah", wato ku zo zuwa sallah, da faɗin mai ji: "Babu dabara kuma babu karfi sai ga Allah", wato babu dabara a kuɓuta daga abubuwan da suke hana biyayya, babu ƙarfi a kan aikatasu, kuma babu iko a kan kowanne abu daga abubuwa sai dace daga Allah - Maɗaukakin sarki -. "Ku yi gaggawa zuwa tsira", wato ku zo zuwa sababin tsira, shi ne rabauta da aljanna da tsira daga wuta.
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan: {Ku tsai da sallah domin tunani} [Daha: 14".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayya cewa wanda ya mance yin kowacce sallar farilla har lokacinta ya fita, to, ya wajaba a kansa ya yi gaggawar ramata a duk lokacin da ya tunata, babu gogewa ko suturtawa ga laifin barinta sai dai kawai musulmi ya sallaceta a yayin da ya tunata, Allah Ya faɗa a littafinSa Mai girma: {Ka tsai da sallah domin tunaNi} [Daha: 14], wato: Ka tsai da sallar daka manta idan ka tunata.
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Manzon Allah SAW ya Kasance yana E'itikafi a cikin goman kowane Azumin Ramadan, to yayin da shekarar da aka karbi ransa ta zo yayi E'itikafi kwana Ashirin"
Buhari ne ya rawaito shiAnnabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana laamtara Masallaci yana yanke komai ya koma ga Allah cikin kwana goma na Azumi, kuma yanayi E’itikafi a cikin goman tsakiyarsa; don fatan riskar daren lalatulkadari yayin da aka san cewa tana goman Karshe ne na watan, sannan yayi E’itikafi a Shekarar day a yi wafati a ciki kwana Ashirin don Karin biyayya; don kusantara Allah Madaukakin Sarki
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Cewa an samu wata mace a wasu daga yakokin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi a kashe, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana kashe mata da yara.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wata mace an kashe ta a ɗaya daga cikin yake-yake, sai ya yi inkarin kashe mata da kananan yara waɗanda basu isa mafarki ba.