





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Tamimud Dari -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Lallai wannan al'amarin zai kai inda dare da rana suka kai, kuma Allah ba Zai bar wani gidan bulo ko na gashi ba sai Allah Ya shigar da wannan addinin cikinsa, da girman mai girma ko da ƙasƙancin kaskantacce, buwaya ce da Allah Yake ɗaukaka musulunci da ita, da ƙasƙancin da Allah Yake ƙasƙantar da kafirci da shi" Tamimi al-Dari ya kasance yana cewa: Haƙiƙa na san hakan a iyalan gidana, haƙiƙa wanda ya musulunta a cikinsu alheri da ɗaukaka da buwaya ya same shi, wanda yake kafiri a cikinsu kuma ƙasƙanci da wulaƙanci da jiziya sun same shi .
Ahmad ne ya rawaito shiManzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wannan addinin zai game dukkan sasannin ƙasa, duk gurin da dare da rana suka kai gurin to wannan addinin sai ya kai wurin, Allah ba Zai bar wani gida a cikin birni ko alƙaryu ko a cikin ƙauyuka da sahara ba sai Ya shigar da wannan addini cikinsa. Wanda ya karɓi wannan addinin kuma ya yi imani da shi to zai zama mabuwayi da buwayar musulunci, wanda ya bijire masa kuma ya kafirce masa to zai zama ƙasƙantacce wulaƙantacce. Sannan sahabi Tamimud Dari - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya ga abinda manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata gare shi - ya bada labari da shi a iyalan gidansa musamman, domin wanda ya musulunta daga cikinsu alheri da ɗaukaka da buwaya sun same shi, wanda kuma ya kafirce daga cikinsu ƙasƙanci da wulaƙanci sun same shi tare da abinda zai dinga bayarwa na dukiya ga musulmai.
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ibn Jud'an ya kasance a lokacin jahiliyya yana sada zumunci, yana ciyar da miskinai, shin hakan zai anfanar da shi? Sai Ya ce: "Ba zai anfanar dashi ba, Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da Abdullahi Ibnu Jud'an, ya kasance yana daga shugabannin Kuraishawa kafin Musulunci, Yana daga kyawawan ayyukansa cewa shi: Yana sada zumuncin 'yan uawansa, yana ciyar da miskinai, da wasunsu daga cikin mafifitan ayyukan da Musulunci ya kwadaitar akan aikatasu, da cewa wadannan ayyukan ba za su anfanar da shi a lahirarsa ba; saboda kafircewarsa ga Allah, kuma shi bai taba fada ba ko sau daya: Ya Ubangiji ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako.
Daga Zaidu Dan Khalid AlJuhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina" Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba a Hudaibiyya - ita wata alkaryace kusa da Makka bayan wani ruwa da ya sauka a wannan daren, Lokacin da ya yi sallama ya idar da sallarasa sai ya fuskanto mutane da fuskarsa, sai ya tambayesu: Shin kun san me Ubangijinku - Mai girma da daukaka - Ya ce ? Sai suka amsa masa: Allah da ManzonSane mafi sani. Sai ya ce: Lallai Allah - Madaukakin sarki - Ya bayyana cewa mutane a lokacin saukar ruwa sun kasu gida biyu: Bangare daya sun yi imani da Allah - Madaukakin sarki -, daya bangaren kuma suka kafircewa Allah - Madaukakin sarki -; Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa, ya danganta saukar ruwa ga Allah - Madaukakin sarki -; to wannan ya yi imani da Allah Mahalicci Mai jujjuya al'amura a cikin halittarsa , kuma ya kafircewa taurari. To amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da tauraro iri kaza da kaza; to wannan ya kafircewa Allah kuma ya yi imani da taurari, shi karamin kafarcine ta inda ya danganta saukar ruwa ga taurari; kuma Allah bai sanya shi wani sababi na shari'a ba ko na kaddara, Amma wanda ya danganta saukar ruwa da waninsa daga fararrun abubuwa na kasa ga motsin taurari a bullowarsu da faduwarsu yana mai kudire cewa su ne masu aikin na hakika to shi kafirine kafirci babba.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zo wurisa sai suka tambaye shi: Mu muna ji a cikin zuciyarmu abinda da dayan mu zai fada to da yana da girma, ya ce: "Kuma hakika kun same shi ?" Suka ce: Eh, ya ce: "Wannan shi ne imani baro-baro".
Muslim ne ya rawaito shiWasu jama'a daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zo sai suka tambaye shi game da abinda suke jinsa a cikin zuciyar su na manyan al'amuran da furta su zai girmama akansu saboda muninsu da kuma kyamarsu garesu. Sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Lallai abinda kuke samunsa shi ne imani baro-baro da sakankancewar da zai kaiku ga hana abinda Shaidan yake jefawa acikin zuciya da kuma inkarinku ga furta shi, da girmama hakan acikin zukatan ku, kuma lallai cewa Shaidan ba ya samun dama a cikin zukatanku, sabanin wanda ya samu dama a zuciyarsa kuma bai samu abinda zai tunkude masa hakan ba.
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo gurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai dayanmu yana ji aransa - ana bijiro masa da abu - ya zama toka shi ya fi masa da ya fadi maganar, sai ya ce: "Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya maida makircinsa zuwa wasiwasi".
Abu Dawud da Nasa’i a cikin AlkubraWani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai dayanmu yana jin wani al'amari yana bijiro masa a zuciyarsa, saidai ya fade shi abu ne mai girma ne wanda ya kai matakin ace ya zama toka ya fi soyuwa agare shi akan ya fadeta. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kabbara sau biyu ya godewa Allah da ya mayar da kaidin Shaidan zuwa ga mujarradin wasuwasi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiManzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da maganin abinda ke taso da tambayoyin da Shaidan yake sa wasiwasi akan su ga mumini. Sai Shaidan ya ce: Waye ya halicci abu kaza? waye ya halicci kaza? waye ya halicci sama? kuma waye ya halicci kasa? Sai mumini ya ba shi amsa a Addinance da dabi'ance da hankalce da fadinsa: Allah ne. Saidai Shaidan ba ya tsayawa a wannan iyakar na wasiwasi, kai yana cirata har sai ya ce: Waye ya halicci Ubangijinka? A wannan yayin ne mumini zai ture wadannan wasiwasin da al'amaura uku: Da yin imani da Allah. Da neman tsarin Allah daga Shaidan. Da kuma tsayawa kada ya zarce akan wasuwasin.
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira. Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana girman falalar Allah akan muminai, da kuma adalcinSa ga kafirai. Amma mumini ba za’a tauye ladan kyakkyawan da ya aikata ba; kai za'a ba shi ladan kyakkyawa anan duniya akan biyayyarsa, tare da abinda aka tanadar masa na sakayya a lahira; zai iya rabauta da kykkyawa gaba dayansa a lahira. Amma kafiri sai Allah Ya ba shi sakamakon abinda ya aikata na kyakkyawa da kyakkyawan duniya, har idan ya tafi lahira ba shi da wani ladan da za’a yi masa sakayya da shi a lahira; domin aiki na gari wanda zai yi anfani a duniya da lahira ba makawa mai shi sai ya zama mumini.
Daga Hakim Dan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya ce:: Na ce: Ya Manzon Allah, kana ganin abubuwan da nake ibada da su a lokacin Jahiliyya na sadaka ko 'yantawa, da sada zumunci, shin a akwai lada? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a agre shi - ya ce: "Ka musulunta akan abinda ka gabatar na alheri".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa idan kafiri ya musulunta to shi ana yi masa sakayya akan abinda ya kasance yana aikatawa a cikin Jahiliyya kafin musuluntarsa na ayyuka na gari kamar sadaka ne ko 'yanta bawa ko sada zumunci.
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin munafiki kuma shi kamar akuya ce mai kaikawo, ba ta san wanne garke za ta bi ba na tumakai, Tana tafiya zuwa wannan garken wani lokaci, da kuma zuwa wani garken a wani lokacin daban, Su masu dimuwane tasakanin imani da kafirci, su ba sa tare da muminai a zahiri da badini, kuma su ba sa tare da kafirai a zahiri da badini, su dai zahirinsu suna tare da muminai, kuma badininsu suna cikin kokwanto da taraddudi, wani lokaci yana karkata zuwa ga wadannan, wani lokacin kuma zuwa ga wadannan.