





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sakamakon musulmi a wurin Allah yana daga jinsin abinda musulmi yake aikata shi ne tare da musulmai; wanda ya yaye ya gusar ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki da tsanani daga baƙƙan cikin duniya, Allah Zai yi masa sakayya da cewa Zai Yaye masa wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin ranar alƙiyama. Wanda ya yalwatawa wanda ke ciki matsi ya kuma sawwaƙa masa ya gusar da matsinsa, Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira. Wanda ya suturta wani musulmi kamar idan ya tsinkaya daga gare shi akan abinda bayyanar da shi ba ya kamata na tuntuɓe da kurakurai, Allah Zai suturta shi a duniya da lahira. Allah Yana kasancewa Mai taimako ga bawanSa, muddin dai bawan ya kasance mai tafiya ne akan taimakon ɗan uwansa a maslahohinsa na Addini da duniya, taimako yana kasancewa ne da addu'a da jiki da dukiya da kuma wanin hakan. Wanda ya yi tafiya zuwa tabbatar da wani ilimi na shari'a, yana mai nufin fuskar Allah - Maɗaukakin sarki - da shi; to Allah Zai sawwaƙa masa hanya zuwa aljanna da shi. Wasu mutane ba su taba taruwaba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah (Msallatai), suna karanta littafin Allah kuma suna mudarasarsa a tsakaninsu, sai nutsuwa ta saukar musu, rahamar Allah ta gamesu ta lulluɓesu, kuma mala'iku sun kewayesu, Allah Ya yi yabo a garesu a cikin makusantan dake wajenSa, kuma ambatan Allah ga bawa a cikin jama'a maɗaukaka ya isa ɗaukaka. Wanda aikinsa ya kasance tauyayye ne, ba zai riskar da shi da darajar ma'abota ayyuka ba, to yana kamata kada ya dogara akan matsayin danganta da falalar iyayeba, ya taƙaita a aiki.
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar mutane da yawaita tuba da istigfari, kuma yana bada labari game da kansa cewa shi yana tuba zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - kuma yana neman gafararSa a yini sama da sau ɗari, alhali haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubinsa da abinda ya jinkirta, a cikin hakan akwai cikar kankan da kai da bauta ga Allah - Maɗaukaki -.
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba".
Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mayafin (tufafin) namiji musulmi, shi ne dukkan abinda yake suturta rabin ƙwauri na ƙasa daga maza, halaye uku ne: Na farko: Abinda yake mustahabbi shi ne ya zama zuwa rabin ƙwauri. Na biyu: Wanda ya halatta ba tare da karhanci ba shi ne abinda ke ƙasansa (ƙwauri) zuwa idan sawu; sune ƙasusuwa biyu masu bayyana a mararrabar ƙwauri da diga-digi. Na uku: Wanda aka haramta shi ne ya zama ƙasa da idan sawu, kuma ana jiye masa tsoron kar wuta ta taɓa shi, idan kuma ya zama dan girman kai ne da nishaɗi da shisshigi to Allah ba zai yi duba zuwa gare shi ba.
Daga Ma'ƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ibada a cikin rashin zaman lafiya kamar hijira ce zuwa gareni".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nunar zuwa ibada da yin riƙo da ita a cikin zamanin rashin zaman lafiya da fitina da yaƙe-yaƙe da cakuɗewar al'amuran mutane, kuma cewa ladanta kamar hijira ce zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, hakan domin cewa mutane suna rafkana daga gareta, suna shagaltuwa daga gareta, babu mai ƙoƙari gareta sai ɗaiɗaiku.
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani musulmi da zai yi wata addu'a wacce babu zunubi a cikinta, kuma babu yanke zumunci, face sai Allah Ya ba shi ɗayan abu uku: Kodai Ya gaggauto masa da (amsa) addu’ar sa, ko kuma Ya tanadar masa ita sai ranar alƙiyama, ko kuma Ya kawar masa da wani mummunan abu irinta". Sai (Sahabbai) suka ce: Kenan mu yawaita? Sai ya ce: "Allah Shi ne Mafi yawaitawa".
Ahmad ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa; Musulmi idan ya roƙi Allah ya roke shi wata bukata wacce ba zunubi ba ce kamar ya roƙeShi da sawwaƙa saɓo da zalinci, kuma bai yi addu'a da yanke zumunci ba; kamar ya yi mummunar addu'a akan 'ya'yansa da 'yan uwansa, sai Allah Ya ba shi ɗayan al'amura uku da addu'arsa: Kodai Ya gaggauto masa da addu'arsa Ya ba shi abinda ya roƙa. Ko kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya jinkirtar masa da ita dan lada gare shi a ranar alƙiyama da ɗaukaka daraoji, ko rahama ko gafarta munanan ayyuka. Ko kuma Ya kawar masa a duniyarsa da mummuna kwatankwacinta da gwargwadan addu'ar. Sai sahabban suka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ai sai mu yawaita addu'a; dan mu samu waɗannan falalolin? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai abinda ke gurin Allah shi ya fi yawa kuma ya fi girma daga abinda kuke tambaya, kyautarSa bata ƙarewa, kuma bata tiƙewa.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - Cewa Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin baƙin ciki: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mai girma kuma Mai haƙuri, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin al'arshi mai girma, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai, Ubangijin ƙasa, kuma Ubangijin al'arshi mai girma».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin tsananin baƙin ciki da takaici gareshi: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Mai girman" daraja, mai girman sha'ani, a cikin zatinSa da siffofinSa da ayyukanSa, "Mai haƙuri" wanda ba Ya gaggauto da uƙuba ga mai saɓo kai Yana jinkirtata, kuma Zai iya yi masa afuwa tare da iko akansa, Shi ne Mai iko - tsarki ya tabbatar maSa akan kowane abu. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi Mai girma. "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai da ƙasa" kuma Mahaliccin sammai da ƙasa, kuma Mahaliccin kowane abu a cikinsu kuma Mamallakinsa kuma Mai gyara shi , kuma Mai tasarrufi a cikinsa yanda ya so, "Ubangijin al'arshi mai girma" Mahaliccin al'arshi mai girma.
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai yi hamma to ya riƙe bakainsa da hannunsa, domin cewa Shaiɗan yana shiga".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadakar da wanda zai yi hamma cewa buɗe bakinsa saboda kasala ce ko cika ko wanin haka; cewa ya ɗora hannunsa akan bakinsa sai ya rufeshi da shi; hakan domin Shaiɗan yana shiga cikinsa idan ya barshi a buɗe, to ɗora hannu yana zama mai hana shigarsa.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi ya yi duba a cikin al'amuran duniya a matsayi da dukiya da kuma alfarma da wasunsu zuwa ga wanda yake ƙasa da shi a hali, kuma kada ya yi duba a cikin al'amuran duniyarsa zuwa ga na sama da shi wanda ya fi shi, domin wannan duban zuwa ga na ƙasa shi ne mafi cancantar da zai sa ba zaka wulaƙanta ni'imar Allah gareka ba.
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga sakin tufafi ko gwabso ƙasan idan sawu dan jiji da kai da kuma girman kai, kuma cewa wanda ya aikata hakan ya kasance ya cancanci narko mai tsanani cewa Allah ba Zai yi duba zuwa gareshi ba duba na rahama a ranar alƙiyama.