





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ni'imomi biyu ana yi wa da yawa daga mutane kamunga a cikinsu: Lafiya da rarar lokaci".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ni'imomi biyu masu girma daga ni'imomin Allah ga mutum wanda da yawa daga mutane suke hasara a cikinsu inda suke juyar da su ba'a mahallinsu ba; domin mutum idan ni'imar lafiya tare da rarar lokaci suka taru gare shi , sai kasala ta rinjaye shi daga ɗa'a to shi yana daga masu hasara; wannan shi ne halin mafi yawancin mutane, idan ya yi anfani da rarar lokaci da kuma lafiyarsa a cikin ɗa'ar Allah to shi mai rabauta ne; inda kuma duniya ita ce gonar lahira, kuma a cikinta akwai kasuwancin da ribarsa take bayyana a lahira, rarar lokaci kuma shagalta tana biye masa, lafiya kuwa rashin lafiya yana biye mata, koda baikasance ba sai tsufa da to ya isa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana addu'a a cikin sujjadarsa sai ya ce: (Ya Allah Ka gafarta mini zunubina) da suturta shi, kuma Ka kareni nauyinsu; sai Ka yi rangwami Ka ƙetare ka kauda kai, (dukkansa), ka taimake ni: (ƙanƙaninsa) ƙaraminsa da ƙanƙaninsa, (da babbansa) babbansa da mai yawansa, (da na farkonsa) farkon zunubi, (da na ƙarshensa), da abinda ke tsakaninsu, (na zahirinsa da na baɗininsa) daga abinda babu wani wanda ya sanshi sai Kai - tsarki ya tabbatar maKa -.
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake yawaita tsinuwa akan wanda bai cancanteta ba to shi ya cancanci uƙuba biyu: Ta farko: Ba zai zama mai shaida ba a ranar alƙiyama akan al'ummu na isarwar Manzanninsu ga saƙonni zuwa garesu, kuma ba za'a karɓi shaidarsa ba a duniya; dan fasiƙancinsa, kuma ba za'a azurta shi da shahada ba ita ce mutuwa a tafarkin Allah. Ta biyu: Ba zai yi ceto ba a ranar alƙiyama lokacin da muminai suke yin ceto ga 'yan uwansu waɗanda suka cancanci (shiga) wuta.
Daga Salman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lalle Ubangijinku Mai kunya ne kuma Mai karamci ne, Yana jin kunyar bawanSa idan ya ɗaga hannayensa zuwa gare Shi Ya dawo da su babu komai".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitarwa akan ɗaga hannaye a lokacin addu'a, kuma ya bada labarin cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa (Mai kunya ne) Mai yawan kunya ne, ba Ya barin kyauta, Yana yi wa bawa abinda yake faranta masa, kuma Yana barin abinda yake cutar da shi, (Mai yawan kyauta ne) Yana bayarwa ba tare da tambaya ba to yaya kuma bayan tambaya! Yana jin kunyar bawanSa mumini ya dawo da hannayensa bayan ɗagasu dan yin addu'a babu komai suna babu komai cikinsu a taɓe daga amsawa.
Daga Nana Juwairiyya Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fita daga wurinta da sassafe yayin da ya yi sallar Asuba, alhali tana wurin sallarta, sannan ya dawo bayan hantsi ya daga, alhali tana nan a zaune, sai ya ce: «Ba ki gusheba a kan halin da na barki a kansa?» Ta ce: Eh, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da za'a auna su da abin da kika faɗa a yau da sun rinjaye su: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyar Sa, adadin halittar Sa, da yardar kanSa, da nauyin Al’Arshin Sa, da tawadar kalmomin Sa).
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita daga wurin matarsa Uwar muminai Nana Juwairiyya - Allah Ya yarda da ita - a farkon yini lokacin da ya yi sallar Asuba, alhali ita tana zaune a wurin sallarta, sannan ya dawo bayan rana ta ɗaga lokacin sallar walaha, alhali ita ba ta gushe ba tana zaune a wurinta, sai ya ce: Shin baki gushe ba akan halin da na barki akansa? Ta ce: Eh, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Haƙiƙa a bayanki na faɗi wasu kalmomi huɗu, kuma na maimaita su sau uku, da za'a auna da abinda kika faɗa a gaba ɗayan lokacin da kike a zaune a cikinsa da sun rinjaye su: (Tsarki ya tabbata ga Allah) da tsarkakarSa daga dukkan tawaya, (da godiyarSa) inda Yake da kyakkyawan yabon da Ya shiryar ga hakan, (adadin halittarSa) waɗanda babu mai iya iyakancesu sai Allah, (da yardar kanSa) da gwargwadan abinda Ya yardar maSa ga wanda Allah Ya yarda da shi daga bayinSa kuma shi wani abu ne ba’a kewaye shi da sani , (da awon Al’arshin sa) wanda shi ne mafi girman halittu kuma mafi nauyinsu, (da tawadar kalmominSa) kuma kalmomin Allah ba sa taƙaituwa kuma ba sa ƙarewa; wannan yana gemawa kuma yana ƙunsar rabe-raben uku; domin tawadar kalmominSa - tsarki ya tabbatar maSa - babu karewa ga iyakarta, ko ga siffarSa ko ga adaddinsa, sai dai abin nufi: Kai matuka da shi a yawa; domin a farko ya ambaci abinda kirge mai yawa na adadin halitta yake iyakance shi , sannan ya hau zuwa abinda shi ne mafi girma daga nan kuma ya bayyanar daga gare shi da yardar kanSa, sannan awon mafi girman halittu shi ne al'Arshi; na farkon dan kirgawa ne da kuma yawa, na biyun kuma da siffa ne da kuma kaifiyya, na uku dan girma da kuma nauyi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi a cikin AlkubraAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga rafkana daga ambatan Allah, kuma cewa wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba kuma basu ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa ba, kuma ba su yi salati ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sai wannan mazaunin ya zama hasara a kansu da nadama da taɓewa da tawaya a ranar alƙiyama, idan Ya so Ya azabtar da su saboda zunubinsu da ya gabata da kuma kasawarsu mai zuwa, idan kuma Ya so Ya gafarta musu dan falala da rahama daga gare shi.
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai wanda ya fiku soyuwa a gare ni kuma mafi kusancinku mazauni a ranar AlKiyama (su ne) mafi kyawunku halayya, kuma mafi ƙinku a gare ni, kuma mafi nisantarku dani a mazauni a ranar AlKiyama masu yawan surutu da masu tsanantawa, da masu jiji da kai», suka ce ya Manzon Allah, haƙiƙa mun san masu yawan surutu da masu tsanantawa to su waye masu jiji da kai ya ce: «Masu girman kai».
Tirmizi ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya bayyana cewa yana daga mafi soyuwarku gare shi a duniya, kuma mafi kusancinku mazauni da shi a ranar Alkiyama (su ne) mafi kyawunku a ɗabi'u, kuma cikin mafi ƙiyayyarku gare shi a duniya, kuma mafi nisantarku mazauni daga gare shi a ranar Alkiyama masu munanan ɗabi'u a cikinku; (masu yawan surutu) sune masu yawaita magana dan ɗorawa kai da kuma fita daga gaskiya, (masu tsanantawa kuwa) sune masu yalwatawa a cikin zance dan ɗorawa kai fasaha da girmama maganarsu ba tare da kiyayewa ba, (da masu girman kai). suka ce: Ya Manzon Allah, haƙiƙa mun san masu yawan surutu da masu tsanatwa, to su waye masu jiji da kai? Ya ce: masu girman kai masu yi wa mutane izgili wadanda suke yawaita magana kuma suke bude bakunansu da shi.
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Haƙiƙa wanda ya miƙa wuya (ga Ubangijinsa), kuma aka azurta shi da abu kaɗan (gwargwadan buƙatarsa), kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya ba shi to ya rabauta».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa haƙiƙa ya rabauta wanda ya miƙa wuya ga Ubangijinsa sai aka shiryar da shi kuma aka datar da shi ga Musulunci, kuma aka azirta shi gwagwadan buƙatarsa daga halal ba tare da ƙari ko ragi ba, kuma Allah Ya sanya shi mai yarda da abinda Ya bashi.
Daga Ubaidullahi ɗan Mihsan al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».
Tirmizi ne ya Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa yaku musulmai duk wanda ya wayi gari a cikinku yana mai lafiyayye kuɓutacce a cikin jikinsa daga illoli da cututtuka, kuma yana amintacce a cikin ransa da iyalansa da hanyarsa ba ya tsoro, kuma yana da isasshen abin cin yininsa na halal; to kamar an tattara masa duniya ne gabaɗayanta.