





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son Addu'ar da ta tattaro komai, kuma yana ƙyale wacce ba ita ba.
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son addu'o'i masu tattaro alherin duniya da lahira wacce lafazinta kaɗan ne kuma ma'anarta yana da yawa, kuma a cikinta akwai yabo ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da manufofi na gari, kuma yana barin koma bayan haka.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi akan rantsuwa da kuma yawaita ta koda ta kasance akan gaskiya ne a siye da siyarwarsa, kuma ya bada labarin cewa ita sababi ce ta yawaitar haja da kaya da kuma samun ribarsu, sai dai hakan tawaya ce kuma ɓata albarkar riba ce da kuma kasuwanci, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai iya dora wasu abubuwa da zasu ɓata su kodai ta hanyar sata ko gobara ko dilmiya a ruwa ko ƙwace ko fizge ko wasu abubuwa masu bijirowa daban waɗanda dukiyarsa zata lalace saboda su.
Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku zagi Iska, idan kuka ga abinda ba kwa so to kuce: Ya Allah mu muna roƙonKa daga alherin wannan iskar, da alherin abinda ke cikinta, da alherin abinda aka umarce ta da shi, kuma muna neman tsarinKa daga sharrin wannan iskar, da kuma sharrin abinda ke cikinta, da kuma sharrin abinda aka umarce ta da shi".
Tirmizi ne ya ruwaito shi(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani da a zagi ko tsinewa iska, domin ita abar umarta ce daga Mahaliccinta, tana zuwa da rahama da kuma azaba, aibanta ta aibanta Allah ne Mahaliccinta, da fushi akan hukuncinSa, sannan tsira da amincn Allah su tabbata agare shi ya shiryar zuwa komawa ga Allah Mahaliccinta da roƙonSa daga alherinta da alherin abinda ke cikinta da alherin abinda aka aikota da shi, kamar zuwanta da ruwa da ɗaukar abinci (wata madatta ce da take ƙarfafa jikin mutum ko dabba) da makancinsa, da kuma neman tsarin Allah daga sharrinta da sharrin abinda ke cikinta da kuma sharrin abinda aka aikota da shi, kamar bata tsirrai da bishiyoyi da kashe dabbobi da rusa gine-gine da makamancinsa, kuma a cikn rokon Allah akwai tabbatar da ubudiyya ga Allah.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ɗayanku ya ce: Ya Allah Ka gafarta mini in Ka so, Ka yi mini rahama in Ka so, Ka azirtani in Ka so, ya ƙudirce niyyar rokonsa, lallai Shi Yana aikata abinda Yake so, babu mai tilasta Shi". Kuma riwayar Muslim: "Sai dai ya ƙudirce niyyar tambaya kuma ya girmama kwaɗayi, domin Allah wani abu da Ya bada shi ba ya yi maSa girma".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga rataya addu'a da wani abu koda ya kasance da Mashi'ar Allah ne (ganin damar Allah) domin hakan wani al'amari ne abin sani abin sakankancewa cewa shi ba'a gafartawa sai idan tsarki ya tabbatar maSa Ya so, kuma babu wata ma'ana ga sharɗanta Mashi'a; domin cewa ita kaɗai ana sharɗantata ne ga wanda ya inganta daga gare shi ya yi aiki ba tare da ya so ba da tilastawa da waninsa daga abinda Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya tsarkaka daga gare shi, haƙiƙa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana a cikin ƙarshen hadisin da faɗinSa lallai shi Allah babu mai tilasta shi, kamar yadda cewa Allah babu wani abu daya da ya bada shi yake girmama a gareShi, kuma Shi ba mai gajiyawa bane kuma wani abu ba ya girmama a gareShi har ace: Idan Ka so, kuma rataya shi da Mashi'a wani nau'i ne na wadatuwa daga gafararSa, to faɗin mai faɗa: Idan Ka so Ka bani kaza to Ka aikata, ba'ayin amfani da wannan sai tare da wanda ya wadata daga gare shi, ko tare da wanda ya gajiya, amma tare da mai iko kuma tare da mai buƙatuwa gare shi to cewa shi ya ƙudirce niyyar roƙonsa, kuma ya yi roƙo irin roƙon mabuƙaci mai tsananin buƙatuwa zuwa ga abinda ya roƙe shi, kuma ya fake zuwa ga Allah; domin cewa Shi Mawadaci ne cikakke, Mai iko a kan dukkan komai.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe hancin mutumin da Ramadan ya shiga sannan ya fita ba’a gafarta masa ba, kuma an turbuɗe hancin mutumin da mahaifansa suka tsufa a wurinsa amma basu shigar da shi aljanna ba".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiMummunar addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan nau'i uku da turbuɗe hancinansu da turɓaya daga ƙasƙanci da wulaƙanci da kuma taɓewa. Nau'i na farko: Wanda aka ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurinsa bai yi masa salati ba da faɗinsa: tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ko makamancinsa. Na biyu: Wanda ya riski watan Ramadan sannan watan ya ƙare ba’a gafarta masa ba saboda gazawarsa a aikata aikin ɗa'a. Na uku: Mutumin da tsufa ya riski iyayensa a wurinsa amma ba su zama sababi a cikin shigarsa aljanna ba dan saɓawarsa da kuma gazawarsa a kan haƙƙinsu.
Daga Bara'u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari: Cewa babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu a wata hanya da makamancinta ɗayansu ya yi wa ɗayan sallama, gaisuwa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu da jikkuna ko da gama gaisuwar.
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Lallai cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu (suna) tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangiji) al-Rahman, kamar zuciya ɗaya, yana jujjuyata yadda Ya so" sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ya Allah Ya mai jujjuya zukata Ka juya zukatanmu a kan biyayyarKa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangijin) shi ne al-Rahman kamar zuciya ɗaya; Yana juya ta yadda Ya so; idan Ya so Ya tsayar da ita akan gaskiya, idan kuma Ya ga dama ya karkatar da ita daga gaskiya, kuma jujjuyawarSa a cikin dukkannin zukata kamar tasarrufi ne a abu ɗaya, wani sha'ani ba ya shagaltar da Shi - tsarki ya tabbatar maSa - daga wani sha'anin, sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi adu'a sai ya ce: Ya Allah ya Mai jujjuya zukata wani lokaci zuwa ga ɗa'a, wani lokaci kuma zuwa saɓo, wani lokaci kuma zuwa tinawa wani lokaci kuma zuwa rafkana, ka juyar da zukatanmu akan biyayyarKa.
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ni'ima da farin ciki da kyau a duniya, kuma Allah Ya isar da shi zuwa ni'imar aljanna da ni'imarta a lahira; ga wanda ya ji zancensa sai ya haddace shi har ya isar da shi ga waninsa, sauda yawa wanda aka isarwa hadisin ya zama ya fi kiyayewa kuma ya fi fahimta kuma ya fi ikon yin istinbaɗi daga wanda ya ruwaito hadisin, sai na farkon ya zama yana kyautata hadda da dakkowa, na biyun kuma ya zama yana kyautata fahimta da istinbaɗi (tsamo hukunci).
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai mumini yana da wata shema a cikin aljanna ta lu'ulu'u ɗaya mai ƙofa a cikinta, tsawonta mil sittin ne, mumini yana da mata a cikinta, mumini zai kewayesu amma sashinsu ba zai ga sashi ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da sashin ni'imar aljanna, kuma lallai cewa mumini a cikin aljanna yana da wata shema mai girma mai yalwar ciki, ta gwal ɗaya wacce a cikinta akwai ƙofa, faɗinta da tsawonta a cikin sama mil sittin ne, a cikin kowane ɓangare da nahiya da kusurwarta daga cikin kusurwoyin ta huɗu akwai mata, sashinsu ba ya ganin sashi, mumini zai kewayesu.