





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari, abinda wani ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani ɗan Adam ba» Abu Huraira ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki da shi} [al-Sajdah: 17].
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ce: Na tanadarwa bayiNa na gari dan girmamawa a cikin aljanna abinda wani ido bai taɓa ganin zatinsa ba, kuma wani kunne bai taɓa jin siffarsa ba, kuma haƙiƙaninsa bai taɓa afkuwa ko wucewa akan zuciyar wani ɗan Adam ba. Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Idan kun so ku karanta: {Wata rai ba ta sanin abinda aka ɓoye musu na abinda rai yake farin ciki (da shi)} [al-Sajda: 17].
Daga Abu Abdullahi al-Jadali ya ce: Na tambayi A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - game da ɗabi'un Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Bai kasance mai yawan alfasha ba, ko mai yawan ɗorawa kansa alfasha ba, ko mai kwararoto a kasuwa, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana yin afuwa kuma yana kau da kai.
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiAn tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Alfasha da munanan maganganu ko ayyuka ba su zama daga ɗabi'unsa ba, kuma ba ya ɗorawa kansa alfasha, kuma ba ya yi da gangan, kuma ba ya ihu yana ɗaga muryarsa a cikin kasuwanni, kuma ba ya rama mummuna da mummuna, sai dai yana sakayya da kyakkyawa, kuma yana yin afuwa a baɗini, kuma yana kau da kai yana kawar dakai a zahiri.
Daga Hani baran Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Usman ya kasance idan ya tsaya akan ƙabari sai ya yi kuka har sai gemunsa ya yi dan shi, sai aka ce masa: Ana ambatan aljanna da wuta amma baka kuka, kuma kana yin kuka saboda wannan? sai ya ce: Lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan Lahira, idan mutum ya tsira a cikinsa to abinda ke bayansa ya fishi sauƙi, idan kuma bai tsira a cikinsa ba to abinda ke bayansa ya fi shi tsanani».
Tirmizi ne ya Rawaito shiSarkin muminai Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya kasance idan ya tsaya akan wani ƙabari sai ya yi kuka har sai hawaye ya sa gemunsa ya yi dan shi, sai akace masa: Ana ambatan aljanna da wuta amma baka kuka dan shauƙi zuwa aljanna ko tsoron wuta! amma kana kuka saboda ƙabari? Sai ya ce: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan lahira, idan ya tsira ya kuɓuta daga cikinsa to abinda ke bayansa na masaukai su ne mafi sauƙi daga gare shi , idan bai tsira daga azabarsa ba; to abinda ke bayansa na uƙuba ya fi tsanani daga abinda ke cikinsa.
Daga Bahzu ɗan Hakim daga babansa daga kakansa ya ce: Na ce ya Manzon Allah: Waye wanda zan fi yi wa biyayya? Ya ce: «Mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan mahaifiyarka, sannan babanka, sannan mafi kusa sai mafi kusa».
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mafi cancantar mutane da yi wa biyayya, da kyautata masa, da kyakkyawar mu'amala, da tsaftatacciyar mu'amala, da abokantakarsa da sadar da zumuncinsa: Ita ce uwa, kuma ya ƙarfafa haƙƙin uwa akan waninta da maimaitawarsa sau uku; dan bayanin falalarta akan ragowar mutane ba tare da togancewa ba. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai bayyana wanda yake biye mata a biyayya: Sannan uba, sannan mafi kusanci sai mafi kusanci daga 'yan dangi, kuma a duk lokacin da ya zama ya fi kusanci to ya zama mafi cancanta da sadar da zumunci daga mafi nesa.
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi».
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji) kuma abin bautawa da gaskiya mai reno kuma mamallaki shugaba kuma mai gyarawa. (Da Musulunci) da dukkanin hukunce-hukuncensa na umarni da hani (Addini) kuma tafarki da shari'a da miƙa wuya. (Da Annabi Muhammad a matsayin manzo) da Annabi; da dukkanin abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi garemu, sai aljanna ta wajaba gare shi.
Daga Ubada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - , kuma ya kasance ya halarci Badr, shi yana daga cikin jagorori a daren Aƙabah: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce alhali a gefensa akwai wasu jama'a daga sahabbansa: «Ku yi mini caffa akan kada ku taranya wani da Allah (a bauta), kada ku yi sata, kada ku yi zina, kada ku kashe 'ya'yanku, kada kuzo da ƙirƙiren ƙaryar da zaku aikata ta tsakanin hannayenku da ƙafafuwanku, kuma kada ku saɓa a wani aikin alheri, to wanda ya aikata a cikinku to ladansa yana wurin Allah, wanda ya aikata wani abu daga hakan (saɓo) sai aka yi masa uƙuba a duniya to shi kaffarane a gare shi, wanda kuma ya aikata wani abu daga hakan (saɓo) sannan Allah Ya suturta shi to shi yana ga Allah, idan Ya so zai yi masa rangwami idan kuma Ya so Ya yi masa uƙuba» sai muka yi masa caffa (mubaya’a) akan hakan.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiUbada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, kuma ya kasance yana daga waɗanda suka halarci yaƙin Badr babba, kuma shi ne jagoran mutanensa waɗanda suka gabato dan yin caffa don taimakon Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a daren Aƙaba wacce ke Mina - a lokacin da Manzo ya kasance a Makka kafin Hijirarsa zuwa Madina - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana zaune tsakanin sahabbansa sai ya nemi su yi masa alƙawari akan wasu al'amura: Na farko: Kada su taranya wani abu da Allah a bautar Allah ko da ya ƙaranta. Na biyu: Kada su yi sata. Na uku: Kada su aikata zina. Na huɗu: Kada su kashe 'ya'yansu; mazansu dan jin tsoron talauci ko matansu dan jin tsoron aibi. Na biyar: Kada su yi ƙaryar da zasu ƙirƙireta tsakanin hannayensu da ƙafafuwansu inda mafi yawancin ayyuka suna afkuwa ne ta su koda ragowar gaɓɓai sun yi tarayya da su (a ciki). Na shida: Ba za su saɓawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba a cikin wani aikin alheri. Wanda ya tabbata a cikinsu akan alƙawarin kuma ya lazimci hakan to ladansa yana ga Allah, wanda kuma ya aikata wani abu daga abinda aka ambata - banda shirka - sai aka yi masa uƙuba saboda shi a duniya ta hanyar tsaida haddi a kansa to shi kaffara ne gare shi kuma da shi ne zunubi ya saraya, kuma wanda ya aikata wani abu sannan Allah Ya suturta shi to al'amarinsa yana ga Allah; idan Ya so zai yi masa afuwa idan kuma Ya so zai yi masa uƙuba, sai duk waɗanda ke gurin suka yi masa caffa (mubaya’a) akan hakan.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Musulunci ya fara yana baƙo, kuma zai dawo baƙo, aljanna ta tabbata ga baƙi».
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Musulunci ya fara yana baƙo a cikin ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙarancin ma'abotansa, kuma zai dawo yana baƙo saboda ƙarancin wanda zai tsayu da shi, to farin ciki, kuma madalla ga baƙi, da farin ciki da sanyin ido gare su.
Daga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Na haneku da ƙananan zunibai, kaɗai misalin ƙananan zunubai kamar mutane ne da suka sauka a cikin wani kwari, sai wannan ya zo da ice, wannan ma ya zo da ice, har suka sa gurasarsu ta nuna, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu saboda su zasu halaka shi».
Ahmad ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga sakaci a aikata ƙananan zunubai, da kuma yawaitasu domin cewa su idan sun taru zasu halakar, kuma ya buga misali akan hakan da wasu mutanen da suka sauka a cikin wani kwari, sai kowanne daga cikinsu ya zo da ita ce ƙarami, har sai da suka sa gurasarsu ta nuna saboda taruwar abinda suka tara na itatuwan, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu da su bai tuba daga garesu ba ko kuma Allah bai yi masa afuwa ba to zasu halaka shi.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kaɗai an aikoni ne dan in cika manyan ɗabi'u».
Bukhari a cikin Al-Adab Al-Mufrad da Ahmad da Baihaki suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agate shi - ya bada labarin cewa kaɗai shi Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya aikoshi ne dan ya cika kyawawan ɗabi'u; inda aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan cika abinda ya gabace shi na manzanni, kuma mai cika kyawawan ɗabi'un larabawa, sun kasance suna son alheri kuma suna ƙin sharri, masu mutunci ne da karamci da gabata; sai aka aiko Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dan cike abubuwan da suka gaza da ke cikin ɗabi'unsu, kamar alfaharinsu da nasabobi, da girman kai, da wulaƙanta talaka da wanin hakan.