





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Ɗan Adam ya cutar da Ni yana zagin zamani alhali Nine zamani, al'amari yana hannunNa iNa jujjuya dare da rana».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi: Mutumin da yake zagin zamani a lokacin saukar masifu da abubuwan ƙi yana cuta ta kuma yana tauyeNi; domin cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne Mai jujjuya al'amura Shi kaɗai, kuma Mai sarrafa abinda yake faruwa; to aibata zamani aibata Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, zamani kuwa kawai shi halitta ne abin horewa, abubuwa suna gudana ne a cikinsa da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Daga Abu Ruƙayya Tamim ibnu Aws al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa Addini a tsaye yake a kan ikhlasi da gaskiya, har sai an yi shi kamar yadda Allah Ya wajabta, cikakke ba tare da tawaya ko algus ba. Sai aka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ga wa nasihar za ta kasance? sai ya ce: Na farko: Nasiha ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -: ta hanyar tsarkake aiki gare shi, da rashin haɗa Shi da wani, kuma mu yi imani da RububiyyarSa da UluhiyyarSa da sunayenSa da siffofinSa, da girmama umarninSa, da kira zuwa ga imani da Shi. Na biyu: Nasiha ga littafinSa shi ne AlKur'ani mai girma: Shi ne mu ƙudirce cewa shi zancenSa ne, kuma ƙarshen littattafanSa, kuma shi mai shafewa ne ga dukkanin shari'o'in da suke kafinsa, kuma mu girmama shi, mu karanta shi haƙiƙanin karanta shi, mu yi aiki da muhkam ɗinsa, kuma mu miƙa wuya ga masu kamanceceniya daga gare shi, kuma mu kore tawilin masu karkace masa, mu wa'azantu da wa'azozinsa, da yaɗa ilimummukansa, mu yi kira zuwa gare shi. Na uku: Nasiha ga ManzonSa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Shi ne mu ƙudire cewa shi ne ƙarshen Manzanni, mu gasgata shi a cikin abin da ya zo da shi, mu yi riko da umarninsa, mu nisanci haninsa, kuma kada mu bautawa Allah da komai sai abin da ya zo da shi, mu girmama haƙƙinsa, mu girmama shi, mu yaɗa Da'awarsa, mu yaɗa shari'arsa, kuma mu kore tuhuma daga gare shi. Na huɗu: Nasiha ga shugabannin musulmai: Ta hanyar taimakonsu a kan gaskiya, da rashin jayayya da su a al'amari, da ji da biyayya garesu akan biyayya ga Allah. Na biyar: Nasiha ga musulami: Ta hanyar kyautatawa zuwa garesu da kiransu, da hana cutar da su, da son alheri garesu, da taimakekeniya tare da su a kan biyayya da tsoron Allah.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Dukkanin gaɓa ta mutane sadaka ce gare shi, kowanne yinin da rana ta hudu a cikinsa ka daidaita tsakanin mutum biyu sadaka ne, ka taimaki mutum a dabbarsa ka ɗora shi a kanta ko ka sauke masa kayansa daga kanta to sadaka ne, kalma mai daɗi sadaka ce, dukkanin takun da ka yi zuwa masallaci sadaka ne, ka kauda ƙazanta akan hanya sadaka ne».
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sadaka ta ɗawwu'i saboda Allah - Maɗaukakin sarki - akan kowanne musulmi mukallafi a kowacce rana a kan kowacce gaba daga cikin gabban jikinsa, sadaka ta Nafila ga Allah madaukakin sarki akan tafarkin godiya gare Shi akan lafiya, kuma sanya ƙasusuwansa gaɓɓai zai samu dama da suna damƙa da shinfiɗawa. kuma cewa wannan sadakar tana kaiwa ga ayyukan alheri gabaɗayanta bata tsayuwa akan bada wata dukiya, Daga ciki: Daidaitawarka da yin sulhunka tsakanin masu husuma sadaka ne. A taimakonka ga wani gajiyayye a dabbarsa (abin hawa) sai ka ɗora shi akanta, ko ka ɗauke masa kayansa sadaka ne. Kalma mai daɗi ta zikiri ce da addu'a da sallama da wasunsu sadaka ce. Kowanne takin da ka yi tafiya da shi zuwa sallah sadaka ne, kawar da abinda ake cutuwa da shi a hanya sadaka ne.
Daga Ubada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji da biyayya a halin rintsi da sauƙi, da farin ciki da baƙin ciki, da kuma nuna fifiko a kammu. Kuma kada mu yi wa ma'abota al'amari jayayya, kuma mu faɗi gaskiya a duk inda muke, ka da mu ji tsoron zargin mai zargi a al'amarin Allah.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya riƙi alƙawari daga sahabbansa wajen jagorantuwa (biyayya) ga majiɓinta al'amura da shugabanni a halin sauƙi da wahala, da halin wadata da talauci, kuma duk ɗaya ne umarninsu ya kasance daga abin da rai yake so ne ko yake ƙi, kai ko da shugabanni sun yi babakere da dukiyar jama'a ko muƙamai ko wanin hakan a kan talakawa; to, dole ne a ji [maganarsu] a yi biyayya bisa sanannun abubuwa, kada a yi musu tawaye, domin fitina da ɓarna wajen yaƙarsu ita ce mafi girma, kuma mafi tsanani daga ɓarnar da za ta faru saboda zaluncinsu, yana daga abin da suka yi alkawari a kansa cewa za su faɗi gaskiya a kowanne wuri suna masu yi wa Allah ikhlasi cikin haka, ba sa jin tsoron wanda zai zargesu.
Daga Ummu Salalmah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Za'a samu wasu shugabanni zaku sansu kuma zaku yi inkarinsu, wanda ya sani ya kubuta, wanda kuma ya yi inkari ya kubuta, saidai wanda ya yarda ya kuma bi" suka ce: Shin ba ma yakesu ba? ya ce: "A'a, muddin dai suna sallah".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa za'a shugabantar da wasu shugabanni akanmu, zamu san wasu daga ayyukansu; dan dacewarsu da abinda aka sani na shari'a, kuma zamu yi inkarin wasu ayyukan na su; dan sabawarsu ga hakan, Wanda ya ki da zuciyarsa amma ba shi da iko akan inkari; to hakika ya kubuta daga zunubi da kuma munafunci, Wanda ya samu iko akan inkari da hannu ko da harshe sai ya yi inkarin hakan akansu to hakika ya kubuta daga sabo da kuma tarayya a cikinsu, sai dai wanda ya yarda da aikinsu ya kuma bi su akansa zai halaka kamar yadda suka halaka. Sannan suka tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Shin ba ba ma yaki shugabannin da wannan ita ce siffarsu ba? mu hanasu hakan, sai ya ce: A'a, muddin dai sun tsaida sallah a cikinku.
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da falalar Allah da rahamarSa, kuma cewa musulmi idan ya kasance al'adarsa cewa yana aikata wani aiki na gari a halin lafiyarsa da kuma zaman gidansa, sannan wani uzuri ya faru da shi sai ya yi rashin lafiya bai samu damar yin sa ba, ko ya shagalta da tafiya bai samu ya yi shi ba, ko wani uzurin; to cewa shi za'a rubuta masa lada cikakke, kamar da ya aikata shi a halin lafiya da zaman gida.
Daga Tamim al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa addini a tsaye yake a kan ikhlasi da gaskiya, har a yi kamar yadda Allah Ya wajabta, cikakke ba tare da tawaya ko algus ba. Sai aka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ga wa nasihar za ta kasance? sai ya ce: Na farko: Nasiha ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya daukaka -: ta hanyar tsarkake aiki gare shi, da rashin haɗa wani da Shi, kuma mu yi imani da Rububiyyarsa da Uluhiyyarsa da sunayensa da siffofinsa, da girmama al'amarinsa, da kira zuwa imani da Shi. Na biyu: Nasiha ga littafinsa shi ne Alƙur'ani mai girma: Shi ne cewa mu ƙudirce cewa shi zancensa ne, kuma ƙarshen littattafansa, kuma cewa shi mai shafewa ne ga dukkanin shari'o'i kafinsa, mu girmamashi, mu karantashi haƙiƙanin karantashi, mu yi aiki da muhkam ɗinsa, mu miƙa wuya ga abubuwa masu kamanceceniya a cikinsa, kuma mu kore tawilin masu karkacewa gareshi, mu wa'azantu da wa'azozinsa, da yaɗa ilimummukansa, da kira zuwa gareshi. Na uku: Nasiha ga manzonsa (Annabi) muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Shi ne mu kudire cewa shi ne karshen manzanni, mu gasgatashi a cikin abin da ya zo da shi, mu kamanta umarninsa, mu nisanci haninsa, kuma kada mu bautawa Allah da komai sai abin da ya zo da shi, mu girmama haƙƙinsa, mu girmamashi, mu yaɗa da'awarsa, mu yaɗa shari'arsa, kuma mu kore tuhuma daga gareshi. Na hudu: Nasiha ga shugabannin musulmai: Ta hanyar taimakonsu a kan gaskiya, da rashin jayayya da su a al'amari, da ji da biyayya garesu a cikin biyayya ga Allah. Na biyar: Nasiha ga musulami: Ta hanyar kyautatawa zuwa garesu da kiransu, da kame cuta daga garesu, da son alheri garesu, da taimakekeniya tare da su a kan biyayya da tsoron Allah.
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana faɗa a cikin wannan ɗakin nawa : "Ya Allah duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tsananta musu, to, ka tsananta masa, duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tausasa musu, to, Ka tausasa masa".
Muslim ne ya rawaito shiManzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi mummunar addu'a a kan dukkanin wanda ya jiɓinci wani al'amari daga al'amuran musulmai ya kasance ƙarami ne ko babba, kuma duk ɗaya ne, wannan shugabancin ya zama shugabanci ne mai gamewa, ko wani bangare ne keɓantacce, kuma ya shigar musu da tsanani bai tausasa musu ba, cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi masa sakayya daga jinsin aikinsa ta yadda zai tsananta masa. Kuma cewa duk wanda ya tausasa musu ya sauƙaƙa al'amuransu cewa Allah Zai tausasa masa kuma zai sauƙaƙa al'amuransa.
Daga Ma'aƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ba da labarin cewa kowane mutumin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanyashi majiɓinci, kuma shugaba ga mutane, duk ɗaya ne ya kasance shugabanci ne mai gamewa kamar sarki, ko keɓantaccen shugabanci ne kamar mutum a gidansa da mace a gidanta, sai ya gaza a haƙƙin waɗanda aka ba shi kiwonsu, ya yi musu algus bai yi musu nasiha ba, sai ya tozarta haƙƙoƙinsu na addini da na duniya, to, haƙiƙa ya cancanci wannan uƙubar mai tsanani.