





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya fita daga biyayya, ya kuma rabu da jama'a sai ya mutu, to, ya mutu irin mutuwar Jahiliyya, wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin makauniyar tuta, yana fushi saboda ƙabilanci, ko yake kira zuwa ƙabilanci, ko yake taimakon ƙabilanci, sai aka kashe shi, to, kisa ne na Jahiliyya, wanda ya yi fito na fito da al'ummata yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kiyaye wa tsakanin mumininta, kuma ba ya cika alkawari ga ma'abocin alkawari (kafirin amana), to, wannan ba ya tare da ni, ni ma ba na tare da shi".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya fita daga biyayyar majiɓinta al'amura, kuma ya rabu da jama'ar musulunci wacce ta haɗu a kan caffar (mubaya’a) shugaba, sai ya mutu a kan wannan halin na rabuwa da rashin biyayya, to, ya mutu irin mutuwar 'yan Jahiliyya, waɗanda ba sa bin wani shugaba, kuma ba sa tarowa zuwa jama'a ɗaya, kawai sun kasance ƙungiyoyi da jama'a-jama'a da sashinsu yana yaƙar sashi. (Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wanda ya yi yaƙi ƙarƙashin tutar da ba a fayyace gaskiyarta daga ƙaryarta ba, yana fushi saboda tsantsar ƙanilanci ga mutanensa ko ƙabilarsa, ba don taimakon Addini ko gaskiya ba, sai ya yi yaƙi don ƙabilanci ba tare da basira ko ilimi ba, to, idan aka kasheshi a kan wannan halin, ya zama kamar kisan Jahiliyya. Kuma wanda ya yi fito na fito da al'ummarsa (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake dukan mutumin kirkinta da fajirinta, ba ya kulawa da abin da yake aikatawa kuma ba ya jin tsoron uƙubarsa na kashe mumininta, kuma ba ya cika alƙawari ga ma'abota alƙawari daga cikin kafirai ko majiɓinta al'amura sai dai ma yana warwaresu, to, wannan yana daga manyan zunubai, wanda ya aikata shi, to, haƙiƙa ya cancanci wannan narkon mai tsanani.
Daga Arfajah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sandarku, ko ya raba jama'arku, to, ku kashe shi ".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa musulmai idan suka haɗu a kan shugabancin mutum ɗaya, da jama'a ɗaya, sannan wani ya zo yana son ya yi jayayya da shi a shugabanci, ko yana son raba musulmai sama da kungiya ɗaya, to, ya wajaba su hana shi da kuma yaƙarsa; don tunkuɗe sharrinsa da kuma kare jinanen musulmai.
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki".
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga mafi girma da anfanin nau'ikan jihadi a tafarkin Allah - Madaukakin sarki - shi ne kalma ta adalci da gaskiya a wurin azzalumin sarki (shugaba); domin cewa shi aiki ne da alama ce ta horo da aikin alheri da hani daga mummuna, daidai ne ya kasance da fada ne ko rubutu ko aikatawa ko wanin hakan wanda maslaha zata tabbata da shi kuma barna ta tunkude barna.
Daga Abu Sufyan Sakhr bin Harb - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: Hercules ya ce: Me yake umartarku - ma'ana: Annabi, Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - Abu Sufyan ya ce: Na ce: "Ka bauta wa Allah shi kaɗai, kada ka haɗa shi da wani abu, kuma bari mahaifinka ya faɗi abin da ya ce. Ta hanyar addu’a, gaskiya, tsabtar rai, da addu’a ».
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDaga Dan Mas’ud - Allah ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Za'a samu babakere da wasu al'amuran da zaku kisu" suka ce : Ya Manzon Allah mezaka umarcemu? Ya ce: "Ku bada hakkin da ya wajaba akanku, kuma ku roki Allah hakkinku ".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shugabanni zasu shugabanci musulmai, za su yi babakere da dukiyoyin musulmai da wasunsu daga al'amuran duniya, za su dinga juyasu kamar yadda suke so zasu hana musulmai hakkokinsu a dukiyar . Kuma wasu al'amuran da za'aki a Addini zasu kasance daga garesu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka yi tambaya: Me za su aikata a wannan halin? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ba su labarin cewa kada wawure (dukiya da suka yi) ya hanaku abinda ya wajaba akanku daura da su na ji da bi, kai ku yi hakuri ku ji ku bi , kada ku yi jayayya da su a al'amari, kuma ku roki Allah hakin dake gareku, kuma Ya gyrasu ya tunkude sharrinsu da zalincinsu.
Daga Nu'uman dan Bashir - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kwatankwacin tsayayye ga iyakokin Allah da mai afkawa cikinsu, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka yi kuri'a a jirgin ruwa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasansa sun kasance idan sun nemi ashayar da su ruwa sai sun wuce wadanda ke samansu, sai suka ce: Dama a ce zamu tsaga wata kafa a rabonmu ba mu cutar da wandanda ke samanmu ba, idan sun barsu da abinda suka yi nufi za su halaka gaba dayansu, idan suka yi riko da hannayensu za su tsira, sai su tsira gaba dayansu".
Bukhari ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya buga misali ga tsayayyu akan dokokin Allah, masu tsayawa akan umarnin Allah, masu horo da aikin alheri, masu hani daga abin ki, da misalin masu afkawa dokokin Allah masu barin kyakkyawan aiki, masu aikata abin ki, da tasirin hakan a nasarar zamantakewar jama'a, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka hau jirgin ruwa, sai suka yi kuri'a ga wanda zai zauna a saman jirgin ruwan da wanda zai zauna a kasansa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasa idan sun so samun ruwa sai sun wuce ta wurin wadanda ke saman, sai wadanda ke kasa suka ce: Da a ce zamu tsaga wata tsaga a daidai wurin mu a kasa mu dinga samun ruwa daga gareshi, har ya zama bamu cutar da wanda ke samanmu ba, da a ce wadanda ke sama sun barsu su aikata hakan da jirgin ruwan ya nitse da su gaba daya, da a ce sun hanasu hakan da duk jama' biyun sun tsira.
Daga Aliyu Dan Abi talib -Allah ya yarda da shi ya ce: "Ku rika zantar da Mutane da abinda suka sani ko kuna son su karyata Allah da Manzonsa ne ?
Buhari ne ya rawaito shiShugaban Muminai Aliyu Dan Abi Dalib - Allah ya yarda da shi - Izuwa cea bai dace ba a gayaa Mutane Marasa Ilimi sai da abinda suka saba ji kuma anda zai amfanar da su a cikin abinda yake na asalin Addininsu da Hukunce Hukuncensa na Tauhidi da bayanin Halal da Haram da kuma barin dukkan abun da ai shagaltar da su daga abubuwan da basa bukatarsu ko kuma abunda zai kai su zua kin karbar gaskiya da watsi da ita sabida rikitar da su da abinda yayi, kuma yayi musu wahalar fahimtar sa
Daga (Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: yaku mutane, lallai ku kuna karanta wannan ayar: {Yaku waɗanda suka yi imani ku lazimci kawunanku wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya}, lallai ni na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya gamesu da uƙuba daga gare shi".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra da Ibnu Majah haka kuma Ahmad(Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - yana bada labari: Cewa mutane suna karanta wannan ayar: {Yaku waɗanda suka yi imani ku lizimci kawunanku, wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya} [al-Ma'ida: 105]. Suna fahimta daga ayar cewa ya wajaba ga mutum ya yi ƙoƙari ya gyara kansa kawai, kuma ɓatan wanda ya ɓata ba zai cutar da shi ba bayan hakan, kuma su ba’a nema daga gare su su yi umarni da kyakkyawa kuma su hana mummuna ba. Sai ya sanar da su cewa ita ayar ba haka take ba, cewa shi ya ji annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai mutane idan suka ga azzalimi ba su hana shi zalincin ba, kuma suna da iko akan hana shin, ya kusa Allah Ya game su baki ɗaya da uƙuba daga gareShi, mai aikata abin ƙin, da mai yin shiru bai hana ba.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta, kowanne yinin da rana ta fito a cikin sa da (mutum) zai daidaita tsakanin mutune biyu sadaka ne, kuma ya taimaki mutum game da dabbar sa; sai ya ɗora shi a kanta, ko ya ɗauke masa kayan sa a kanta, to, sadaka ne, kuma kalma mai daɗi sadaka ce, kuma kowanne taku da zai yi zuwa sallah sadaka ne, kuma ya kau da ƙazanta daga hanya sadaka ne".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sadaka ta ɗawwu'i saboda Allah - Maɗaukakin sarki - akan kowanne musulmi mukallafi a kowacce rana a kan kowacce gaba daga cikin gabban jikinsa, sadaka ta Nafila ga Allah madaukakin sarki akan tafarkin godiya gare Shi akan lafiya, kuma sanya ƙasusuwansa gaɓɓai zai samu dama da suna damƙa da shinfiɗawa. kuma cewa wannan sadakar tana kaiwa ga ayyukan alheri gabaɗayanta bata tsayuwa akan bada wata dukiya, Daga ciki: Daidaitawarka da yin sulhunka tsakanin masu husuma sadaka ne. A taimakonka ga wani gajiyayye a dabbarsa (abin hawa) sai ka ɗora shi akanta, ko ka ɗauke masa kayansa sadaka ne. Kalma mai daɗi ta zikiri ce da addu'a da sallama da wasunsu sadaka ce. Kowanne takin da ka yi tafiya da shi zuwa sallah sadaka ne, kawar da abinda ake cutuwa da shi a hanya sadaka ne.