





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
An rawito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:Al-janna da wuta sun kai kara, sai Aljanna ta ce: Raunana ne da miskinai zasu shige ni, Sai wuta ta ce: Ni kuma Jabberan Mutane da Masu girman kai ne za su shige ni, sai ya ce da Wuta: ke Azaba ta ce, kuma ina yin Ukuba da ke ga wanda na so, Kuma ya ce da Al-jannah: Ke Rahama ta ce, kuma ina jin kan wanda na su da ke
Bukhari da Muslim Suka Rawaito shi a Ma'anarsaAn rawaito daga Sahl Bn Sa'ad -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai 'Yan Al-janna suna ganin Dakunan a cikin Al-Jannah kamar yadda kuke ganin Taurari a Sama"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiMatsayi a cikin Al-jannah ya banbanta daidai da Falalar kowa,har ta kai cewa "yan Al-jannah Madauakan Matsayansu wadanda suke Kasa asu rika gano na Samansu Kamar Taurari.
Daga Hassan ya ce: Jundub ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya yi mana hadisi a cikin wannan masallacin, kuma bamu manta ba tun da ya yi mana hadisin, kuma bama jin tsoron cewa Jundub ya yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninka ya kasance yana da ciwo, sai ya kasa haƙuri, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa, jinin bai tsaya ba har sai da ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: BawaNa yayi miNi gaggawa da ransa, (saboda haka) na haramta masa aljanna".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wani mutum daga waɗanda ke gabaninku ya kasance rauni ya same shi, sai ya kasa haƙuri bai yi haƙuri akan raɗaɗin ba, sai ya ɗauki wuƙa sai ya yanke hannunsa da ita kuma ya gaggautowa mutuwa, jinin bai tsaya ba har ya mutu, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawa Na ya yi miNi gaggawa da ransa, haƙiƙa na haramta masa aljanna.
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: "Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, wannan lafazin na Muslim ne, amma Bukhari ya rawaito shi a taƙaiceYa kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: (Ya Allah gareKa ne na miƙa wuya) kuma na jawu, (da Kai ne na yi imani) na gasgata kuma na yi iƙrari, (kuma gareKa ne na dogara) na fawwala na kuma dogara, (gareKa ne na koma) na koma na fuskanta, (saboda Kai ne na yi husuma) na yi jayayya da maƙiyanKa, (Ya Allah ni ina neman tsarinKa) ina fakewa (da buwayarKa) da hanawarKa da kuma rinjayenKa, (babu abin bautawa da gaskiya sai Kai) kuma babu wani abin bautawa da gaskiya inba Kai ba, (da Ka ɓatar da ni) daga shiriya da dacewa da yardarKa, (Kai ne Rayayye wanda ba zai mutu ba) kuma ba zai ƙareba, (aljanu da mutane kuwa zasu mutu).
Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum (Aminci ya tabbata agare ku), sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Goma» Sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Ashirin», sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai ya ce: «Talatin».
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Tirmizi da Ahmad da kuma DarimiWani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Assalamu alaikum, (Aminci ya tabbata agare ku) sai ya amsa masa sannan ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: An rubuta masa lada goma, sannan wani ya zo sai ya ce: Assalamu alaikum wa rahmatullah, (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada ashirin, sannan wani ya zo sai ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), sai ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Yana da lada talatin; wato kowane lafazi yana da lada goma.
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: «Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata».
Muslim ne ya rawaito shiYa kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Ya Allah ni ina roƙonKa shiriya» hanya madaidaiciya na sanin gaskiya da aiki da ita. «Da tsoron Allah», ruko da umarni da nisantar hane-hane. «Da kamewa» kamewa daga abinda ba ya halatta kuma ba shi da kyau na magana ne ko aiki. «Da wadatuwa» daga halitta, inda ba zai yi buƙatuwa ba zuwa ga wani inba Uabngijinsa - Mai girma da ɗaukaka ba -.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka abu kaza da abu kaza daga Safiyya, - wani daga maruwaita ya ce: Tana nufin cewa ita gajera ce - sai ya ce: «Haƙiƙa kin faɗi kalmar da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta canza shi» ta ce: Kuma na kwaikwayi wani mutum gare shi , sai ya ce: «Bana son ace na kwaikwayi wani mutum koda kuwa (na karɓi) abu kaza da abu kaza».
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadNana Aisha Uwar muminai A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya isheka daga Safiyya - tana nufin Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa daga cikin aibukanta na jiki ita gajera ce, sai ya ce: Haƙiƙa kin faɗi kalmar da da za'a cakuɗata da ruwan kogi da ta rinjaye shi ta canjashi ta kuma ɓata shi, ta ce: Kuma na aikata irin aikin wani mutum dan ɓata shi, sai Annabi - tsira da amincin Allsh su tabbata agare shi - ya ce: In ya faɗi aibinsa ba ya faranta mini rai, ko in kwaikwaye shi in aikata irin aikinsa ko in faɗi irin maganarsa ta fuskar tauyewa ko da kuwa an bani wani abu mai yawa na duniya akan haka.
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna».
Tirmizi ne ya ruwaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah) Ya tsarkakeShi (Mai girma) da zatinSa da siffofinSa da kuma ayyukanSa (da yabonSa) abin haɗawa da raɓa siffofin cika gareShi - tsarki ya tabbatar maSa -; za'a kafa kuma za'a dasa masa wani dabino a cikin ƙasar aljanna a duk lokacin da ya faɗeta.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi kuma kada ya ƙi taimakonsa, kada ya wulaƙanta shi tsoron Allah a nan yake" - ya yi nuni zuwa ƙirjin sa, sau uku - "Ya ishi mutum sharri ya wulaƙanta ɗan uwansa Musulmi, kowane Musulmi akan Musulmi haramun ne (ya zubda) jininsa, da dukiyarsa da mutuncinsa". Mutuncinsa".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa musulmi wasiyya ta alheri ga ɗan'uwansa musulmi, kuma ya bayyana sashin abinda yake wajaba akansa na wajibai da ladubba daura da su; daga hakan: Wasiyya ta farko: Kada ku yi wa juna hassada, ita ce sashinku ya yi burin gushewar ni'imar sashi. Na biyu: Kada ku yi cinikin koɗe shi ne mutumin da ba ya nufin yin siyan abin siyan sai ya yi ƙari a farashin abin siyan; kawai yana nufin anfanar mai siyarwar, ko cutar da mai siyan. Na uku: Kada ku yi ƙiyayya, ita ce nufin shigar da cuta kuma ita ce kishiyar soyayya; sai dai idan ƙiyayyar ta kasance ne a lamarin Allah ne - Maɗaukakin sarki -; to shi wajibi ce. Na huɗu: Kada ku juyawa juna baya, shi ne kowane ɗaya daga cikinku ya juyawa ɗan'uwansa bayansa da ƙeyarsa sai ya bijire masa kuma ya ƙaurace masa. Na biyar: Kada sashinku ya yi ciniki akan cinikin sashi, shi ne yacewa mai siyan: A wurina akwai irinta da ƙasa da farashinta ko ta fita kyau kuma farashinta bai kai nata ba. Sannan tsira da aminci su tabbata a gare shi ya yi wasiyya da wasiyya mai tattaro (ma'anoni da hikimomi masu yawa) sai ya ce: Ku zama kamar 'yan'uwa ta hanyar barin abubuwan da aka hana, da kuma nuna soyayya da sassauci da tausayi da sauƙaƙawa da taimakekeniya a aikin alheri, tare da tsarkakakkiyar zuciya da kuma yin nasiha a kowane hali. Daga abinda wannan 'yan uwantakar take hukuntawa: Kada ya zalinci ɗan'uwansa musulmi kuma ya yi ta'addanci akansa. Kada ya bari a zalinci ɗan'uwansa sai ya ƙi taimakonsa a gurin da yake da ikon ya taimake shi, kuma ya ɗauke masa zalincin. Kuma kada ya wulaƙanta shi ya raina shi ya dinga kallonsa da kallo na raini da izgili; shi mai fitowa ne daga girman kai a cikin zuciya. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana har sau uku cewa tsoron Allah a cikin zuciya yake, wanda a cikin zuciyarsa akwai tsoron Allah wanda yake hukunta kyakkyawar ɗabi'a, da tsoron Allah da muraƙabarSa to cewa shi ba zai wulaƙanta musulmi ba, kuma ya ishe shi ɗabi'u na sharri da ƙasƙanci ya wulaƙanta ɗan'uwansa musulmi, hakan saboda girmankan dake cikin zuciyarsa. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa hakan abinda ya wuce cewa kowane musulmi akan musulmi haramun ne: jininsa: Shi ne ya yi masa ta'addanci da kisa ko abinda bai kai kisa ba kamar rauni ko duka da makamancinsu, haka nan dukiyarsa: Shi ne ya ci dukiyar ba tare da wani haƙƙi ba, haka nan mutuncinsa: Shi ne ya zarge shi a kansa ko tsareshi.