





























Hadeeth Cards
Da'wa cards that highlight great meanings from the noble prophetic hadiths in a simple style and attractive display that helps the Muslim to have a deeper understanding of his religion in an easy way
All
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah SAW ya ce:"Kuji kuma Kub,i koda kuwa kuwa Bawa Bahabashe aka Shugabantar muku, Kai kace kansa gudaddajin Zabibi ne"
Buhari ne ya rawaito shiKu laimci Ji da biyayya ga Shuwagabannni, kuma koda Za'a dora muku Bawa Bahabashe -na Asali ko ko reshensa ko kuma a Halitta- a kan ku, wanda gashin Kansa Kamar zabibi, kuma wannan an fada ne ta hanyar kanbamawa cikin kasancewar wannan Ma'akacin Bawa ne bahabashe na Asali ko wani reshi daga shi, fadinsa: "Koda za'a dora muku" ya hade Shigaban da yake karbar Umarni daga Sarki, haka ma in shi ne Sarkin, da ace cewa Sarki ya yaki mutane yai Nasara a kansu kuma koda ba Balarabe ba ne; kai ace ma Bawa ne daga Habasha, to ya wajaba mu ji kuma mu bi shi, to wannan Hadisin yana nuna Wajabcin biyayya ga Shuwagabannni sai in Sabon Allah ne, saboda Alkairan da Zaman Lafiya da kwanciyar Hankalin dake cikin sa, da rashin tashin Hankali da rashin bin Son rai amma idan aka sabawa shuwagabanni cikin wani Al-amari da ya Wajabata ayi musu biyayya a cikinsa; saboda za'a iya samun tashin tashina, kuma za'a kowa ya kafe kan Ra'ayinsa, sai a rasa zaman lafiya, kuma abubuwa su baci, kuma futuntunu suyi yawa.
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya bini to hakika yabi Allah, kuma duk wanda ya Sabamun to hakika ya sabawa Allah, kuma duk wanda yabi Sugabansa to hakika ya bini, kuma duk wanda ya Sabawa Shugaba to hakika ya sabamun"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiAnnabi SAW yayi bayanin cewa biyayya gare shi tana daga cikin biyayya ga Allah, kuma Annabi SAW baya Umarni sai da Shari'a wacce Allah ya Shar'anta ga Al'ummarsa to idan yai Umarni da da wani abu to shi Sharia ne kuma duk wanda ya bi shi to ya bi Allah, kuma duk wanda ya saba Masa to ya sabawa Allah, kuma Shugaba idan Mutum ya bi shi to hakika ya bi Manzo SAW kuma idan ya Saba masa to hakika ya sabawa Manzon; domin Annabi SAW shi wanda ya yi umarni da hakan a cikin mafi yawan Hadisai; sai dai in yayi Umarni da Sabo
Daga Auf Bn Malik -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Mafiyan Shuwagabanninku su ne wadan da kuke son su kuma suma suke sonku, kuke sadawa da su kuma suma suke saduwa, Mafi Sharrin Suwagabannninku su ne wadanda kuke kinsu suke kinku, kuke La'antarsu suma suna la'antarku" ya ce: muka ce: ya Manzon Allah bama yi watsi da su ba? ya ce: "Aa, matukar dai suna tsaida Salla a cikin ku, a'a Matukar dai suna tsaida Sallah a cikin ku"
Muslim ne ya rawaito shiWannan Hadisin yana nuna cewa a cikin Shuwagabannin Musulmi akwai Nagari akwai kuma wadan da suke da Fasikanci da karancin Addini, kuma duk da hakan bai halarta ayi musu tawaye ba matukar dai suna kulawa da Sallah da abubuwan Musulunci, kuma ya Karfafa tsaida Sallah
A kan Ibn Abbas - Allah ya yarda da su duka - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce ta jakin da ke alama a fuskarsa, sai ya ce: “Allah ya la’ance wanda ya yi masa alama. ” Kuma a cikin wata ruwaya ta Muslim kuma cewa: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana buga fuska da Alamar fuska.
Muslim ne ya rawaito shiA cikin wannan hadisin akwai hani tabbatacce da gargadi mai karfi game da wanda ya yiwa dabba alama a fuska kuma an buge shi a fuska. Malamai - Allah ya yi musu rahama - sun dauke shi daga cikin manyan zunubai, kuma malamai sun yi hani da haramcin. Cewa fuska mai taushi ce kuma tana tattaro cancanta, kuma membobinta suna da daraja da taushi, kuma mafi yawansu suna sane da shi.
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki wata ƙaramar runduna sai ya shugabantar da wani mutum daga cikin mutanen Madina, kuma ya umarcesu da su yi masa biyayya, sai (mutumin) ya yi fushi, sai ya ce: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai umarce ku ku bini ba? suka ce: Ya umarcemu. (Sai) Ya ce: Ku haɗa mini itatuwa, sai suka haɗa masa, sai ya ce: Ku kunna wuta, sai suka kunnata, sai ya ce: Ku shigeta, sai suka yi niyyar (shiga), sai wasu daga cikinsu suka riƙe wasu, suna cewa: Mun gujewa wuta ne zuwa wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, basu gushe ba har sai da wutar ta mutu, sai fushinsa ya gushe, sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: «Da a ce sun shigeta da ba zasu fita daga cikinta ba har zuwa ranar alƙiyama; biyayya tana kasancewa ne kawai a aikin alheri».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki wata runduna, sai ya sanya wani mutum daga cikin mutanen Madina shugaba a kansu, kuma ya umarcesu da su yi masa biyayya, sai shugaban ya yi fushi a kansu kuma ya ce musu: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai umarceku ku bini ba? Suka ce: Ya yi umarni, ya ce: To na umarceku ku tattara mini itace ku kunna wuta, sannan ku shiga cikinta, sai suka tara itatuwa suka kunna wuta, lokacin da suka yi yunkurin shiga cikinta, sai sashinsu ya fara kallon sashi. Suka ce: Lallai mu bamu bi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sai donin gujewa wuta shin ma shigeta kuwa? Suna cikin haka sai wutar ta mutu, kuma fushin shugaba ya tafi. Sai aka baiwa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin hakan, sai ya ce: Da sun bi shi sun shiga cikin wutar da suka kunnata da an yi musu azaba a cikinta har ƙarewar duniya, babu biyayya ga wani abin halitta a cikin saɓon Mahalicci; kaɗai biyayya tana wajaba ne a aikin alheri ba'a saɓo ba.
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai za'a samu wasu shugabanni zasu dinga ƙarya suna zalinci, wanda ya gasgata su akan ƙaryarsu kuma ya taimakesu akan zalincinsu to ba ya ta tare da ni, nima bana tare da shi, kuma ba zai gangarowa Alkausara ba, wanda bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to shi yana tare da ni, nima ina tare da shi, kuma zai zo Alkausara".
Ahmad ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wasu shagabanni da zasu shugabanci mutane bayan rasuwarsa zasu dinga ƙarya a magana sai su dinga faɗin abinda ba sa aikatawa, kuma suna zalinci a cikin hukunci, wanda ya shiga gurinsu ya gasgata su akan ƙaryarsu, kuma ya taimakesu da aikata zalinci ko faɗarsa, kamar ba su fatawa dan neman kusancinsu da kwaɗayin abinda ke hannunsu; to ni babu ruwana da shi, ba shi ba ni, ba ni ba shi, kuma ba zai zo Alkausara ba ranar alƙiyama. Wanda bai shige su ba , kuma bai gasgatasu akan ƙaryarsu ba kuma bai taimakesu akan zalincinsu ba to yana tare da ni, kuma zai zo Alkausara ranar alƙiyama ba.
Aisha, Allah ya saka musu da alheri ya kawo: «Idan Allah yana son yarima mai kyau, ka sanya shi Ministan Ikhlasi, cewa ya manta an ambata, amma ya ce ya taimake shi, kuma idan yana so ya yi in ba haka ba ya sanya shi rashin lafiya, idan ya manta bai ambaci ba, amma ya ce ba Aanh».
Abu Daud Ya Rawaito shiManzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fada a cikin wannan hadisin cewa Allah Madaukaki: "Idan Yarima yana son alheri," kuma wannan sadaka ta fassara ta ne ta wani minista wanda aka nada shi zuwa ga ministan gaskiya daga cikin sarakuna a sadaka ta rabauta ga sadaka biyu, kuma an fassara wannan sadaka da aljanna Da fadinsa: "Ya sanya shi mai hidimar gaskiya," ma'anarsa ta magana da aiki, zahiri da badini, da kuma kara shi a kan gaskiya; Domin shine asalin abota da sauransu. Don haka "idan ya manta" ma'ana: wannan basaraken, idan ya manta abin da yake buƙata - kuma ya manta game da ɗabi'ar mutane - ko kuma ya kauce daga hukuncin shari'a, abin da aka zalunta, ko maslahar wata ikilisiya, ya "tunatar da shi" wato: wannan minista mai gaskiya ya shiryar da shi. Kuma idan “yariman” ya faɗi hakan, ya “taimake shi” da ra'ayi, magana da aiki. Amma fadinsa: “Kuma idan yana son wani abu ya yi shi,” wato: ban da alheri, ta hanyar son sharri tare da shi, sakamakon ya kasance “ya zama ministan sharri a gare shi.” Abin da ake nufi shi ne: ministan sharri a cikin maganganu da ayyuka, daidai da abin da aka ambata a baya a kansa. Idan ya manta, watau ya bar abin da ake bukata, bai tuna masa ba; Saboda bashi da hasken zuciya da zai kai shi ga hakan. Idan kuma ya tuna shi, ba haka yake nufi ba, sai dai ya nemi dauke hankalinsa daga gare shi. Zuwa ga tartsatsin ɗabi'arsa, da rashin lafiyarsa.
Daga Abu Sa`id al-Khudri da Abu Hurairah - Allah ya yarda da su - tare da isnadi: “Allah bai aiko daga annabi ba, kuma ban sanya wanda zai gaje shi ba daga khalifa, amma yana da layi biyu: layin da yake umurtar shi da yi masa nasiha zuwa ga alheri, kuma layin da yake umartar shi da sharri da kwadaitarwa, kuma ma'asumi shine.
Buhari ne ya rawaito shiDaga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi, lokacin da ya girma, sai ya cewa sarkin: Haƙiƙa ni na girma, ka aiko min da wani yaron da zan koya masa tsafi, sai ya aika masa da wani yaron da zai koya masa, ya kasance akan hanyarsa idan ya shiga akwai mai ibada sai ya zauna a wurinsa ya ji zancensa, sai ya ƙayatar da shi, ya kasance idan zai zo wajen matsafin sai ya wuce ta wajen mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan ya zo wajen matsafin sai ya dake shi, sai ya kai ƙarar hakan wajen mai ibadar, sai ya ce: Idan ka ji tsoron matsafin, to ka ce : Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma ka ji tsoron iyalanka to ka ce: Matsafi ne ya tsareni. Yana cikin haka sai ga shi ya zo wajen wata babbar dabbar da ta tsare mutane, sai ya ce: A yau ne zan san cewa matsafi ne ya fi ko mai ibada ne ya fi ? sai ya ɗauki wani dutse, sai ya ce: Ya Allah idan al'amarin mai ibadar ne shi ne mafi soyuwa gareKa to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su tafi, sai ya jefeta sai ya kasheta, mutane suka wuce, sai ya zo wajen mai ibadar sai ya ba shi labari, sai mai ibadar ya ce masa: Ya kai ɗana kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka ya kai abinda ka gani, lallai cewa kai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nuna ni, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, kuma yana bawa mutane maganin sauran cututtuka, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya makance ya ji, sai ya zo masa da kyaututtuka masu yawa, sai ya ce: Abinda ke nan saboda kaine na tarasu, idan ka warkar da ni, sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, idan ka yi imani da Allah zan roƙi Allah sai Ya warkar da kai, sai ya yi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai ya zo wajen sarkin, sai ya zauna a wurinsa kamar yadda ya kasance yana zama, sai sarkin ya ce da shi: Waye ya dawo maka da ganinka? Ya ce: Ubangijina, ya ce: Shin kana da wani Ubangijin wanina? ya ce: Ubangijina kuma Ubangijinka Shi ne Allah, sai ya kama shi bai gushe ba yana ta azabtar da shi har saida ya nuna yaron, sai aka zo da yaron, sai sarkin ya ce masa: Yakai ɗana, haƙiƙa tsafinka ya kai har kana iya warkar da makaho da kuturu kana yin kaza da kaza?! sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kama shi bai gusheba yana azabtar da shi har sai da ya nuna mai ibadar, sai aka zo da mai ibadar sai aka ce masa: Ka bar Addinika, sai ya ƙi, sai ya sa aka kawo masa zarto sai ya ɗora zartan a tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi har saida ɓarikan jikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da ɗan majalisar sarki sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai aka ɗora zarton akan tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi da shi har sai da ɓangarorin jnikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da yaron sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai ya miƙa shi wurin wasu jama'a daga mutanensa, sai ya ce: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza, ku hau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa idan ya bar Addininsa to (ku kyale shi) inba haka ba fa to ku jeho shi, sai suka tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza sai suka hau dutsen da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su sai suka faɗo, sai ya zo yana tafiya zuwa wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya ƙara bada shi ga wasu daga cikin mutanensa sai ya ce: Ku tafi da shi ku ɗauke shi a cikin jirgin ruwa, kuje tsakiyar kogi da shi, idan ya bar Addininsa to inba haka ba fa to ku jefa shi, sai suka tafi da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiye, sai ya zo yana tafiya wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya cewa sarkin: Kai ba zaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi, ya ce: Menene shi? ya ce: Ka tara mutane wuri ɗaya ka tsireni akan wani kututture, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar gwafa sannan ka ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai kai idan ka aikata hakan to zaka kasheni, sai ya tara mutane a wuri ɗaya, sai ya tsire shi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa sannan ya sanya mashin a cikin tsakiyar gwafa, sannan yace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbe shi sai ya faɗi ta kayakayinsa, sai ya ɗora hannunsa akan kayakayinsa sai ya mutu, sai mutane suka ce: Mun yi imani da Ubangijin yaro, sai aka zo wa sarkin sai aka ce da shi: Shin kana ganin abinda tsoro, haƙiƙa wallahi tsoronka ya faru, mutane sun yi imani, sai ya yi umarni da haƙa rami ta farkon layuka sai aka haƙa kuma aka hura wuta a cikinsu kuma ya ce: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku cusa shi a cikinta, ko a ce masa: Ka faɗa sai suka aikata, har sai da wata mace ta zo alhali a tare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya taƙi kutsawa ciki, sai ɗan nata ya ce mata: Ya babata ki yi haƙuri lallai cewa ke akan gaskiya kike".
Muslim ne ya rawaito shiAnnabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wani sarki cikin waɗanda suka gabacemu daga cikin al’ummu, ya kasance yana da wani matsafi, lokacin da matsafin ya girma (ya tsufa), sai ya cewa sarkin: Lallai ni na girma, to ka aiko wani saurayi zuwa wurina in koya masa tsafi. Sai sarkin ya aika masa da wani saurayin da zai koya masa, a kan hanyar saurayin idan zai tafi gurin matsafin akwai wani mai ibada, sai ya zauna a wurinsa sau ɗaya ya ji zancensa, sai ya ƙayatar da shi. Ya kasance idan ya zo wurin matsafin sai ya wuce wurin mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan kuma ya je wurin matsafin sai ya dake shi, saboda jinkirin da ya yi, sai ya kai ƙarar hakan wurin mai ibadar, sai ya ce: Idan ka ji tsoron matsafin, to ka ce: Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma ka ji tsoron iyalanka to ka ce : Matsafi ne ya tsareni. Sun kasance a haka lokacin da ya zo wa wata babbar dabba ta hana mutane wucewa, sai ya ce: A yau ne zan san cewa matsafi ne ya fi ko kuma mai ibada ne yafi? Sai ya ɗauki wani dutse, sai ya ce: Ya Allah idan al'amarin wannan mai ibadar ne mafi soyuwa gareKa daga al'amarin matsafin nan to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su wuce, sai ya jefeta sai ya kasheta, kuma mutane suka wuce, sai ya zo wajen mai ibadar sai ya ba shi labari, sai mai ibadar ya ce masa: Ya kai ɗana ! Kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka ya kai abinda kake gani, kuma lallai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nuna ni, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, yana bawa mutane maganin sauran cututtuka da izinin Allah, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya rasa idonsa ya ji, sai ya zo masa da kyautuka masu yawa, sai ya cewa yaron: Dukkan abinda ke nan na kyautuka naka ne idan ka warkar da ni. Sai ya ce: Lallai ni bana warkar da wani kawai Allah ne Yake warkarwa, idan ka ni imani da Allah zan roƙi Allah Ya warkar da kai, sai ya yi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai ya zo wajen sarkin sai ya zauna a wurinsa kamar yadda ya kasance yake zama, sai sarkin ya ce masa: Waye ya mayar maka da ganinka? Ya ce: Ubangijina, ya ce: Shin kana da wani Ubangijin wanina? Ya ce: Ubangijina da Ubangijinka shi ne Allah. Sai ya kama shi bai gushe ba yana azabtar da shi har sai da ya nuna yaron, sai aka zo da yaron, sai sarkin ya ce masa: Ya kai ɗana ! haƙiƙa tsafinka yakai har kana warkar da makaho da kuturu, kana aikata kaza da kaza. Sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kama shi bai gushe ba yana azabtar da shi har saida ya nuna mai ibadar. Sai aka zo da mai ibadar, sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai yaƙi, sai ya ce akawo masa zarto, sai ya ɗora shi akan tsakiyar kansa, sai ya raba shi gida biyu. Sannan aka zo da ɗan majalisar sarkin sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi sai ya sanya zarto akan tsakiyar kansa, sai ya raba shi gida biyu. Sannan aka zo da yaron sai aka ce masa ka bar Addinika, sai ya ƙi sai ya miƙashi wurin wasu mazaje daga mutanensa tsakanin uku da goma. Sai ya ce: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza, ku hau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa, idan ya bar Addininsa to, inba haka bafa to ku jeho shi, sai suka tafi da shi sai suka hau dutsen da shi. Sai yaron ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su ya yi motsi motsi mai tsanani sai suka faɗo, sai ya zo yana tafiya zuwa wurin sarkin. Sai sarkin ya ce masa: Me mutanenka suka yi? Ya ce: Allah Ya isar mini su. Sai ya miƙashi zuwa wasu mutane daga cikin mutanensa, sai ya ce: Ku tafi da shi ku ɗaukeshi a cikin ƙaramin jirgin ruwa, sai ku tafi tsakiyar kogi da shi, idan ya bar Addininsa (ku kyale shi) inba haka ba fa to ku jefa shi a cikin kogin. Sai suka tafi da shi, sai ya ce: Ya Allah Ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiya, sai ya zo yana tafiya wurin sarkin. Sai sarkin ya ce masa: Me mutanenka suka yi? Sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai yaron ya cewa sarkin: Lallai cewa kai ba zaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi. Ya ce: Menene shi? Ya ce: Ka tara mutane a babban fili, ka tsireni akan kututturen bishiya, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar kwari, sannan ka ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai cewa kai idan ka aikata haka to zaka kasheni, sai ya tara mutane a wuri ɗaya, ya tsire shi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa, sannan ya sanya mashin a tsakiyar kwari, sannan ya ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbe shi sai mashin ya faɗa a kayakayinsa tsakanin idanuwansa da kunnansa, sai ya ɗora hannunsa a kayakayinsa a wurin da mashin (ya faɗa) sai ya mutu. Sai mutane suka ce: Mun yi imani da Ubangijin yaro, mun yi imani da Ubangijin yaro, Mun yi imani da Ubangijin yaro. Sai aka zo wa sarkin aka ce masa: Shin kaga abinda ka kasance kana jin tsoro? Haƙiƙa wallahi abinda ka ji tsoro ya kasance, shi ne mutane suna bin yaron da yin imani da Ubangijin yaron bakiɗayansu, sai ya yi umarni a tsaga ƙasa a yi manyan ramuka masu tsawo a ƙofofin hanyoyi, aka kunna wuta a cikinsu, kuma ya ce: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku jefa shi a cikinta, sai suka aikata abinda sarkin ya umarcesu da shi, har wata mace ta zo atare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya ta lazimci inda take, taƙi shiga cikin wutar, sai ɗanta ya ce mata: Ya babata ki yi haƙuri, lallai ke akan gaskiya kike.